Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Babu wani abu mafi girma a wurin Allah - Maɗaukakin sarki- sama da addu'a

عن أبي هريرة رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «لَيْسَ شَيْءٌ أَكْرَمَ عَلَى اللهِ تَعَالَى مِنَ الدُّعَاءِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Babu wani abu mafi girma a wurin Allah - Maɗaukakin sarki- sama da addu'a".
Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shiDarajaHasan ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana cewa babu wani abu a ibadu mafifici a wurin Allah sama da addu'a; domin a cikinta akwai iƙirari da wadatar Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka -, da kuma iƙirari da gajiyawar bawa da buƙatuwarsa gareshi.

Fa’idoji
  1. Falalar addu'a kuma wanda ya roƙi Allah, to, shi mai girmamashi ne, kuma mai tabbatarwa ne da cewa Shi (Allah) Mawadaci ne - tsarki ya tabbatar masa - ba a roƙon mabuƙaci, kuma cewa Shi Mai yawan ji ne kurma ba a roƙonsa, kuma cewa shi mai kyauta ne, marowaci ba a roƙonsa, kuma cewa Shi Mai jin ƙai ne mai bushewar zuciya ba a roƙonsa, kuma cewa Shi Mai iko ne gajiyayye ba a roƙonsa, kuma cewa Shi Makusanci ne manisanci ba ya ji, da wanin haka na siffofin ɗaukaka da kyau na Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka -.
Madogara

سنن الترمذي (5/ 385) (3370). سنن ابن ماجه (5/ 6) (3829). مسند أحمد (14/ 360) (8748). توضيح الأحكام من بلوغ المرام، للبسام (7/ 546). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (10/ 416). فتح ذي الجلال والإكرام، لابن عثيمين (6/ 481). سبل السلام بشرح بلوغ المرام، للصنعاني (2/ 707).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALAR ADDU'A

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com