عن أبي أمامة رضي الله عنه قال: سمعتُ رسولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم يقولُ: «اقْرَؤُوا القرْآنَ؛ فَإنَّهُ يَأتِي يَوْمَ القِيَامَةِ شَفِيعًا لأَصْحَابِهِ».
Daga Jabir: -Naji Manzon Allah yana cewa:" Mafificin Zikiri: cewa babu abin bautawa face Allah"
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya bukaci al-ummar sa da karatun Alkur’ani. Idan, a Ranar Kiyama, Allah ya sanya - Mai Girma da --aukaka - sakamakon wannan Alkur'ani a matsayin abu mai tsayuwa da kai, ranar tashin kiyama za ta zo don yin c interto ga masu karanta ta da waɗanda suke aiki a cikinta waɗanda suka bi umarnin da kuma hana shi.
Madogara
1-بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين؛ تأليف سليم الهلالي، دار ابن الجوزي.
2-دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين؛ لمحمد بن علان الشافعي، دار الكتاب العربي-بيروت.
3-رياض الصالحين من كلام سيد المرسلين؛ للإمام أبي زكريا النووي، تحقيق د. ماهر الفحل، دار ابن كثير-دمشق، الطبعة الأولى، 1428هـ.
4-شرح رياض الصالحين؛ للشيخ محمد بن صالح العثيمين، مدار الوطن، الرياض، 1426هـ.
5-صحيح مسلم؛ للإمام مسلم بن الحجاج، حققه ورقمه محمد فؤاد عبدالباقي، دار عالم الكتب-الرياض، الطبعة الأولى، 1417هـ.
6-نزهة المتقين شرح رياض الصالحين؛ تأليف د. مصطفى الخِن وغيره، مؤسسة الرسالة-بيروت، الطبعة الرابعة عشر، 1407هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن عبد الله بن مسعود رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «مَنْ قَرَأَ حَرْفًا مِنْ كِتَابِ اللهِ فَلَهُ بِهِ حَسَنَةٌ، وَالْحَسَنَةُ بِعَشْرِ أَمْثَالِهَا، لَا أَقُولُ {الم} حَرْفٌ، وَلَكِنْ {أَلِفٌ} حَرْفٌ، وَ{لَامٌ} حَرْفٌ، وَ{مِيمٌ} حَرْفٌ».
An karbo daga Abdullahi Ɗan Mas’ud Allah ya yarda da shi ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Duk wanda ya karanta wani harafi daga littafin Allah, to, yana da lada, kuma kowane lada za a ninkashi goma. amma ba zan ce Alif Laam Meem harafi ɗaya ba ne, sai dai Alif, harafi ne, Laam harafi ne, Meem harafi ne"
Tirmizi ne ya ruwaito shiDarajaHasan ne
Sharhi
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ba da labari cewa kowanne Musulmi ne ya karanta harafi daga littafin Allah, to, yana da lada a wannan karatun, kuma za a ninka masa lada zuwa ninki goma.
Sannan ya yi bayanin hakan da faɗinsa: Ban ce : Alif, Laam, Meem, harafi ba ne, sai dai Alifun harafi ne, Lamun harafi ne, Mimun harafi ne, sai ya kasance harufa uku, lada talatin kenan.
Fa’idoji
- Kwaɗaitarwa a kan yawaita karatun Alkur’ani.
- Mai karatu a kowanne harafi na kalma da yake rerawa yana da lada da za’a nunka sau goma.
- Yalwatuwar rahamar Allah, da kuma karamcinSa, ta yadda ya nunka wa bayinSa lada; falala ce da karamci daga gareShi.
- Falalar Alƙur’ani a kan wani zancen da ba shi ba, da yadda ake bauta da karanta shi, saboda shi zancen Allah ne.
Madogara
سنن الترمذي (5/ 33) (2910).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 229).
سلسلة الأحاديث الصحيحة، للألباني (7/ 970).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (4/ 655).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمصطفى الخِن وغيره (1/ 742).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ عَائِشَةَ رضي الله عنها قَالَتْ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «الْمَاهِرُ بِالْقُرْآنِ مَعَ السَّفَرَةِ الْكِرَامِ الْبَرَرَةِ، وَالَّذِي يَقْرَأُ الْقُرْآنَ وَيَتَتَعْتَعُ فِيهِ، وَهُوَ عَلَيْهِ شَاقٌّ، لَهُ أَجْرَانِ».
Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Gangaran a karatun Alƙur'ani yana tare da manyan mala'iku masu biyayya ga Allah, kuma wanda yake karanta Alƙur'ani kuma yake guragura a cikinsa yana mai shan wuya to yana da lada biyu.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda yake karanta Alƙur'ani, alhali shi mai kyakkyawar hadda ne mai kyautatawa, kuma gwani haziƙi a karanta shi, to a lahira yana da ladan da zai zama a matsayinsa tare da manyan mala'iku matafiya masu karamci. Kuma wanda yake karanta Alƙur'ani yake guragura a cikinsa yana kaikawo a karanta shi; dan raunin haddarsa alhali shi tare da hakan yana riƙe da shi, kuma yana wahalar da shi to shi yana da lada biyu; ladan karatun Alkur'ani da kuma ladan wahala da kaikawo a cikin karanta shi.
Fa’idoji
- Kwaɗaitarwa akan haddace Alƙur'ani da kyautata shi da yawaita karanta shi dan samun lada da sakamako, da kuma bayanin ɗaukakar matsayin wanda ya aikata hakan.
- Alƙali ya ce: Ba wai ma'anarsa cewa wanda yake guragura gurin karanta shi ya fi gwani lada ba, kai gwani ya fi yawan lada; domin shi gwani yana tare da mala'iku matafiya kuma yana da ladaddaki mai yawa, kuma bai ambaci wannan matsayin ga waninsa ba, to kuwa ta yaya wanda bai kula da Littafin Allah - Maɗaukakin sarki - ba da haddace shi da kyautata shi da yawan karanta shi da dirayarsa hakikanin kulawarsa har ya zama gwani a cikinsa zai riske shi.
- Ibnu Baaz ya ce: Wanda yake karanta Alƙur'ani alhali shi gwani ne a cikinsa, yana kyautata karatunsa, kuma yana haddarsa da kyau yana tare da mala'iku matafiya masu daraja, yana nufin: Idan ya kasance yana karanta shi a faɗa da aiki, ba wai mujarradin karantawar kawai ba, yana kyautata karatunsa kuma yana aiki da shi, shi yana tsaye da shi a lafazi da ma'ana.
Madogara
صحيح البخاري (6/ 166) (4937).
صحيح مسلم (1/ 549) (798).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 226).
تحفة الأحوذي بشرح جامع الترمذي، لمحمد المباركفوري (8/ 174).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص580).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (4/ 639).
شرح كتاب التوحيد من صحيح البخاري، لعبدالله الغنيمان (2/ 592).
فتح الباري بشرح صحيح البخاري، لابن حجر العسقلاني (9/ 127).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (12/ 562).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمصطفى الخِن وغيره (1/ 740).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي أمامة الباهلي رضي الله عنه قال: سمعتُ رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «اقرؤوا القرآنَ فإنَّه يأتي يوم القيامة شَفِيعًا لأصحابه، اقرؤوا الزَّهرَاوَين البقرةَ وسورةَ آل عِمران، فإنهما تأتِيان يوم القيامة كأنهما غَمَامَتان، أو كأنهما غَيَايَتانِ، أو كأنهما فِرْقانِ من طَيْر صَوافٍّ، تُحاجَّان عن أصحابهما، اقرؤوا سورة البقرة، فإن أخذها بَرَكة، وتركها حَسْرة، ولا تستطيعها البَطَلَة».
Daga Abu Umamah al-Bahili - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa: «Ku karanta Alƙur’ani domin zai zo ranar alƙiyama yana mai ceton ma'abotansa, Ku karanta surori biyu Baƙara da al-Imran, domin cewa su za su zo a ranar alƙiyama kamar giza-gizai ko kamar wata tawagar tsuntsaye sun yi sahu, suna kare ma'abocinsu, ku karanta Surat al-Baƙara don haddace ta albarka ne, kuma barinta asara ne, kuma matsafa ba zasu iya ta ba».
