Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Addu'a ita ce ibada

عن النعمان بن بَشِير رضي الله عنه قال: سمعت النبيَّ صلى الله عليه وسلم يقول: «الدُّعَاءُ هُوَ الْعِبَادَةُ»، ثُمَّ قَرَأَ: «{وَقَالَ رَبُّكُمُ ادْعُونِي أَسْتَجِبْ لَكُمْ إِنَّ الَّذِينَ يَسْتَكْبِرُونَ عَنْ عِبَادَتِي سَيَدْخُلُونَ جَهَنَّمَ دَاخِرِينَ} [غافر: 60]».
Daga Nu'uman ɗan Bashir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa: "Addu'a ita ce ibada', sannan ya karanta; " {Ubangijinku Ya ce ku roƙeni zan amsa muku, lallai waɗanda suke girman kai game da bautata za su shiga Jahannama suna ƙasƙantattu} [Gafir: 60].
Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annbai - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa addu'a ita ce ibada, to, wajibi ne ta zama dukkaninta abar tsarkakewa ga Allah, duka ɗaya ne, ta kasance addu'ar tambaya ce da nema, da ya roƙi Allah - Maɗaukakin sarki - abin da zai amfaneshi, da tunkuɗe abin da zai cutar da shi a duniya da lahira, ko addu'ar ibada, ita kuma itace dukkanin abin da Allah Yake sonsa kuma Ya yarda da shi na maganganu da ayyuka na zahiri da baɗini, ibadu na zuciya ko na jiki ko na dukiya. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya kafa dalili akan haka ta inda ya ce: Allah Ya ce: {Ku roƙeni zan amsa muku, lalle waɗanda suke girman kai game da bauta min, da sannu za su shiga jahannama suna ƙasƙantattu}.

Fa’idoji
  1. Addu'a ita ce asalin ibada, ba ya halatta a juyar da ita ga wanin Allah.
  2. Addu'a ta ƙunshi haƙiƙanin bauta da iƙirari bisa wadatar Ubangiji da ikonsa - Maɗaukakin sarki -, da buƙatuwar bawa gareshi.
  3. Narko mai tsanani sakamakon girman kai game da bautar Allah da barin roƙonsa, kuma waɗanda suke girman kai game da roƙon Allah za su shiga jahannama suna ƙasƙantattu.
Madogara

سنن أبي داود (2/ 603) (1479). سنن الترمذي (5/ 292) (3247). سنن ابن ماجه (5/ 5) (3828). مسند أحمد (30/ 297) (18352). توضيح الأحكام من بلوغ المرام، للبسام (7/ 546). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (10/ 416). فتح ذي الجلال والإكرام، لابن عثيمين (6/ 480). سبل السلام بشرح بلوغ المرام، للصنعاني (2/ 707).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALAR ADDU'A

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com