Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

HADDIN GIYA

Hadisai 5

Cewa Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- anzo masa da wani Mutum ya sha giya, sai aka yi masa Bulala da zarbar Dabino kwatankwacin Arba'in

عن أنس بن مالك رضي الله عنه «أَنَ النّبي صلى الله عليه وسلم أُتِي بِرَجُل قَدْ شَرِب الْخَمْرَ، فَجَلَدَهُ بِجَريدة نحو أربعين»
An rawaito daga Anas Bn Malik -Allah ya yarda da shi- "Cewa Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- anzo masa da wani Mutum ya sha giya, sai aka yi masa Bulala da zarbar Dabino kwatankwacin Arba'in"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Wani Mutum ya sha giya a lokacin Annabi SAW sai aka yi masa Bulala da Zarbar Dabino kwatankwacin Bulala Arba’in, Kuma Abubakar –Allah ya yarda das hi- yayyi Bulala ga Mashayin giya a lokacin Halifancinsa kwatankwacin Bulalar Manzon Allah SAW, yayin da lokacin Halifancin Umar ya zo, aka samu bude garuruwa da yawa, Musulmai suka cudanya da wasun su, sai shan giyar ya karu, sai ya Shawarci Malaman Sahabbai akan haddin da zai rika yi musu don ya hana su Shan giyar, kamar yadda haka Al-adarsa take idan Muhimman abubuwa suka faru, da kuma abubuwan da suke bukatar Ijtihadi, saboda Mutane sun karu wajen Shan giya a lokacinsa, sai Abdul-Rahman Bn Auf y ace: kasanya shi daidai da mafi karancin Haddi, shi ne Bulala Tamanin, kuma shi ne Haddin wanda yayi Kazafi, Sai Umar ya sanya shi Bulala Tamanin, to wannan Karin Jan kunne kuma ya danganta da abunda Shugaba ya gani

Madogara

- صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422ه. - صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، 1423 هـ - عمدة الأحكام من كلام خير الأنام صلى الله عليه وسلم لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، ط2، دار الثقافة العربية، دمشق ، بيروت، مؤسسة قرطبة، 1408 هـ - تأسيس الأحكام للنجمي، ط2، دار علماء السلف، 1414هـ - تيسير العلام شرح عمدة الأحكام للبسام، حققه وعلق عليه وخرج أحاديثه وصنع فهارسه: محمد صبحي بن حسن حلاق، ط10، مكتبة الصحابة، الأمارات - مكتبة التابعين، القاهرة، 1426 هـ - الإلمام بشرح عمدة الأحكام للشيخ إسماعيل الأنصاري-مطبعة السعادة-الطبعة الثانية 1392ه. الإعلام بفوائد عمدة الأحكام لا بن الملقن المحقق: عبد العزيز بن أحمد بن محمد المشيقح - دار العاصمة للنشر والتوزيع، المملكة العربية السعودية الطبعة: الأولى، 1417 هـ - 1997 م.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

"Duk abun Shan da ya sa Maye to Haramun ne"

عن عائشة رضي الله عنها: «أَنَّ رسول الله صلى الله عليه وسلم سُئِل عن الْبِتْعِ؟ فقال: كل شَرَابٍ أَسْكَر فهو حَرَامٌ».
An rawaito daga Nana Aisha -Allah ya yarda da ita: "Cewa Manzon Allah SAW an tambayr shi game da tsumi sai ya ce: "Duk abun Shan da ya sa Maye to Haramun ne"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

- صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422ه. - صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، 1423 هـ - عمدة الأحكام من كلام خير الأنام صلى الله عليه وسلم لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، ط2، دار الثقافة العربية، دمشق ، بيروت، مؤسسة قرطبة، 1408 هـ - تأسيس الأحكام للنجمي، ط2، دار علماء السلف، 1414هـ. - الإلمام بشرح عمدة الأحكام لإسماعيل الأنصاري، ط1، دار الفكر، دمشق، 1381ه - تيسير العلام شرح عمدة الأحكام للبسام، حققه وعلق عليه وخرج أحاديثه وصنع فهارسه: محمد صبحي بن حسن حلاق، ط10، مكتبة الصحابة، الإمارات - مكتبة التابعين، القاهرة، 1426 هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Haramta giya ya sauka ne kuma ana yin ta daga abubuwa biyar ne: inibi, dabino, zuma, alkama, da sha'ir"

