عَن أُمِّ الدَّرْدَاءِ وَ أَبِي الدَّرداءِ رَضيَ اللهُ عنهما أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ يَقُولُ: «دَعْوَةُ الْمَرْءِ الْمُسْلِمِ لِأَخِيهِ بِظَهْرِ الْغَيْبِ مُسْتَجَابَةٌ، عِنْدَ رَأْسِهِ مَلَكٌ مُوَكَّلٌ كُلَّمَا دَعَا لِأَخِيهِ بِخَيْرٍ، قَالَ الْمَلَكُ الْمُوَكَّلُ بِهِ: آمِينَ وَلَكَ بِمِثْلٍ».
Daga Ummu al-Darda'i da Abu al-Darda'i - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbara agare shi - ya kasance yana cewa: «Addu'ar musulmi ga ɗan'uwansa a ɓoye abar karɓa ce, a daidai kansa akwai wani Mala'ika wanda aka wakilta a duk lokacin da ya yi wa ɗan'uwansa addu'a ta alheri, sai Mala'ikan da aka wakilta gare shi ya ce: Amin, kaima (Allah Ya baka) kwatankwacin haka».
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa addu'ar musulmi ga ɗan'uwansa musulmi a bayan idon wanda aka yi wa addu'ar abar karɓa ce; domin cewa hakan ya fi kai matuƙa a cikin ikhlasi, kuma lallai cewa a wajen kan mai addu'ar akwai wani Mala'ikan da aka wakilta, a duk lokacin da ya yi wa ɗan'uwansa addu'a ta alheri, sai Mala'ikan da aka wakilta gare shi ya ce; Amin, kaima (Allah Ya baka) kwatankwacin abinda ka roƙa.
Fa’idoji
- Kwaɗaitarwa akan kyautatawa muminai sashinsu ga sashi ko da da addu'a ne.
- Addu'a a ɓoye tana nuni a bayyane akan gaskiyar imani da kuma 'yan uwantaka.
- Ƙayyade addu'a da cewa a ɓoye; domin cewa hakan ya fi kai matuƙa a ikhlasi (wato yi domin Allah) da kuma halartowar zuciya.
- Daga cikin sabubban amsa addu'a akwai musulmi ya yi wa ɗan'uwansa musulmi addu'a a ɓoye.
- Nawawi ya ce; Falalar addu'a ga ɗan'uwansa musulmi a ɓoye, da a ce zai yi wa jama'ar musulmai addu'a to wannan falalar zata tabbata, da kuma a ce zai yi addu'a ga jumlar musulmai to zance mabayyani shi ne samuwar (falalar), wani daga cikin magabata na gari ya kasance idan yana so ya yi wa kansa addu'a sai ya yi wa ɗan'uwansa addu'a da wannan addu'ar; domin cewa ita za'a amsata, kuma zai samu kwatankwacinta.
- Bayanin wasu daga cikin ayyukan Mala'iku, kuma cewa daga cikinsu akwai wanda Allah Ya wakilta shi ga wannan aikin.
Madogara
صحيح مسلم (4/ 2094) (2733).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 585).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 1018).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (6/ 48).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (17/ 510).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن النعمان بن بَشِير رضي الله عنه قال: سمعت النبيَّ صلى الله عليه وسلم يقول: «الدُّعَاءُ هُوَ الْعِبَادَةُ»، ثُمَّ قَرَأَ: «{وَقَالَ رَبُّكُمُ ادْعُونِي أَسْتَجِبْ لَكُمْ إِنَّ الَّذِينَ يَسْتَكْبِرُونَ عَنْ عِبَادَتِي سَيَدْخُلُونَ جَهَنَّمَ دَاخِرِينَ} [غافر: 60]».
Daga Nu'uman ɗan Bashir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa: "Addu'a ita ce ibada', sannan ya karanta; " {Ubangijinku Ya ce ku roƙeni zan amsa muku, lallai waɗanda suke girman kai game da bautata za su shiga Jahannama suna ƙasƙantattu} [Gafir: 60].
Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annbai - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa addu'a ita ce ibada, to, wajibi ne ta zama dukkaninta abar tsarkakewa ga Allah, duka ɗaya ne, ta kasance addu'ar tambaya ce da nema, da ya roƙi Allah - Maɗaukakin sarki - abin da zai amfaneshi, da tunkuɗe abin da zai cutar da shi a duniya da lahira, ko addu'ar ibada, ita kuma itace dukkanin abin da Allah Yake sonsa kuma Ya yarda da shi na maganganu da ayyuka na zahiri da baɗini, ibadu na zuciya ko na jiki ko na dukiya.
Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya kafa dalili akan haka ta inda ya ce: Allah Ya ce: {Ku roƙeni zan amsa muku, lalle waɗanda suke girman kai game da bauta min, da sannu za su shiga jahannama suna ƙasƙantattu}.
Fa’idoji
- Addu'a ita ce asalin ibada, ba ya halatta a juyar da ita ga wanin Allah.
- Addu'a ta ƙunshi haƙiƙanin bauta da iƙirari bisa wadatar Ubangiji da ikonsa - Maɗaukakin sarki -, da buƙatuwar bawa gareshi.
- Narko mai tsanani sakamakon girman kai game da bautar Allah da barin roƙonsa, kuma waɗanda suke girman kai game da roƙon Allah za su shiga jahannama suna ƙasƙantattu.