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar akan dawwama kan karatun Alƙur'ani; domin shi (Alkur’ani) zai yi ceto a ranar alƙiyama ga masu karanta shi masu aiki da shi, sannan ya ƙarfafa karanta surori biyu: Baƙara da al-Imran, kuma ya ambace su da Zahrawani masu haske; saboda haskensu da kuma shiryarawarsu, kuma lallai ladan karanta su da tadabburin ma'anoninsu da kuma aiki da abinda ke cikinsu, zasu zo ranar alƙiyama kamar gizagizai biyu ko wasunsu, ko ka ce su garken tsntsaye ne waɗanda suka shinfiɗa fukafukansu sashinsu na saduwa da sashi, suna yi wa ma'abocinsu inuwa kuma suna kare shi. Sannan (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ƙarfafa dawwama a kan karanta Suratul Baƙara da tadabburin ma'anoninta da kuma aiki da abinda ke cikinsu, kuma hakan a cikinsa akwai albarka da amfani mai girma a duniya da lahira, kuma barin hakan a cikinsa akwai asara da nadama a ranar alƙiyama, kuma daga cikin falalar wannan surar matsafa ba zasu iya cutar da wanda ya karantata ba.
Fa’idoji
- Umarni da karanta alƙur'ani da kuma yawaita hakan, kuma shi (Alkur’ani) zai ceci ma'abotansa a ranar alƙiyama, masu karanta shi, masu riƙo da shiriyarsa, masu tsayawa kan abinda ya yi umarni da shi, masu barin abinda ya hana.
- Falalar karanta Suatul Baƙara da al-Imran da kuma girman ladansu.
- Falalar karanta Suratul Baƙara, kuma cewa ita tana kare ma'abocinta daga tsafi.
Madogara
صحيح مسلم (1/ 553) (804).
مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي القاري (4/ 1460).
التنوير شرح الجامع الصغير، لمحمد الصنعاني (2/ 606).
شرح الأربعين النووية، لابن عثيمين (ص232).
معارج القبول بشرح سلم الوصول إلى علم الأصول، لحافظ الحكمي (2/ 846).
التَّحبير لإيضَاح مَعَاني التَّيسير، لمحمد الصنعاني (2/ 9).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل المبارك (ص579).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ النَّوَّاسِ بْنِ سَمْعَانَ الْأَنْصَارِيِّ رضي الله عنه عَنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «ضَرَبَ اللهُ مَثَلًا صِرَاطًا مُسْتَقِيمًا، وَعَلَى جَنْبَتَيْ الصِّرَاطِ سُورَانِ، فِيهِمَا أَبْوَابٌ مُفَتَّحَةٌ، وَعَلَى الْأَبْوَابِ سُتُورٌ مُرْخَاةٌ، وَعَلَى بَابِ الصِّرَاطِ دَاعٍ يَقُولُ: أَيُّهَا النَّاسُ، ادْخُلُوا الصِّرَاطَ جَمِيعًا، وَلَا تَتَعَرَّجُوا، وَدَاعٍ يَدْعُو مِنْ فَوْقِ الصِّرَاطِ، فَإِذَا أَرَادَ يَفْتَحُ شَيْئًا مِنْ تِلْكَ الْأَبْوَابِ، قَالَ: وَيْحَكَ لَا تَفْتَحْهُ، فَإِنَّكَ إِنْ تَفْتَحْهُ تَلِجْهُ، وَالصِّرَاطُ الْإِسْلَامُ، وَالسُّورَانِ: حُدُودُ اللهِ، وَالْأَبْوَابُ الْمُفَتَّحَةُ: مَحَارِمُ اللهِ، وَذَلِكَ الدَّاعِي عَلَى رَأْسِ الصِّرَاطِ: كِتَابُ اللهِ، وَالدَّاعِي مِنِ فَوْقَ الصِّرَاطِ: وَاعِظُ اللهِ فِي قَلْبِ كُلِّ مُسْلِمٍ».