عن عَبْدُ الله بن عمر رضي الله عنهما أن عمر قال -على منبر رسول الله- صلى الله عليه وسلم : "أما بعد، أيها الناس، إنه نزل تحريم الخمر وهي من خمسة: مِنَ العنب، والتمر، والعسل، والحنطة، والشعير. والخمر: مَا خَامَرَ العَقْلَ. ثَلاثٌ وَدِدْتُ أَنَّ رَسُولَ الله صلى الله عليه وسلم كَانَ عَهِدَ إلَيْنَا فِيهَا عَهْداً نَنْتَهِي إلَيْهِ: الجَدُّ، والكَلالَةُ، وأَبْوَابٌ مِنَ الرِّبَا".
Daga Abdullah Dan Umar -Allah ya yarda da su- cewa Umar ya ce:- yana kan minbarin Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi:" Bayan haka, ya ku mutane,tabbas hukuncin haramta giya ya sauka alhaliana yin ta ce daga abubuwa biyar: Inibi,da Zuma,da Alkama da Sha'ir; bin da ake cewa giya: Shi ne duk abin da zai gusar da hankali
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Umar Dan Khaddab -Allah ya yarda da shi- ya yi huduba a masallaci Manzon Allah -tsira da aminci su tabbata a gare shi- kuma akan minbarinsa, kuma ya tabbatar da cewa lallai giya itaa ce duk wani abu da zai iya jirkita hankali, ba wacce aka yi da inibi ba kawai, duk wani abin sha wanda zai iyi jirkita hankali ko da kuwa da dabino ko zuma ko alkama to suma sun zama giya, kuma hakika Uma r ya fadi abubuwa uku a cikin Hudubarsa wanda akawai rikitarwa a cikinsa kuma yayi burin ace Annabi yana raye, cikim wadan nan abubuwa guda uka da ya da aka kure matuka izuwa gare shi sune Gadon Kaka, da Gadon Mamacin da bashi da Da ko Mahaifi, da wasu abubuwa kan Riba, kuma Alhamdulillah cewa lallai Hukuncin wannan abubuwa guda uku sananne ne, kuma wannan ba yana nufin cewa Annabi baiyi bayaninsu ba Hakika Annabi ya Isar da Sakonsa, kuma ya bada Amana, kuma ya isar da sakon Allah abun da yafi wannan ma buya da kuma wanda ya fi wannan ma girma kuma Umar yana son yakasance akawai nassi gwari gwari ne a kansu da baya bukatar wani Ijtihadi.

Madogara

صحيح البخاري، محمد بن إسماعيل البخاري الجعفي، تحقيق: محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى 1422هـ. صحيح مسلم، مسلم بن الحجاج القشيري النيسابوري، تحقيق محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، الطبعة: 1423هـ. تأسيس الأحكام، أحمد بن يحيى النجمي، دار علماء السلف، الطبعة: الثانية 1414هـ. تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، عبد الله بن عبد الرحمن البسام، تحقيق: محمد صبحي حلاق، مكتبة الصحابة، الإمارات، مكتبة التابعين، القاهرة، الطبعة: العاشرة 1426هـ. عمدة الأحكام من كلام خير الأنام -صلى الله عليه وسلم- لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، دار الثقافة العربية، دمشق، بيروت، مؤسسة قرطبة، الطبعة: الثانية 1408هـ. المعجم الوسيط، مجمع اللغة العربية بالقاهرة، (إبراهيم مصطفى، أحمد الزيات، حامد عبد القادر، محمد النجار)، الناشر: دار الدعوة.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

An zuwarwa Manzon Allah SAW da wani Mutum ya Sha Giya, sai ya ce: "Ku masa Duka"

عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: أُتِي النبي صلى الله عليه وسلم برجل قد شَرِب خمرا، قال: «اضربوه». قال أبو هريرة: فمنا الضارب بيده، والضارب بنعله، والضارب بثوبه، فلما انصرف، قال بعض القوم: أخزاك الله، قال: «لا تقولوا هكذا، لا تُعِينُوا عليه الشيطان».
Daga Abu huraira -Allah ya yarda da shi- ya ce: An zuwarwa Manzon Allah SAW da wani Mutum ya Sha Giya, sai ya ce: "Ku masa Duka" sai Abu huraira ya ke cewa: daga cikin mu akwai mai dukansa da hannu da Mai dukansa da Takalmi, da mai dukansa da tufarsa, yayin da ya juya sai wasu daga cikin Mutane suka ce: Allah ya Qasqantaka, sai ya ce: "Kada ku ce haka, kada ku taimakawa shixan a kansa"
Buhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

