Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

‌Wanda ya aikata laifin da za'a iya yi masa haddi sai aka gaggauto da uƙubarsa a duniya to Allah Shi ne Mafi karamcin Ya yi wa bawanSa uƙuba (biyu, daya aduniya da kuma) a lahira

عَنْ عَلِيٍّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَنْ أَصَابَ حَدًّا فَعُجِّلَ عُقُوبَتَهُ فِي الدُّنْيَا فَاللَّهُ أَعْدَلُ مِنْ أَنْ يُثَنِّيَ عَلَى عَبْدِهِ العُقُوبَةَ فِي الآخِرَةِ، وَمَنْ أَصَابَ حَدًّا فَسَتَرَهُ اللَّهُ عَلَيْهِ وَعَفَا عَنْهُ فَاللَّهُ أَكْرَمُ مِنْ أَنْ يَعُودَ فِي شَيْءٍ قَدْ عَفَا عَنْهُ».
Daga Aliyu - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «‌Wanda ya aikata laifin da za'a iya yi masa haddi sai aka gaggauto da uƙubarsa a duniya to Allah Shi ne Mafi karamcin Ya yi wa bawanSa uƙuba (biyu, daya aduniya da kuma) a lahira, wanda ya aikata laifin da za’a yi masa haddi sai Allah Ya suturta shi kuma Ya yi masa afuwa to Allah Shi ne Mafi karamcin ya dawo da abinda Ya riga Ya yi afuwarsa».
Tirmizi ne ya Rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya aikata wani saɓon da yake wajabta haddin shari'a, kamar zina da sata, sai ya samu uƙubarsa kuma aka tsayar masa da haddi a duniya, to lallai hakan zai shafe masa wannan saɓon, kuma zai shafe uƙubarsa ta lahira; domin cewa Allah Shi ne Mafi karamci kuma Mafi jin ƙan ya haɗawa bawanSa uƙuba biyu. Wanda kuma Allah Ya suturta shi a duniya, ba a yi masa uƙuba ba akan wannan saɓon, kuma Allah Ya yi masa afuwa Ya gafarta masa, to Allah Shi ne Mafi buwaya kuma Mafi girma Mafi karamcin ya dawo da uƙubar zunubin da Ya riga Ya gafarta shi kuma Ya yi afuwarsa.

Fa’idoji
  1. Girman adalcin Allah da karamcinSa da kuma rahamarSa.
  2. Tsaida haddi a duniya yana kankare zunubi.
  3. Wanda ya afka a zunubin da a cikinsa akwai haddi yana kamata ya suturta kansa tunda Allah Ya suturta shi, kuma ya yi gaggawar tuba na gaskiya.
Madogara

سنن الترمذي (4/ 312) (2626). سنن ابن ماجه (3/ 627) (2604). مرشد ذوي الحجا والحاجة إلى سنن ابن ماجه والقول المكتفى على سنن المصطفى (15/ 224). التيسير بشرح الجامع الصغير (2/ 399). فيض القدير (6/ 65).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
HADDODI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com