Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

HADDODI

Hadisai 18

‌Wanda ya aikata laifin da za'a iya yi masa haddi sai aka gaggauto da uƙubarsa a duniya to Allah Shi ne Mafi karamcin Ya yi wa bawanSa uƙuba (biyu, daya aduniya da kuma) a lahira

عَنْ عَلِيٍّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَنْ أَصَابَ حَدًّا فَعُجِّلَ عُقُوبَتَهُ فِي الدُّنْيَا فَاللَّهُ أَعْدَلُ مِنْ أَنْ يُثَنِّيَ عَلَى عَبْدِهِ العُقُوبَةَ فِي الآخِرَةِ، وَمَنْ أَصَابَ حَدًّا فَسَتَرَهُ اللَّهُ عَلَيْهِ وَعَفَا عَنْهُ فَاللَّهُ أَكْرَمُ مِنْ أَنْ يَعُودَ فِي شَيْءٍ قَدْ عَفَا عَنْهُ».
Daga Aliyu - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «‌Wanda ya aikata laifin da za'a iya yi masa haddi sai aka gaggauto da uƙubarsa a duniya to Allah Shi ne Mafi karamcin Ya yi wa bawanSa uƙuba (biyu, daya aduniya da kuma) a lahira, wanda ya aikata laifin da za’a yi masa haddi sai Allah Ya suturta shi kuma Ya yi masa afuwa to Allah Shi ne Mafi karamcin ya dawo da abinda Ya riga Ya yi afuwarsa».
Tirmizi ne ya Rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya aikata wani saɓon da yake wajabta haddin shari'a, kamar zina da sata, sai ya samu uƙubarsa kuma aka tsayar masa da haddi a duniya, to lallai hakan zai shafe masa wannan saɓon, kuma zai shafe uƙubarsa ta lahira; domin cewa Allah Shi ne Mafi karamci kuma Mafi jin ƙan ya haɗawa bawanSa uƙuba biyu. Wanda kuma Allah Ya suturta shi a duniya, ba a yi masa uƙuba ba akan wannan saɓon, kuma Allah Ya yi masa afuwa Ya gafarta masa, to Allah Shi ne Mafi buwaya kuma Mafi girma Mafi karamcin ya dawo da uƙubar zunubin da Ya riga Ya gafarta shi kuma Ya yi afuwarsa.

Fa’idoji
  1. Girman adalcin Allah da karamcinSa da kuma rahamarSa.
  2. Tsaida haddi a duniya yana kankare zunubi.
  3. Wanda ya afka a zunubin da a cikinsa akwai haddi yana kamata ya suturta kansa tunda Allah Ya suturta shi, kuma ya yi gaggawar tuba na gaskiya.
Madogara

سنن الترمذي (4/ 312) (2626). سنن ابن ماجه (3/ 627) (2604). مرشد ذوي الحجا والحاجة إلى سنن ابن ماجه والقول المكتفى على سنن المصطفى (15/ 224). التيسير بشرح الجامع الصغير (2/ 399). فيض القدير (6/ 65).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Lallai Allah Ya wajabta farillai, dan haka kada ku tozartasu, kuma Ya sa iyakoki, dan haka kada ku ƙetaresu, kuma Ya haramta wasu abubuwa, dan haka kada ku ketasu, kuma Ya yi shiru game da wasu abubuwa dan rahama gareku badan mantuwa ba dan, haka kada ku yi bincike game da su

عَنْ أَبِي ثَعْلَبَةَ الخُشَنِيِّ جُرْثُومِ بن نَاشِرٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنْ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَال: «إِنَّ اللَّهَ فَرَضَ فَرَائِضَ فَلَا تُضَيِّعُوهَا، وَحَدَّ حُدُودًا فَلَا تَعْتَدُوهَا، وَحَرَّمَ أَشْيَاءَ فَلَا تَنْتَهِكُوهَا، وَسَكَتَ عَنْ أَشْيَاءَ رَحْمَةً لَكُمْ غَيْرَ نِسْيَانٍ فَلَا تَبْحَثُوا عَنْهَا».
Daga Abu Sa'alabata alKhushani Jursumu Ibnu Nashir - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Lallai Allah Ya wajabta farillai, dan haka kada ku tozartasu, kuma Ya sa iyakoki, dan haka kada ku ƙetaresu, kuma Ya haramta wasu abubuwa, dan haka kada ku ketasu, kuma Ya yi shiru game da wasu abubuwa dan rahama gareku badan mantuwa ba dan, haka kada ku yi bincike game da su».
Dar Al-Kutni ya ruwaito shi a cikin Sunan din sa da waninsaDarajaNawawi ya ce: Hadisi ne mai kyau
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa Allah Ya wajabta wasu abubuwa kuma Ya faralanta wasu farillai, to ku lazimcesu kada ku yi sakaci a cikinsu ta hanyar barinsu ko wulaƙantar da su, kuma Ya sanya muku shamaki da abubuwan da ya tsawatar abubuwan ƙaddarawa waɗanda zasu kareku kuma su tsawatar da ku daga abin da bai yarda da shi ba, dan haka kada ku yi ƙari kan a bin da shari'a ta yi muku umarni da shi, kuma Ya haramta wasu abubuwan da Ya haramta dan haka kada ku aikata su kai karma ku kusancesu, kuma bayan wannan Ya barsu kuma Ya yi shiru game da su dan rahama ga bayinSa, sai suka wanzu akan asalin halaccinsu dan haka kada ku yi bincike game da su.

Fa’idoji
  1. Hadisin dalili ne akan cewa Allah Shi ne Mai shar'antawa, al'amari yana hannunSa - tsarki ya tabbatar maSa -.
  2. Hadisin ya ƙunshi wasu ƙa'idojin shari'a na hukunci da kuma halattawa; domin hukunci na shari'a ko dai an yi shiru game da shi ko kuma an yi magana a kansa, hakan kuma ko dai: An yi umarni da shi na wajabci ko mandubi, ko an yi hani game da shi hani na haramci, ko na karhanci, ko kuma ya halatta.
  3. Cewa abinda Allah Ya yi shiru game da shi bai wajabta shi ba, kuma bai sa masa iyaka ba, kuma bai yi hani game da shi ba to shi halal ne.
  4. Kyakkyawan bayanin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - in da ya koro hadisin da wadannan rabe-raben a bayyane.
  5. Wajabcin kiyayewa akan abubuwan da Allah - Maɗaukakin sarki ya wajabta
  6. Haramcin ƙetare iyakokin Allah - Maɗaukakin sarki -.
Madogara

سنن الدارقطني (4396). المعجم الكبير للطبراني (22/221). جامع العلوم والحكم (ص617). شرح الأربعين النووية للعثيمين (ص309). توضيح الأحكام من بلوغ المرام (6/ 210).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com