Daga Nawwas Dan Sam'an Al’Ansary - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Allah Ya buga wani misali hanya ce madaidaiciya, a gefunan hanyar biyu akwai ganuwowi biyu, a cikinsu akwai budaddun kofofi, akan kofofin akwai sakakkun labulaye, a kofar hanyar akwai wani mai kira yana cewa; Yaku mutane, ku shigo hanyar gaba daya, kada ku karkace, da wani mai kiran kuma yana kira a birbishin hanyar, idan ya yi nufin ya bude wani abu daga wadancan kofofin, zai ce: Kaicanka kada ka bude shi , domin cewa kai idan ka bude shi zaka shige shi.
Tafarkin shi ne Musulunci, ganuwowin biyu kuma: Su ne iyakokin Allah, budaddun kofofin kuma: Su ne abubuwan da Allah Ya haramta, wannan mai kiran kuma akan tafarkin: Shi ne littafin Allah, mai kiran kuma a birbishin tafarkin: Mai wa'azin Allah ne (Ajiyoyin Allah) a cikin zuciyar kowane musulmi".
Tirmizi da Ahmad sun rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa; Allah Ya buga wani misali ga Musulunci da hanya madaidaiciya mikakkiya babu karkata a cikinta, agefan wannan hanyar akwai ganuwowi biyu, to bangwaye da suke kewaye da ita ta fuskarsa su ne iyakokin Allah, wasu budaddun kofofi suna shiga wadannan ganuwowi biyun su ne Abubuwan da Allah Ya haramta, akan wadannan kofofin akwai labulayen da basa bayyanar da wanda yake cikinsu ga mai wucewa akan hanyar, afarkon hanyar akwai wani mai kira yake fuskantar da mutane kuma yake shiryar da su yana ce musu: Ku tafi akansa ba tare da kun karkace zuwa wani bangaren ba, wannan mai kiran duk lokacin da mai tafiya akan tafarkin ya yi niyyar ya bude wani gwargwado mai sauki daga labulayen kofofin sai ya tsawatar masa ya ce da shi: Kaicanka kada ka bude shi! domin cewa kai idan ka bude shi zaka shigeshi kuma ba zaka sami damar kare kanka ba daga shiga, wannan mai kiran shi ne mai wa'azin Allah a cikin zuciyar kowane Musulmi.
Fa’idoji
- Musulunci shi ne addinin gaskiya, kuma shi ne tafarki madaidaici wanda zai sadar da mu zuwa Aljanna.
- Wajabcin lazimtar iyakokin Allah da abinda Ya halatta da abinda Ya haramta, kuma cewa sakaci a cikinsu yana gadar da halaka.
- Falalar Alkur’ani mai girma da kwadaitarwa akan aiki da shi, a cikinsa akwai shiriya da haske da tsira.
- Rahamar Allah ga bayinSa da abinda Ya ajiye shi a cikin zukatan muminai na a binda zai hanasu ya kuma wa'azantar da su daga fadawa a cikin halaka.
- Allah da rahamarSa Ya sanya shamakin da zai hana bayinSa afkawa cikin sabo.
- Daga cikin hanyoyin koyarwa akwai buga misali dan kusantowa da bayyanawa.
Madogara
سنن الترمذي (4/ 539) (2859)، مسند أحمد (29/ 181، 183) (17634)، جامع العلوم والحكم (2/161)، فيض القدير (4/253)، التنوير شرح الجامع الصغير (7/100)، الفتح الرباني لترتيب مسند الإمام أحمد بن حنبل الشيباني (1/ 83).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَيُحِبُّ أَحَدُكُمْ إِذَا رَجَعَ إِلَى أَهْلِهِ أَنْ يَجِدَ فِيهِ ثَلَاثَ خَلِفَاتٍ عِظَامٍ سِمَانٍ؟» قُلْنَا: نَعَمْ. قَالَ: «فَثَلَاثُ آيَاتٍ يَقْرَأُ بِهِنَّ أَحَدُكُمْ فِي صَلَاتِهِ خَيْرٌ لَهُ مِنْ ثَلَاثِ خَلِفَاتٍ عِظَامٍ سِمَانٍ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shin dayanku yana son idan ya koma zuwa iyalansa ya samu manyan taguwowi masu ciki masu giba?" muka ce: Eh. Ya ce; "To ayoyi uku dayanku zai karantasu a cikin sallarsa sun fiye masa alheri daga taguwowi uku manya masu ciki".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa ladan karanta ayoyi uku a cikin sallah; shi ne mafi alheri daga mutum ya sami taguwowi uku masu ciki manya a cikin gidansa.