Madogara
سنن أبي داود (2/ 603) (1479).
سنن الترمذي (5/ 292) (3247).
سنن ابن ماجه (5/ 5) (3828).
مسند أحمد (30/ 297) (18352).
توضيح الأحكام من بلوغ المرام، للبسام (7/ 546).
منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (10/ 416).
فتح ذي الجلال والإكرام، لابن عثيمين (6/ 480).
سبل السلام بشرح بلوغ المرام، للصنعاني (2/ 707).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي هريرة رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «لَيْسَ شَيْءٌ أَكْرَمَ عَلَى اللهِ تَعَالَى مِنَ الدُّعَاءِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Babu wani abu mafi girma a wurin Allah - Maɗaukakin sarki- sama da addu'a".
Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shiDarajaHasan ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana cewa babu wani abu a ibadu mafifici a wurin Allah sama da addu'a; domin a cikinta akwai iƙirari da wadatar Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka -, da kuma iƙirari da gajiyawar bawa da buƙatuwarsa gareshi.
Fa’idoji
- Falalar addu'a kuma wanda ya roƙi Allah, to, shi mai girmamashi ne, kuma mai tabbatarwa ne da cewa Shi (Allah) Mawadaci ne - tsarki ya tabbatar masa - ba a roƙon mabuƙaci, kuma cewa Shi Mai yawan ji ne kurma ba a roƙonsa, kuma cewa shi mai kyauta ne, marowaci ba a roƙonsa, kuma cewa Shi Mai jin ƙai ne mai bushewar zuciya ba a roƙonsa, kuma cewa Shi Mai iko ne gajiyayye ba a roƙonsa, kuma cewa Shi Makusanci ne manisanci ba ya ji, da wanin haka na siffofin ɗaukaka da kyau na Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka -.
Madogara
سنن الترمذي (5/ 385) (3370).
سنن ابن ماجه (5/ 6) (3829).
مسند أحمد (14/ 360) (8748).
توضيح الأحكام من بلوغ المرام، للبسام (7/ 546).
منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (10/ 416).
فتح ذي الجلال والإكرام، لابن عثيمين (6/ 481).
سبل السلام بشرح بلوغ المرام، للصنعاني (2/ 707).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم قَالَ: «إِذَا مَاتَ الْإِنْسَانُ انْقَطَعَ عَنْهُ عَمَلُهُ إِلَّا مِنْ ثَلَاثَةٍ: إِلَّا مِنْ صَدَقَةٍ جَارِيَةٍ، أَوْ عِلْمٍ يُنْتَفَعُ بِهِ، أَوْ وَلَدٍ صَالِحٍ يَدْعُو لَهُ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan mutum ya rasu akin sa ya yanke sai dai daga abu uku: Sadaka mai gudana, ko wani ilimin da ake anfanuwa da shi, ko ɗa na gari da ya ke masa addu'a".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa aikin mamaci yana yankewa da rasuwarsa,, kyawawan ayyuka basa samunsa bayan mutuwnrsa sai a waɗannan ukun; dan kasancewarsa ya zama sababinsu:
Na farko: Sadakar da ladanta yake gudana kuma yake dawwama, ba mai yankewa ba, kamar waƙafi, da gina masallatai, da haƙa rijiyoyi, da wanin hakan.
Na biyu: Ilimin da mutane suke anfanuwa da shi, kamar wallafa littattafan ilimi, ko kamar ya koyar da wani mutum, sai wannan mutumin ya yaɗa wannan ilimin bayan mutuwarsa.
Na uku: Ɗa na gari mumini da zai yi masa addu'a.
Fa’idoji
- Ma'abota ilimi sun haɗu akan cewa daga abinda yake riskar mutum bayan mutuwarsa na lada: Sadaka mai gudana, da ilimin da ake anfanuwa da shi, da addu'a, kuma ya zo a cikin wasu Hadisan daban: Hajji kuma.
- An keɓanci waɗannan ukun da ambato a cikin wannan Hadisin; domin sune tushen alheri, kuma mafi rinjayar abinda ma'abota falala suke nufin wanzuwarsa bayansu.
- Dukkan ilimin da ake anfanuwa da shi to shi lada yana samuwa gare shi, sai dai ƙololuwarsu shi ne ilimi na shari'a da ilimummuka masu ƙarfafarsa.
- Ilimi mafi anfani shi ne waɗannan ukun; domin ilimi mutumin da yake neman saninsa yana anfanuwa da shi, akwai kiyaye shari'a a cikin ilimi, akwai anfanar halitta a gamewa, shi ne mafi ƙunsa kuma mafi gamewa; domin shi yana neman iliminka samamme a cikin rayuwarka kuma samamme bayan mutuwarka.
- Kwaɗaitarwa akan tarbiyyar yara salihai; su ne waɗanda suke anfanar iyayensu a lahira, daga anfanar su suna yi musu addu'a.
- Kwaɗaitarwa akan kyautatawa mahaifa bayan mutuwarsu, shima yana daga aikin alherin ɗa zai anfana da shi.
- Addu'a tana anfanar mamaci koda daga wanin ɗa ne, sai dai ankeɓanci ɗa da ambato; domin shi ne wanda yake ci gaba a addu'a ga mutum a galibi har zuwa mutuwarsa.
Madogara
صحيح مسلم (3/ 1255) (1631)، البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (28/ 413).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com