Mummunar addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a kan nau'i uku da turbuɗe hancinansu da turɓaya daga ƙasƙanci da wulaƙanci da kuma taɓewa. Nau'i na farko: Wanda aka ambaci Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wurinsa bai yi masa salati ba da faɗinsa: tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ko makamancinsa. Na biyu: Wanda ya riski watan Ramadan sannan watan ya ƙare ba’a gafarta masa ba saboda gazawarsa a aikata aikin ɗa'a. Na uku: Mutumin da tsufa ya riski iyayensa a wurinsa amma ba su zama sababi a cikin shigarsa aljanna ba dan saɓawarsa da kuma gazawarsa a kan haƙƙinsu.
- Sindi ya ce: A taƙaice cewa kowane mutum daga waɗannan haƙiƙa ya samu abinda da badan kasawa daga gare shi ba da ya sami wani rabo mai yawa na alheri, yayin da ya kasa har hakan ya wuce shi to haƙiƙa ya taɓe kuma yayi hasara.
- Kwaɗaitarwa akan salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a duk lokacin da aka ambaci sunansa.
- Kwaɗaitarwa akan ƙoƙari da zage damtse ga ibada a cikin watan Ramadan.
- Kwaɗaitarwa akan ƙoƙari a cikin biyayya ga mahaifa da kuma girmamasu, musamman ma a lokacin tsufa.
سنن الترمذي (5/ 513) (3545). مسند أحمد (12/ 421) (7451). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 411). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 963). مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي القاري (2/ 744). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 485). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص767).