Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

ZIKIRAI NA AL'AMURA MASU BIJIROWA

Hadisai 14

Lallai Waxan nan Ayoyi Allah ya turo su, ba wai sun kasance saboda Mutuwa wani Mutum bane ko rayuwarsa, sai dai Allah yana aiko su don ya tsorata bayinsa, to idan kuka ga wani abu daga cikin su to zabura zuwa Anbaton Allah da roqonsa da kuma neman gafararsa"

عن أبي موسى الأشعري رضي الله عنه قال: خَسَفَت الشمس على زمان رسول الله صلى الله عليه وسلم . فقام فَزِعًا، ويخشى أن تكون الساعة، حتى أتى المسجد، فقام، فصلى بأطول قيام وسجود، ما رأيته يفعله في صلاته قطُّ، ثم قال: إن هذه الآيات التي يُرْسِلُهَا الله عز وجل : لا تكون لموت أحد ولا لحياته، ولكن الله يُرْسِلُهَا يُخَوِّفُ بها عباده، فإذا رأيتم منها شيئا فَافْزَعُوا إلى ذكر الله و دُعَائِهِ وَاسْتِغْفَارِهِ.
Daga Abu Musa Al-ash'ari -Allah ya yarda da shi- ya ce: anyi Khusufin Rana a lokacin Manzon Allah SAW sai ya tashi a firgice, kuma yana tsoron ko tashin Al-qiyama ne. har yaje Masallaci, sai ya tashi, sai yayi sallah da mafi tsawon tsayuwa da Sujada, da ban tava ganin yayi kwatankwacinsa ba a sallarsa, sannan ya cea: "Lallai Waxan nan Ayoyi Allah ya turo su, ba wai sun kasance saboda Mutuwa wani Mutum bane ko rayuwarsa, sai dai Allah yana aiko su don ya tsorata bayinsa, to idan kuka ga wani abu daga cikin su to zabura zuwa Anbaton Allah da roqonsa da kuma neman gafararsa"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري، ط1، دار الفكر، دمشق، 1381هـ. تيسير العلام شرح عمدة الأحكام للبسام، حققه وعلق عليه وخرج أحاديثه وصنع فهارسه: محمد صبحي بن حسن حلاق، ط10، مكتبة الصحابة، الإمارات - مكتبة التابعين، القاهرة، 1426هـ. تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين، ط1، مكتبة الصحابة، الإمارات، 1426هـ. عمدة الأحكام من كلام خير الأنام صلى الله عليه وسلم، لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، ط2، دار الثقافة العربية، دمشق ، بيروت، مؤسسة قرطبة، 1408 هـ. صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422هـ. صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، 1423هـ. الموسوعة الفقهية الكويتية، صادر عن: وزارة الأوقاف والشئون الإسلامية، الكويت، الطبعة: (من 1404 - 1427 هـ).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Wani mutum ya zo wurin Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya ce: Ya Manzon Allah, Ina son tafiya, don haka ka azurta ni, sai ya ce: “Allah Ya azurta ku da takawa. : Ka warkar da ni, ya ce: "Kuma ka kyautata maka a duk inda kake

عن أنس بن مالك رضي الله عنه قال: جاء رجل إلى النبي صلى الله عليه وسلم فقال: يا رسول الله، إني أريد سَفَرًا، فَزَوِّدْنِي، فقال: «زَوَّدَكَ الله التقوى» قال: زِدْنِي قال: «وَغَفَرَ ذَنْبَكَ» قال: زِدْنِي، قال: «ويَسَّرَ لك الخيَر حَيْثُمَا كنتَ».
Daga Anas bin Malik, yardar Allah ta tabbata a gare shi, wanda ya ce: Wani mutum ya zo wurin Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya ce: Ya Manzon Allah, Ina son tafiya, don haka ka azurta ni, sai ya ce: “Allah Ya azurta ku da takawa. : Ka warkar da ni, ya ce: "Kuma ka kyautata maka a duk inda kake."
Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Al-Darumi Ya Rawaito shiDarajaHasan ne kuma Garibi
Madogara

بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، سليم بن عيد الهلالي، دار ابن الجوزي، الدمام، الطبعة: الأولى 1415هـ. تحفة الأحوذي بشرح جامع الترمذي، محمد عبد الرحمن بن عبد الرحيم المباركفورى، دار الكتب العلمية، بيروت. سنن الترمذي، محمد بن عيسى الترمذي، تحقيق وتعليق: أحمد محمد شاكر، ومحمد فؤاد عبد الباقي، وإبراهيم عطوة عوض، شركة مكتبة ومطبعة مصطفى البابي الحلبي، مصر، الطبعة: الثانية، 1395هـ، 1975م. دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين، محمد علي بن البكري بن علان، اعتنى بها: خليل مأمون شيحا، دار المعرفة، بيروت، الطبعة: الرابعة 1425هـ. رياض الصالحين من كلام سيد المرسلين، أبو زكريا محيي الدين النووي، تحقيق ماهر الفحل، دار ابن كثير، دمشق، بيروت، الطبعة: الأولى 1428هـ. سنن الدارمي، تحقيق: حسين سليم أسد الداراني، دار المغني للنشر والتوزيع، المملكة العربية السعودية، الطبعة: الأولى 1412هـ. نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، مجموعة من الباحثين، مؤسسة الرسالة، بيروت، الطبعة: الرابعة عشرة 1407هـ. الكلم الطيب/تقي الدين ابن تيمية -تحقيق: محمد ناصر الدين الألباني-المكتب الإسلامي - بيروت - الطبعة: الثالثة - 1977م.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

'Lallai Ni na san wata kalmar da zai faɗeta da abinda yake ji ya tafi daga gare shi, da zaice: Ina neman tsarin Allah daga Shaiɗan, abinda yake ji zai tafi

عَنْ سُلَيْمَانَ بْنِ صُرَدٍ رضي الله عنه قَالَ: كُنْتُ جَالِسًا مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَرَجُلاَنِ يَسْتَبَّانِ، فَأَحَدُهُمَا احْمَرَّ وَجْهُهُ، وَانْتَفَخَتْ أَوْدَاجُهُ، فَقَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِنِّي لَأَعْلَمُ كَلِمَةً لَوْ قَالَهَا ذَهَبَ عَنْهُ مَا يَجِدُ، لَوْ قَالَ: أَعُوذُ بِاللَّهِ مِنَ الشَّيْطَانِ، ذَهَبَ عَنْهُ مَا يَجِدُ» فَقَالُوا لَهُ: إِنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «تَعَوَّذْ بِاللَّهِ مِنَ الشَّيْطَانِ»، فَقَالَ: وَهَلْ بِي جُنُونٌ؟
Daga Salaiman Bin Surad - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance ina zaune tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali wasu mutane biyu suna zage-zage, ɗayansu fuskarsa ta yi jā, jijiyoyinsa sun buɗe, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: 'Lallai Ni na san wata kalmar da zai faɗeta da abinda yake ji ya tafi daga gare shi, da zaice: Ina neman tsarin Allah daga Shaiɗan, abinda yake ji zai tafi" sai suka ce masa: Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ka nemi tsarin Allah daga Shaiɗan", sai ya ce: Shin ni ina da hauka ne?
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

wasu mutane biyu sun yi zage-zage a gaban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, alhali fuskar ɗayansu ta yi jā, jijiyoyinsa da suka kewaye wuyansa sun kunbura. Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Lallai ni na san kalmar da wannan mai fushin zai faɗeta da fushin ya tafi daga gare shi, da zai ce: Ina neman tsarin Allah daga Shaiɗan abin jefewa. Sai suka ce masa: Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ka nemi tsarin Allah daga Shaiɗan. Sai ya ce: Shin ni mahaukaci ne? ya yi zatan cewa ba mai neman tsari daga Shaiɗan sai wanda yake da hauka.