- صحيح البخاري، للإمام أبي عبد الله محمد بن إسماعيل البخاري، عناية محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة، الطبعة الأولى، 1422هـ. - كنوز رياض الصالحين، حمد بن ناصر العمار، دار كنوز إشبيليا، الطبعة الأولى، 1430ه. - شرح رياض الصالحين، للشيخ محمد بن صالح العثيمين، مدار الوطن، الرياض، 1426هـ. - دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين، لمحمد بن علان الشافعي، تحقيق خليل مأمون شيحا، دار المعرفة، بيروت، الطبعة الرابعة، 1425ه. - بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، تأليف سليم الهلالي، دار ابن الجوزي، الطبعة الأولى، 1418ه. - نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، تأليف د. مصطفى الخِن وغيره، مؤسسة الرسالة، بيروت، الطبعة الرابعة عشرة، 1407هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kada ku tsine masa, na rantse da Allah ban san wani abu daga gare shi ba sai dai yana son Allah da ManzonSa

عَنْ عُمَرَ بْنِ الخَطَّابِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ: أَنَّ رَجُلًا عَلَى عَهْدِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ اسْمُهُ عَبْدَ اللَّهِ، وَكَانَ يُلَقَّبُ حِمَارًا، وَكَانَ يُضْحِكُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، وَكَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَدْ جَلَدَهُ فِي الشَّرَابِ، فَأُتِيَ بِهِ يَوْمًا فَأَمَرَ بِهِ فَجُلِدَ، فَقَالَ رَجُلٌ مِنَ القَوْمِ: اللَّهُمَّ الْعَنْهُ، مَا أَكْثَرَ مَا يُؤْتَى بِهِ؟ فَقَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لاَ تَلْعَنُوهُ، فَوَاللَّهِ مَا عَلِمْتُ أَنَّهُ يُحِبُّ اللَّهَ وَرَسُولَهُ».
Daga Umar Ibnul Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi -: Cewa wani mutum a zamanin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sunansa Abdullahi, kuma ya kasance ana yi masa laƙabi da jaki, ya kasance yana sa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - dariya, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance ya yi masa bulala saboda giya, sai aka zo da shi wata rana sai ya sa aka yi masa bulala, sai wani mutum daga cikin mutanen ya ce: Ya Allah Ka tsine masa, ina mamakin yawan abin da ake zuwa da shi saboda shi?! sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ku tsine masa, na rantse da Allah ban san wani abu daga gare shi ba sai dai yana son Allah da ManzonSa".
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

A zamanin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akwai wani mutum sunansa Abdullahi, ana yi masa laƙabi da jaki, ya kasance yana sa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - dariya a cikin wasu daga cikin kalamansa, (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya kasance ya yi masa bulala saboda giya, sai wata rana aka zo da shi ya sha giya sai ya sa aka yi masa bulala. Sai wani daga cikin mahalarta ya zage shi, ya ce: Allah Ya tsine masa, ya mamakin yawan zuwan da ake yi da shi ya sha giya?! sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Kada ku yi masa mummunar addu'ar korewa daga rahamar Allah, na rantsae da Allah ban san wani abuba daga gare shi sai cewa shi yana son Allah da ManzonSa.

Fa’idoji
  1. Babu korewa tsakanin aikata abin da aka hana da kuma tabbacin son Allah da MaznonSa a cikin zuciyar mai aikata laifin; domin shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda aka ambata yana son Allah da ManzonSa tare da abin da ya bijiro daga gare shi .
  2. Mai aikata babban laifi idan ya mutu alhali shi yana nacewa akan wani abu na laifin, to yana ƙarƙashin mashi'a, idan Allah Ya so Ya yi masa gafara idan Ya so kuma Ya yi masa azaba, babu wani mutum daga cikin musulmai da za'a dawwamar da shi a cikin wuta.
  3. Hanin tsinewa mashayin giya da sunansa; dan yi wuwar samuwar wani abu mai hanawa daga riskuwar tsinuwar; domin tsinewa wani mutum da sunansa da yi masa mummunar addu'a zai iya sa shi ci gaba, ko ya sa shi yanke ƙauna daga karɓar tuba.
  4. Halaccin tsinewa wanda ba’a ayyana sunansa ba wanda kuma ya siffantu da hakan.
Madogara

صحيح البخاري (8/ 158) (6780). إرشاد الساري لشرح صحيح البخاري (9/ 452). البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (29/ 394).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com