Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Duk wanda ya karanta wani harafi daga littafin Allah, to, yana da lada, kuma kowane lada za a ninkashi goma

عن عبد الله بن مسعود رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «مَنْ قَرَأَ حَرْفًا مِنْ كِتَابِ اللهِ فَلَهُ بِهِ حَسَنَةٌ، وَالْحَسَنَةُ بِعَشْرِ أَمْثَالِهَا، لَا أَقُولُ {الم} حَرْفٌ، وَلَكِنْ {أَلِفٌ} حَرْفٌ، وَ{لَامٌ} حَرْفٌ، وَ{مِيمٌ} حَرْفٌ».
An karbo daga Abdullahi Ɗan Mas’ud Allah ya yarda da shi ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Duk wanda ya karanta wani harafi daga littafin Allah, to, yana da lada, kuma kowane lada za a ninkashi goma. amma ba zan ce Alif Laam Meem harafi ɗaya ba ne, sai dai Alif, harafi ne, Laam harafi ne, Meem harafi ne"
Tirmizi ne ya ruwaito shiDarajaHasan ne
Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ba da labari cewa kowanne Musulmi ne ya karanta harafi daga littafin Allah, to, yana da lada a wannan karatun, kuma za a ninka masa lada zuwa ninki goma. Sannan ya yi bayanin hakan da faɗinsa: Ban ce : Alif, Laam, Meem, harafi ba ne, sai dai Alifun harafi ne, Lamun harafi ne, Mimun harafi ne, sai ya kasance harufa uku, lada talatin kenan.

Fa’idoji
  1. Kwaɗaitarwa a kan yawaita karatun Alkur’ani.
  2. Mai karatu a kowanne harafi na kalma da yake rerawa yana da lada da za’a nunka sau goma.
  3. Yalwatuwar rahamar Allah, da kuma karamcinSa, ta yadda ya nunka wa bayinSa lada; falala ce da karamci daga gareShi.
  4. Falalar Alƙur’ani a kan wani zancen da ba shi ba, da yadda ake bauta da karanta shi, saboda shi zancen Allah ne.
Madogara

سنن الترمذي (5/ 33) (2910). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 229). سلسلة الأحاديث الصحيحة، للألباني (7/ 970). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (4/ 655). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمصطفى الخِن وغيره (1/ 742).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALAR KULAWA DA ALƘUR'ANI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com

Duk wanda ya karanta wani harafi daga littafin Allah, to, yana da lada, kuma kowane lada za a ninkashi goma · Hadisai tare da sharhi · Sabīl