Fa’idoji
  1. Kwaɗayin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan shiryarwa da fadakarwa a yayin samuwar sababinsa.
  2. Fushi daga Shaiɗan ne.
  3. Umarni da neman tsarin Allah daga Shaɗan abin jefewa a yayin fushi, Allah Maɗaukakin sarki Ya ce: {Idan fuzga daga Shaiɗan ta fuzgeka to ka nemi tsarin Allah..} Aya.
  4. Gargaɗi akan zagi da abinda ke kama da shi na tsinuwa, da kuma nisanta daga garesu; domin su suna kaiwa zuwa ɓarna tsakanin mutane.
  5. Kawo nasiha ga wanda bai ji ta ba dan ya anfana da abinda ke cikinta.
  6. Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsoratar daga fushi; domin cewa shi yana kaiwa zuwa sharri da rashin tinani, tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya kasance ba ya fushi sai dai idan an keta alfarmar Allah - Maɗaukakin sarki -, shi ne fushi abin yabo.
  7. AlNawawi ya faɗa akan faɗinsa: "Shin kana ganin ni ina da hauka ne": Zai yiwu cewa wannan mai maganar ya kasance yana daga munafukai, ko daga larabawan ƙauye masu wauta.
Madogara

صحيح البخاري (4/ 124) (3282). صحيح مسلم (4/ 2015) (2610). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 110). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص50). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (1/ 270). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 78).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Marowaci shi ne wanda aka ambace ni a wurinsa bai yi mini salati ba

عَنِ الحُسَينِ بنِ عَلِيٍّ بنِ أَبِي طَالِبٍ رضي الله عنهما قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «الْبَخِيلُ مَنْ ذُكِرْتُ عِنْدَهُ فَلَمْ يُصَلِّ عَلَيَّ».
Daga Husaini ɗan Ali ɗan Abu Ɗalib - Allah Ya yarda da su (Husain da Ali) - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Marowaci shi ne wanda aka ambace ni a wurinsa bai yi mini salati ba".
Tirmizi da Nasa'i cikin alkubra haka Ahmad suka ruwaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsoratar akan barin salati gare shi a halin jin sunansa ko alkunyarsa ko siffarsa, ya ce: Marowaci mai cikakkiyar rowa (shi ne) wanda aka ambaceni a wurinsa bai yi mini salati ba; hakan saboda wasu al'amura: Na farko: Cewa hakan rowa ce, da wani abun da ba ya asara saboda shi kaɗan ne ko mai yawa, kuma ba ya bada wata dukiya, kuma ba ya yin wani ƙoƙari. Na biyu: Cewa shi ya yi wa kansa rowa kuma ya haramta mata ladan salati ga Manzonsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -; domin cewa shi haƙiƙa ya yi rowa saboda hanuwarsa daga salati gare shi, kuma ya hanu daga bada haƙƙin da bada shi ya wajaba akansa dan ruko da umarni kuma ake samun lada da shi. Na uku: Cewa salati gare shi a cikinsa akwai bada haƙƙin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, shi ne wanda ya sanar damu, kuma shi ne wanda ya shiryar damu, shi ne wanda ya kiramu zuwa ga Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - kuma ya zo mana da wannan wahayin, da kuma wannan shari'ar, shi ne sababin shiriyarmu - bayan Allah - alhrerinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - wanda bai yi masa salati ba zai zama haƙiƙa ya yi wa kansa rowa, kuma ya yi rowa ga AnnabinSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da wani haƙƙin da yana daga mafi ƙasan haƙƙoƙinsa.

Fa’idoji
  1. Barin salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - take ne na rowa.
  2. Salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana daga mafificin ayyukan kusanci da kuma ɗa'a a dukkanin lokuta, kuma yana ƙarfafuwa a halin ambatansa.
  3. Al-Nawawi ya ce: Idan zai yi salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - to ya haɗa tsakanin salati da sallama, kada ya taƙaita akan ɗayansu; kada ya ce: (Allah Ya yi salati gare shi) kadai, ko: (Amnici ya tabbata agare shi) kadai.
  4. Abul Aliya ya faɗa a cikin faɗinSa: {Lallai Allah da mala'ikunSa suna salati ga wannan Annabi} ya ce: Salatin Allah - Mai girma da ɗaukaka - ga AnnabinSa: YabonSa gare shi, salati daga mala'iku da mutane: Addu'a.
  5. AlHulaimi ya ce: Ma'anar: "Ya Allah Ka yi salati ga (Annabi) Muhammad": Ya Allah ka girmama shi a duniya da ɗaukaka ambatansa, da bayyanar da Addininsa, da wanzar da shari'arsa, a lahira kuma: Da neman cetansa a sha'anin al'ummarsa, da gwaggwaɓa ladansa da sakamakonsa, da bayyanar da falalarsa ga na farko da na karshe da matsayi abin yabo, da gabatar da shi akan dukkan makusanta masu halartowa.
Madogara

