Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Gangaran a karatun Alƙur'ani yana tare da manyan mala'iku masu biyayya ga Allah, kuma wanda yake karanta Alƙur'ani kuma yake guragura a cikinsa yana mai shan wuya to yana da lada biyu

عَنْ عَائِشَةَ رضي الله عنها قَالَتْ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «الْمَاهِرُ بِالْقُرْآنِ مَعَ السَّفَرَةِ الْكِرَامِ الْبَرَرَةِ، وَالَّذِي يَقْرَأُ الْقُرْآنَ وَيَتَتَعْتَعُ فِيهِ، وَهُوَ عَلَيْهِ شَاقٌّ، لَهُ أَجْرَانِ».
Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Gangaran a karatun Alƙur'ani yana tare da manyan mala'iku masu biyayya ga Allah, kuma wanda yake karanta Alƙur'ani kuma yake guragura a cikinsa yana mai shan wuya to yana da lada biyu.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda yake karanta Alƙur'ani, alhali shi mai kyakkyawar hadda ne mai kyautatawa, kuma gwani haziƙi a karanta shi, to a lahira yana da ladan da zai zama a matsayinsa tare da manyan mala'iku matafiya masu karamci. Kuma wanda yake karanta Alƙur'ani yake guragura a cikinsa yana kaikawo a karanta shi; dan raunin haddarsa alhali shi tare da hakan yana riƙe da shi, kuma yana wahalar da shi to shi yana da lada biyu; ladan karatun Alkur'ani da kuma ladan wahala da kaikawo a cikin karanta shi.

Fa’idoji
  1. Kwaɗaitarwa akan haddace Alƙur'ani da kyautata shi da yawaita karanta shi dan samun lada da sakamako, da kuma bayanin ɗaukakar matsayin wanda ya aikata hakan.
  2. Alƙali ya ce: Ba wai ma'anarsa cewa wanda yake guragura gurin karanta shi ya fi gwani lada ba, kai gwani ya fi yawan lada; domin shi gwani yana tare da mala'iku matafiya kuma yana da ladaddaki mai yawa, kuma bai ambaci wannan matsayin ga waninsa ba, to kuwa ta yaya wanda bai kula da Littafin Allah - Maɗaukakin sarki - ba da haddace shi da kyautata shi da yawan karanta shi da dirayarsa hakikanin kulawarsa har ya zama gwani a cikinsa zai riske shi.
  3. Ibnu Baaz ya ce: Wanda yake karanta Alƙur'ani alhali shi gwani ne a cikinsa, yana kyautata karatunsa, kuma yana haddarsa da kyau yana tare da mala'iku matafiya masu daraja, yana nufin: Idan ya kasance yana karanta shi a faɗa da aiki, ba wai mujarradin karantawar kawai ba, yana kyautata karatunsa kuma yana aiki da shi, shi yana tsaye da shi a lafazi da ma'ana.
Madogara

صحيح البخاري (6/ 166) (4937). صحيح مسلم (1/ 549) (798). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 226). تحفة الأحوذي بشرح جامع الترمذي، لمحمد المباركفوري (8/ 174). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص580). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (4/ 639). شرح كتاب التوحيد من صحيح البخاري، لعبدالله الغنيمان (2/ 592). فتح الباري بشرح صحيح البخاري، لابن حجر العسقلاني (9/ 127). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (12/ 562). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمصطفى الخِن وغيره (1/ 740).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALAR KULAWA DA ALƘUR'ANI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com