Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Mafi kusancin lokacin da bawa yake kasancewa kusa da Ubangiji a cikin (kason) dare na karshe

عَن أَبِي أُمَامَةَ قَالَ: حَدَّثَنِي عَمْرُو بْنُ عَبَسَةَ رضي الله عنه أَنَّهُ سَمِعَ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «أَقْرَبُ مَا يَكُونُ الرَّبُّ مِنَ العَبْدِ فِي جَوْفِ اللَّيْلِ الآخِرِ، فَإِنْ اسْتَطَعْتَ أَنْ تَكُونَ مِمَّنْ يَذْكُرُ اللَّهَ فِي تِلْكَ السَّاعَةِ فَكُنْ».
Daga Abu Umamah ya ce: Amr ɗan Abasa - Allah Ya yarda da shi - ya zantar da ni cewa shi ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Mafi kusancin lokacin da bawa yake kasancewa kusa da Ubangiji a cikin (kason) dare na karshe, idan kana da ikon ka kasance daga wanda yake ambatan Allah a wannan lokacin to ka kasance".
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i ne Suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa Ubangiji - tsarki ya tabbatar maSa - Shi ne mafi kusa ga bawa a lokacin sulusin dare na karshe; idan an datar da kai kuma ka samu iko - ya kai mumini - da ka kasance daga jumlar masu bauta masu sallah masu ambatan Allah masu tuba a wannan lokacin to shi wani al'amari ne wanda yana kamata a ci ribarsa da kokari a cikinsa.

Fa’idoji
  1. Kwaɗaitar da musulmi akan zikiri a karshen dare.
  2. Fifikon lokuta a tsakaninsu ga zikiri da addu'a da sallah.
  3. Mirik ya ce: A cikin banbanci tsakaknin faɗinsa: "Mafi kusancin lokacin da Ubangiji ya fi kusa da bawa", da tsakanin faɗinsa: " Mafi kusancin lokacin da bawa yake kusa da Ubangijinsa alhali shi yana mai sujjada': Abin nufi a nan bayanin lokacin kasancewar Ubangiji Shi ne mafi kusa ga bawa shi ne tsakiyar dare, abin nufi a can bayanin kusancin halayen bawa ga Ubangiji alhali shi yana halin sujjada.
Madogara

سنن الترمذي (5/ 537) (3579). سنن أبي داود (2/ 454) (1277). سنن النسائي (1/ 279) (572). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 1019). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (5/ 509). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (17/ 535). مشكاة المصابيح، للتبريزي (1/ 387).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
SABABAI NA AMSAR ADDU'A DA MASU HANA AMSARTA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com