السنن الكبرى للنسائي (7/ 291) (8046). سنن الترمذي (5/ 513) (3546). مسند أحمد (3/ 257) (1736). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 486). فيض القدير شرح الجامع الصغير، لعبدالرؤوف المناوي (2/ 404). مشكاة المصابيح، لمحمد التبريزي (1/ 294). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 965).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Wanda ya ci abin ci sai ya ce: Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya ciyar da ni wannan kuma Ya azirtani shi ba tare da wata dabara daga gareni ko ƙarfi ba, za'a gafarta masa abinda ya gabata daga zunubinsa

عَنْ سَهْلِ بْنِ مُعَاذِ بْنِ أَنَسٍ عَنْ أَبِيهِ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ أَكَلَ طَعَامًا فَقَالَ: الحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي أَطْعَمَنِي هَذَا وَرَزَقَنِيهِ مِنْ غَيْرِ حَوْلٍ مِنِّي وَلاَ قُوَّةٍ، غُفِرَ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِهِ».
Daga Sahlu ɗan Mu'azu ɗan Anas daga babansa ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya ci abin ci sai ya ce: Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya ciyar da ni wannan kuma Ya azirtani shi ba tare da wata dabara daga gareni ko ƙarfi ba, za'a gafarta masa abinda ya gabata daga zunubinsa".
Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kwaɗaitar da wanda ya ci wani abinci da ya godewa Allah, babu wani iko gareni a samun abinci, ko a cinsa sai ga Allah - Maɗaukakin sarki - da kuma taimakonSa, Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi wa wanda ya faɗi hakan bushara da cewa shi ya cancanci gafarar Allah gare shi a abinda ya shuɗe daga zunubansa ƙananu.

Fa’idoji
  1. An so godewa Allah - Maɗaukakin sarki - a ƙarshen cin abin ci.
  2. Bayanin girman falalar Allah - Maɗaukakin sarki - ga bayinSa, inda Ya azirtasu kuma Ya sawwaƙa musu sabubban arziƙi , kuma Ya sanya kankare munanan ayyuka a cikin hakan.
  3. Al'amuran bayi gabaɗayansu daga Allah ne - Mai girma da ɗaukaka -, ba da dabararsu ko ƙarfinsu ba, kuma bawa abin umarta ne da aikata sabubba.
Madogara

سنن الترمذي (5/ 452) (3458). سنن أبي داود (6/ 138) (4023). سنن ابن ماجه (4/ 417) (3285). مسند أحمد (24/ 394) (15632). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، مجموعة من الباحثين (1/ 602). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، للهلالي (2/ 54). تاج العروس من جواهر القاموس، للزبيدي (28/ 366).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

"Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya ciyar da mu kuma ya Shayar da mu, kuma ya isar mana kuma ya bamu Makwanci, Saboda da yawa wanda babu mai isar masa ko mai bashi makwanci"

عن أنس رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم كان إذا أوى إلى فراشه، قال: «الحمد لله الذي أطعمنا وسقانا، وكفانا وآوانَا، فَكَمْ مِمَّنْ لا كَافِيَ له وَلاَ مُؤْوِيَ».
An rawaito daga Anas -Allah ya yarda da shi- cewa Manzon Allah ya Kasance idan zai tafi zuwa Makwancinsa yana cewa: "Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya ciyar da mu kuma ya Shayar da mu, kuma ya isar mana kuma ya bamu Makwanci, Saboda da yawa wanda babu mai isar masa ko mai bashi makwanci"
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

