Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

HADDIN RIDDA

Hadisai 2

Kada Ku yi azaba da azabar Allah

عَنْ عِكْرِمَةَ: أَنَّ عَلِيًّا رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ حَرَّقَ قَوْمًا، فَبَلَغَ ابْنَ عَبَّاسٍ فَقَالَ: لَوْ كُنْتُ أَنَا لَمْ أُحَرِّقْهُمْ لِأَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «لاَ تُعَذِّبُوا بِعَذَابِ اللَّهِ»، وَلَقَتَلْتُهُمْ كَمَا قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ بَدَّلَ دِينَهُ فَاقْتُلُوهُ».
Daga Ikramah: Cewa Aliyu - Allah Ya yarda da shi - ya ƙona wasu mutane, sai labarin ya kaiwa Ibnu Abbas sai ya ce: Da ace ni ne ba zan ƙonasu ba; domin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Kada Ku yi azaba da azabar Allah», da na kashe su kamar yadda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Duk wanda ya canja Addininsa to ku kashe shi».
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Aliyu ibnu Abi Ɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya yi ijtihadi sai ya ƙona wasu mutane daga cikin zindiƙai waɗanda suka yi ridda suka bar Musulunci (ya Kona su) da wuta, sai labarin hakan ya kai ga Abdullahi ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su -, sai ya ƙarfafe shi akan kisan su; sai dai ya yi inkarin ƙona su da wuta. Kuma ya ce: Da ace nine a matsayinsa da ban ƙonasu da wuta ba; domin shi Annabi- tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa babu mai yin azaba da wuta sai Ubangijin wuta, saidai kashesu ya wadatar, inda (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Duk wanda ya yi ridda daga Musulunci ya canja Addinisa zuwa wani Addinin daban to ku kashe shi.

Fa’idoji
  1. Wajabcin kashe wanda ya yi ridda ya bar Musulunci da ijma'in ma'abota ilimi, hakan da sharuɗɗansa, bamai aikata haka sai shugaba da alƙali.
  2. Faɗinsa: "Wanda ya canja Addininsa to ku kashe shi" wato: Wanda ya yi ridda daga Musulunci: Hukunci ne gamamme ga maza da mata.
  3. Wanda ya yi ridda ba'a barinsa akan riddarsa, kai za'a kira shi zuwa ga Musulunci, idan bai amsa ba sai a kashe shi.
  4. A cikin wannan hadisin akwai hani akan azabtarwa da wuta, kuma haddodi ba'a zartar da su da wuta.
  5. Falalar Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su -, da yalwar iliminsa da fahimtarsa da hadisan Annbi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  6. A cikin wannan akwai ladabin inkari akan wanda ya saɓa.
Madogara

صحيح البخاري (4/ 61) (3017). عمدة القاري شرح صحيح البخاري، لبدر الدين العيني (14/ 264). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (8/ 364). توضيح الأحكام شرح بلوغ المرام، لعبد الله البسام (6/ 204). فتح ذي الجلال والإكرام بشرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (5/ 218). الإفصاح عن معاني الصحاح، لابن هبيرة (3/ 190). التوضيح لشرح الجامع الصحيح، لابن الملقن (18/ 58). نيل الأوطار، للشوكاني (7/ 225).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Wasu mutane daga Ukl ko Urainah suka zo (wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -), sai suka ƙyamaci zama a Madina

عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَدِمَ أُنَاسٌ مِنْ عُكْلٍ أَوْ عُرَيْنَةَ، فَاجْتَوَوْا المَدِينَةَ فَأَمَرَهُمُ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بِلِقَاحٍ، وَأَنْ يَشْرَبُوا مِنْ أَبْوَالِهَا وَأَلْبَانِهَا، فَانْطَلَقُوا، فَلَمَّا صَحُّوا قَتَلُوا رَاعِيَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، وَاسْتَاقُوا النَّعَمَ، فَجَاءَ الخَبَرُ فِي أَوَّلِ النَّهَارِ، فَبَعَثَ فِي آثَارِهِمْ، فَلَمَّا ارْتَفَعَ النَّهَارُ جِيءَ بِهِمْ، فَأَمَرَ فَقَطَعَ أَيْدِيَهُمْ وَأَرْجُلَهُمْ، وَسُمِرَتْ أَعْيُنُهُمْ، وَأُلْقُوا فِي الحَرَّةِ، يَسْتَسْقُونَ فَلاَ يُسْقَوْنَ، قَالَ أَبُو قِلاَبَةَ: فَهَؤُلاَءِ سَرَقُوا وَقَتَلُوا، وَكَفَرُوا بَعْدَ إِيمَانِهِمْ، وَحَارَبُوا اللَّهَ وَرَسُولَهُ.
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wasu mutane daga Ukl ko Urainah suka zo (wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -), sai suka ƙyamaci zama a Madina sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarce su suje gurin raƙuman (zakka), kuma su sha fitsarinsu da nononsu, sai suka tafi, lokacin da suka samu lafiya sai suka kashe mai kiwon (dabbobin) Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, suka kora dabbobin, sai labari ya zo a farkon yini, sai ya aika aka bi bayansu, lokacin da rana ta ɗaga sai aka zo da su, sai ya yi umarni a yanke hannayensu da ƙafafuwansu, kuma aka tsire idanuwansu, aka jefasu a cikin zafin rana, suna neman a shayar da su ruwa amma ba'a shayar da su ba. Abu Ƙilabah ya ce: Waɗannan sun yi sata sun yi kisa, sun kafirta bayan sun yi imani, sun yaƙi Allah da ManzonSa.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Wasu mutane daga ƙabilu biyu na Ukl da Urainah waɗanda su musulmai ne sun zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai wata cuta ta samesu wacce cikinsu ya kumbura, kuma suka ƙyamaci zama a Madina saboda abincinta da iskarta ba su dace da su ba. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarcesu su je inda raƙuman zakka suke, su sha fitsarinsu da nononsu, sai suka tafi, lokacin da suka samu lafiya suka yi ƙiba launinsu ya dawo musu sai suka kashe mai kiwon dabbobin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, suka kora raƙuman, sai labari ya zo a farkon yini (da safe), sai ya aika a nemo su, sai aka riskesu, lokacin da rana ta ɗaga sai aka zo da su gurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a ɗaure, sai ya yi umarni a yanke hannayensu da ƙafafuwansu, kuma aka tsiyayar da idanuwansu, domin haka suka yi wa makiyayin, kuma aka jefasu a cikin zafin rana, sunan neman a shayar da su ruwa amma ba'a shayar da su, har suka mutu. Abu Ƙilabah ya ce: Lallai su sun yi sata, sun yi kisa, sun kafirce bayan sun yi imani, kuma sun yaƙi Allah da ManzonSa.

Fa’idoji
  1. Tsarkin fitsarin dukkan abinda ake cin namansa.
  2. Halaccin magani da nonon rakuma da kuma fitsarinsu.
  3. Shar'ancin yin tamka (a yi wa mutum yadda ya yi wa wani) a cikin ƙisasi, kuma hani akan musla (daddatsa mutum) abin ɗauka ne ta hanyar da bata sakayya ko ƙisasi ba.
  4. Kashe jama'a idan sun kashe mutum ɗaya daidai ne sun kashe shi ta hanyar kisan gilla ne ko kuma ta hanyar fashi.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 56) (233). صحيح مسلم (3/ 1296) (1671). إرشاد الساري لشرح صحيح البخاري (1/ 298). عمدة القاري شرح صحيح البخاري (3/ 154). التوضيح لشرح الجامع الصحيح (4/ 455). النهاية في غريب الحديث والأثر (1/ 318).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com