Wasu mutane daga ƙabilu biyu na Ukl da Urainah waɗanda su musulmai ne sun zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai wata cuta ta samesu wacce cikinsu ya kumbura, kuma suka ƙyamaci zama a Madina saboda abincinta da iskarta ba su dace da su ba. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarcesu su je inda raƙuman zakka suke, su sha fitsarinsu da nononsu, sai suka tafi, lokacin da suka samu lafiya suka yi ƙiba launinsu ya dawo musu sai suka kashe mai kiwon dabbobin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, suka kora raƙuman, sai labari ya zo a farkon yini (da safe), sai ya aika a nemo su, sai aka riskesu, lokacin da rana ta ɗaga sai aka zo da su gurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a ɗaure, sai ya yi umarni a yanke hannayensu da ƙafafuwansu, kuma aka tsiyayar da idanuwansu, domin haka suka yi wa makiyayin, kuma aka jefasu a cikin zafin rana, sunan neman a shayar da su ruwa amma ba'a shayar da su, har suka mutu. Abu Ƙilabah ya ce: Lallai su sun yi sata, sun yi kisa, sun kafirce bayan sun yi imani, kuma sun yaƙi Allah da ManzonSa.
- Tsarkin fitsarin dukkan abinda ake cin namansa.
- Halaccin magani da nonon rakuma da kuma fitsarinsu.
- Shar'ancin yin tamka (a yi wa mutum yadda ya yi wa wani) a cikin ƙisasi, kuma hani akan musla (daddatsa mutum) abin ɗauka ne ta hanyar da bata sakayya ko ƙisasi ba.
- Kashe jama'a idan sun kashe mutum ɗaya daidai ne sun kashe shi ta hanyar kisan gilla ne ko kuma ta hanyar fashi.
صحيح البخاري (1/ 56) (233). صحيح مسلم (3/ 1296) (1671). إرشاد الساري لشرح صحيح البخاري (1/ 298). عمدة القاري شرح صحيح البخاري (3/ 154). التوضيح لشرح الجامع الصحيح (4/ 455). النهاية في غريب الحديث والأثر (1/ 318).