كنوز رياض الصالحين, بإشراف حمد العمار, دار كنوز إشبيليا, الطبعة الأولى, 1430ه. نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، نشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة: الرابعة عشر، 1407ه 1987م. بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، للهلالي، نشر: دار ابن الجوزي. صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، نشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Duk wanda ya sauka wani masauki, sai ya ce: Ina neman tsarin kalmomin Allah cikakku daga sharrin abin da ya halitta, to, babu abin da zai cutar da shi har ya bar wannan masaukin

عن خَوْلَةَ بِنْتَ حَكِيمٍ السُّلَمِيَّةَ قَالتْ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «مَنْ نَزَلَ مَنْزِلًا ثُمَّ قَالَ: أَعُوذُ بِكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّاتِ مِنْ شَرِّ مَا خَلَقَ، لَمْ يَضُرَّهُ شَيْءٌ حَتَّى يَرْتَحِلَ مِنْ مَنْزِلِهِ ذَلِكَ».
Daga Khaulah ’Yar Hakim Al-Sulamiyyah, ta ce: Na ji Ma’aikin Allh tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: Duk wanda ya sauka wani masauki, sai ya ce: Ina neman tsarin kalmomin Allah cikakku daga sharrin abin da ya halitta, to, babu abin da zai cutar da shi har ya bar wannan masaukin.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana nunawa al’ummarsa mafaka da matsera masu amfani, waɗanda za su kawar masa da duk abin da mutum yake tsoro, a lokacin da yake a wani wuri a nan doran ƙasa, shin yana halin tafiya ne ko shaƙatawa, ko wanin haka: sai ya nemi tsari da mafaka da kalmomin Allah cikakku a falalarsu da albarkarsu da amfaninsu, wanda ba su da kowane aibi da tawaya, daga sharrin duk abin halitta, to, sai ya amintu a inda ya sauka, muddin yana nan babu abin da zai cutar da shi.

Fa’idoji
  1. Neman tsari ibada ne, kuma shi ne abin da ya kasance daga Allah maɗaukaki ko sunayanSa ko kuma siffofinSa.
  2. Halaccin neman tsarin Allah da zancenSa, domin sifa ce daga cikin siffofinSa mai tsarki, saɓanin neman tsari daga wani abin halitta wannan shirka ne.
  3. Falalar wannan Addu’ar da kuma albarkarta.
  4. Neman mafaka da zikiri dalili ne na tsare bawa daga sharri.
  5. Lalata neman tsari da wanin Allah kamar aljan da matsafa da shedanu da sauransu.
  6. Shar’antuwar wannan Addu’ar ga duk wanda ya sauka wani wuri a halin zaman gida ko tafiya.
Madogara

صحيح مسلم (4/ 2080) (2708). مجموع الفتاوى (6/ 230). القول المفيد على كتاب التوحيد، لابن عثيمين (1/ 253). الملخص في شرح كتاب التوحيد، لصالح الفوزان (ص111). الجديد في شرح كتاب التوحيد، لمحمد القرعاوي (ص122). معجم اللغة العربية المعاصرة، لأحمد مختار (2/ 869).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Manzon Allah ya kasance idan yayi tafiya yana neman tsarin Allah daga Wahalar Tafiya, da Mummunar Dawowa, da tabarbarewar Yanayi, da kuma Addu'ar wanda aka Zalunta, da kuma Mummunan gani a cikin Ahali da Dukiya"

عن عبد الله بن سَرْجِس رضي الله عنه قال: كان رسول الله صلى الله عليه وسلم إذا سافر يَتَعَوَّذ مِن وَعْثاء السَّفَر، وكآبة الـمُنْقَلَب، والحَوْر بعد الكَوْن، ودعوة المظلوم، وسُوء الـمَنْظَر في الأهل والمال.
An rawaito daga Abdullahi Bn Sarjis -Allah ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah ya kasance idan yayi tafiya yana neman tsarin Allah daga Wahalar Tafiya, da Mummunar Dawowa, da tabarbarewar Yanayi, da kuma Addu'ar wanda aka Zalunta, da kuma Mummunan gani a cikin Ahali da Dukiya"
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

