Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Duk wanda ya sauka wani masauki, sai ya ce: Ina neman tsarin kalmomin Allah cikakku daga sharrin abin da ya halitta, to, babu abin da zai cutar da shi har ya bar wannan masaukin

عن خَوْلَةَ بِنْتَ حَكِيمٍ السُّلَمِيَّةَ قَالتْ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «مَنْ نَزَلَ مَنْزِلًا ثُمَّ قَالَ: أَعُوذُ بِكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّاتِ مِنْ شَرِّ مَا خَلَقَ، لَمْ يَضُرَّهُ شَيْءٌ حَتَّى يَرْتَحِلَ مِنْ مَنْزِلِهِ ذَلِكَ».
Daga Khaulah ’Yar Hakim Al-Sulamiyyah, ta ce: Na ji Ma’aikin Allh tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: Duk wanda ya sauka wani masauki, sai ya ce: Ina neman tsarin kalmomin Allah cikakku daga sharrin abin da ya halitta, to, babu abin da zai cutar da shi har ya bar wannan masaukin.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana nunawa al’ummarsa mafaka da matsera masu amfani, waɗanda za su kawar masa da duk abin da mutum yake tsoro, a lokacin da yake a wani wuri a nan doran ƙasa, shin yana halin tafiya ne ko shaƙatawa, ko wanin haka: sai ya nemi tsari da mafaka da kalmomin Allah cikakku a falalarsu da albarkarsu da amfaninsu, wanda ba su da kowane aibi da tawaya, daga sharrin duk abin halitta, to, sai ya amintu a inda ya sauka, muddin yana nan babu abin da zai cutar da shi.

Fa’idoji
  1. Neman tsari ibada ne, kuma shi ne abin da ya kasance daga Allah maɗaukaki ko sunayanSa ko kuma siffofinSa.
  2. Halaccin neman tsarin Allah da zancenSa, domin sifa ce daga cikin siffofinSa mai tsarki, saɓanin neman tsari daga wani abin halitta wannan shirka ne.
  3. Falalar wannan Addu’ar da kuma albarkarta.
  4. Neman mafaka da zikiri dalili ne na tsare bawa daga sharri.
  5. Lalata neman tsari da wanin Allah kamar aljan da matsafa da shedanu da sauransu.
  6. Shar’antuwar wannan Addu’ar ga duk wanda ya sauka wani wuri a halin zaman gida ko tafiya.
Madogara

صحيح مسلم (4/ 2080) (2708). مجموع الفتاوى (6/ 230). القول المفيد على كتاب التوحيد، لابن عثيمين (1/ 253). الملخص في شرح كتاب التوحيد، لصالح الفوزان (ص111). الجديد في شرح كتاب التوحيد، لمحمد القرعاوي (ص122). معجم اللغة العربية المعاصرة، لأحمد مختار (2/ 869).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
ZIKIRAI NA AL'AMURA MASU BIJIROWA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com