Fa’idoji
- Bayanin falalar karanta Alkur’ani a cikin sallah.
- Ayyuka na gari su ne mafi alheri kuma mafi wanzuwa daga jin dadin duniya mai karewa.
- Wannan falalar ba ababen kayyadewa bane da karanta ayoyi uku kawai; duk lokacin da mai sallah ya kara karanta ayoyi a cikin sallarsa ladanta zai zama mafi alheri gare shi daga adadinsu daga taguwowi masu ciki.
Madogara
صحيح مسلم (1/ 552) (802)، إكمال المعلم (3/172)، الإفصاح عن معاني الصِّحاح (8/65)، فتح المنعم شرح صحيح مسلم (3/620)، البحر المحيط الثجاج (16/343).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن عبد الله بن عمرو رضي الله عنهما قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «يقالُ لصاحبِ القرآن: اقرَأ وارتَقِ، ورتِّل كما كُنْتَ ترتِّل في الدُنيا، فإن منزِلَكَ عندَ آخرِ آية تقرؤها».
Daga Abdullahi dan Amr dan Aas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Za'a ce da ma'abocin Alkur’ani: Karanta ka daukaka, ka rera kamar yadda ka kasance kana rerawa a duniya, domin cewa matsayinka zai tasayane a karshen ayar da ka karantata".
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i a cikin alkubra haka Ahmad suka ruwaito shiDarajaHasan ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa, za’a ce da makarancin Alkur’ani, mai aiki da abinda ke cikinsa, wanda ya lazimceshi a karatu da hadda idan ya shiga Aljanna: Ka karanta ka daukaka da wannan a cikin darajojin Aljanna, ka rera kamar yadda ka kasance kana rerawa a duniya da karanta shi da bi ahankali da nutsuwa; domin cewa matsayinka na karshen ayar da ka karantata ne.
Fa’idoji
- Sakayya tana daidai da dacewar ayyuka a yawa da yanayi.
- Kwadaitarwa akan karatun Alkur’ani da kyautata shi da hardace shi da tadabburi da kuma aiki da shi.
- Aljanna masaukaice darajoji masu yawa, ma'abota Alkur’ani zasu samu madaukakan darajoji a cikinta.
Madogara
سنن أبي داود (2/ 592) (1464)، سنن الترمذي (5/ 35) (2914)، مسند أحمد (11/ 403) (6799)، السنن الكبرى للنسائي (7/ 272) (8002)، معالم السنن (1/290)، تحفة الأحوذي (8/187)، عون المعبود وحاشية ابن القيم (4/ 237).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن عُقبة بن عامر الجُهني رضي الله عنه قال: قال رسولُ الله صلَّى الله عليه وسلم: «الجاهِرُ بالقرآن كالجاهِرِ بالصَّدَقَةِ، والمُسِرُّ بالقرآن كالمُسِرِّ بالصَّدَقَة».
Daga Uqubah Dan Amir Al-Juhani - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Mai bayyanar da Alkur’ani kamar mai bayyanar da sadaka ne, mai boye Alkur’ani kamar mai boye sadaka ne".
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i ne Suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa mai bayyanar da karatun Alkur’ani kamar mai bayyanar da bayar da sadaka ne, mai boye karatun Alkur’ani kamar mai boye bayar da sadaka ne.
Fa’idoji
- Boye karatun Alkur’ani shi ya fi , kamar yadda boye sadaka shi yafi, dan abinda yake cikinsa na tsarkake niyya da nisanta daga riya da jiji da kai, sai dai idan bukata da maslaha sun bukaci bayyanarwar kamar koyar da Alkur’ani .
Madogara
سنن أبي داود (2/ 494) (1333)، سنن الترمذي (5/ 40) (2919)، سنن النسائي (5/ 80) (2561)، الكاشف عن حقائق السُّنن (5/1688)، شرح أبي داود للعيني (5/238)، تحفة الأحوذي (8/ 191)، التنوير في شرح الجامع الصغير (5/286).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com