كنوز رياض الصالحين, بإشراف حمد العمار, دار كنوز إشبيليا, الطبعة الأولى, 1430هـ. نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، نشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة: الرابعة عشر، 1407ه 1987م. شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين، نشر: دار الوطن للنشر، الرياض، الطبعة: 1426هـ. معالم السنن، للخطابي، نشر: المطبعة العلمية - حلب، الطبعة: الأولى 1351 هـ - 1932م. مرعاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، للمباركفوري، نشر: إدارة البحوث العلمية والدعوة والإفتاء - الجامعة السلفية - بنارس الهند، الطبعة: الثالثة ، 1404 هـ - 1984م. صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، نشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
8 cikin 14
Hadisai 14
  1. Lallai Waxan nan Ayoyi Allah ya turo su, ba wai sun kasance saboda Mutuwa wani Mutum bane ko rayuwarsa, sai dai Allah yana aiko su don ya tsorata bayinsa, to idan kuka ga wani abu daga cikin su to zabura zuwa Anbaton Allah da roqonsa da kuma neman gafararsa"
  2. Wani mutum ya zo wurin Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya ce: Ya Manzon Allah, Ina son tafiya, don haka ka azurta ni, sai ya ce: “Allah Ya azurta ku da takawa. : Ka warkar da ni, ya ce: "Kuma ka kyautata maka a duk inda kake
  3. 'Lallai Ni na san wata kalmar da zai faɗeta da abinda yake ji ya tafi daga gare shi, da zaice: Ina neman tsarin Allah daga Shaiɗan, abinda yake ji zai tafi
  4. Marowaci shi ne wanda aka ambace ni a wurinsa bai yi mini salati ba
  5. Wanda ya ci abin ci sai ya ce: Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya ciyar da ni wannan kuma Ya azirtani shi ba tare da wata dabara daga gareni ko ƙarfi ba, za'a gafarta masa abinda ya gabata daga zunubinsa
  6. "Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya ciyar da mu kuma ya Shayar da mu, kuma ya isar mana kuma ya bamu Makwanci, Saboda da yawa wanda babu mai isar masa ko mai bashi makwanci"
  7. Duk wanda ya sauka wani masauki, sai ya ce: Ina neman tsarin kalmomin Allah cikakku daga sharrin abin da ya halitta, to, babu abin da zai cutar da shi har ya bar wannan masaukin
  8. Manzon Allah ya kasance idan yayi tafiya yana neman tsarin Allah daga Wahalar Tafiya, da Mummunar Dawowa, da tabarbarewar Yanayi, da kuma Addu'ar wanda aka Zalunta, da kuma Mummunan gani a cikin Ahali da Dukiya"
  9. Kada ku zagi Iska, idan kuka ga abinda ba kwa so to kuce: Ya Allah mu muna roƙonKa daga alherin wannan iskar, da alherin abinda ke cikinta, da alherin abinda aka umarce ta da shi, kuma muna neman tsarinKa daga sharrin wannan iskar, da kuma sharrin abinda ke cikinta, da kuma sharrin abinda aka umarce ta da shi
  10. An turbuɗe hancin mutumin da aka ambaceni a wurinsa bai yi mini salati ba, an turbuɗe hancin mutumin da Ramadan ya shiga sannan ya fita ba’a gafarta masa ba, kuma an turbuɗe hancin mutumin da mahaifansa suka tsufa a wurinsa amma basu shigar da shi aljanna ba
  11. Shin bana shiryar daku ga mafi alheri daga abinda kuka tambaya ba? idan kun kwanta - ko kunzo shinfiɗarku - to ku yi tasbihi sau talatin da uku, ku yi hamdala sau talatin da uku, ku yi kabbara sau talatin da da hudu, to shi ne mafi alheri gareku daga dan aiki
  12. "Ya Kasance idan ya ga jinjirin wata yakan ce: Ya Ubangiji ka saukar mana shi a gare mu da aminci da kuma Imani"
  13. Abu Saleh Ya kasance yana Umartarmu idan dayan mu zai bacci ya kwanta akan bangaren sa na dama
  14. Wannan wani Sahiɗan ne ana ce masa khinzab, idan ka ji shi ka nemi tsarin Allah daga gare shi, ka yi tofi a hagunka sau uku

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com