Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

FALALAR HAJJI DA UMARA

Hadisai 6

Idan Ramadan ya zo to ki yi umara, domin umara a cikinsa yana daidai da Hajji

عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لِامْرَأَةٍ مِنَ الْأَنْصَارِ سَمَّاهَا ابْنُ عَبَّاسٍ فَنَسِيتُ اسْمَهَا: «مَا مَنَعَكِ أَنْ تَحُجِّي مَعَنَا؟» قَالَتْ: لَمْ يَكُنْ لَنَا إِلَّا نَاضِحَانِ فَحَجَّ أَبُو وَلَدِهَا وَابْنُهَا عَلَى نَاضِحٍ وَتَرَكَ لَنَا نَاضِحًا نَنْضِحُ عَلَيْهِ، قَالَ: «فَإِذَا جَاءَ رَمَضَانُ فَاعْتَمِرِي، فَإِنَّ عُمْرَةً فِيهِ تَعْدِلُ حَجَّةً».
Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce wa wata mata daga mutanen Madina, Ibnu Abbas ya ambaceta sai na manta sunanta: "Meya hanaki ki yi Hajji tare da mu?" Ta ce: Ba mu da komai sai raƙuma biyu, sai baban ɗanta da ɗanta suka yi Hajji akan raƙumi ɗaya, kuma ya bar mana ɗayan muna ban ruwa da shi, ya ce: "Idan Ramadan ya zo to ki yi umara, domin umara a cikinsa yana daidai da Hajji".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya dawo daga Hajjin ban kwana, sai ya cewa wata mata daga mutanen Madina wacce bata yi Hajji ba: Me yahanaki yin Hajji tare da mu? Sai ta kawo hanzarin cewa suna da raƙuma biyu ne, sai mijinta da ɗanta suka yi Hajji akan ɗayan su, kuma ya bar ɗayan dan su yi ban ruwa da shi daga rijiya. Sai Annabi - tsira da aminci su tabbata agare shi - ya bata labarin cewa yin Umura a watan Ramadan ladansa ya yi daidai da ladan Hajji.

Fa’idoji
  1. Falalar Umra a cikin watan Ramadan.
  2. Umra a Ramadan tana daidai da Hajji a lada, ba a sarayar da Hajjin farilla ba.
  3. Ladan ayyuka yana ƙaruwa da ƙaruwar ɗaukakan lokuta, daga hakan akwai ayyuka a cikin Ramadan.
Madogara

صحيح البخاري (3/ 19) (1863). صحيح مسلم (2/ 917) (1256). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 403). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمصطفى الخِن وغيره (2/ 896). المنهاج شرح صحيح مسلم بن الحجاج، للنووي (9/ 2).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Wanda ya yi Hajji bai yi kwarkwasaba, kuma bai yi fasikanciba zai dawo kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi

عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: سمعت النبي صلى الله عليه وسلم يقول: «مَنْ حَجَّ لِلهِ فَلَمْ يَرْفُثْ وَلَمْ يَفْسُقْ رَجَعَ كَيَوْمِ وَلَدَتْهُ أُمُّهُ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Wanda ya yi Hajji bai yi kwarkwasaba, kuma bai yi fasikanciba zai dawo kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa wanda ya ziyarci Dakin Allah - Madaukakin sarki - da Hajji kuma bai yi kwarkwasaba, kwarkwasa ita ce jima'i da abubuwan dake da alaka da shi na sumbata da runguma, kuma ana ambatansa da mummunanan zance, kuma bai yi fasikanciba, ta hanayar aikata sabo da munanan ayyuka ba, Daga fasikanci akwai aikata abubuwan da ka haramta in an yi harama, zai dawo daga hajjinsa wanda aka gafartawa, kamar yadda ake haifar yaro kubutacce daga zunubai.

Fa’idoji
  1. Fasikanci koda ya kasance abin hanawa a kowane lokaci, to hanin yana karfafuwa a aikin hajji dan girmamawa ga ayyukan Hajji.
  2. Mutum ana haifarsa ba tare da kurakurai ba kubutacce daga zunubai; to shi ba ya daukar kuskuren waninsa.
Madogara

صحيح البخاري (2/ 133) (1521). صحيح مسلم (2/ 983) (1350). رياض الصالحين من كلام سيد المرسلين (ص358) (1274). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 401). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (15/ 378). شرح رياض الصالحين، للشيخ محمد بن صالح العثيمين (5/ 321). شرح النووي على مسلم (9/ 119). إكمال المعلم بفوائد مسلم، للقاضي عياض (4/ 462).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ya manzon Allah, muna ganin yaƙi shi ne mafificin aiki, shin ba ma yi yaƙi ba? ya ce: "A'a, sai dai mafificin yaƙi: Shi ne kubutaccen aikin Hajji

عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤْمِنِينَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا أَنَّهَا قَالَتْ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، نَرَى الجِهَادَ أَفْضَلَ العَمَلِ، أَفَلاَ نُجَاهِدُ؟ قَالَ: «لَا، لَكُنَّ أَفْضَلُ الجِهَادِ: حَجٌّ مَبْرُورٌ».
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Ya manzon Allah, muna ganin yaƙi shi ne mafificin aiki, shin ba ma yi yaƙi ba? ya ce: "A'a, sai dai mafificin yaƙi: Shi ne kubutaccen aikin Hajji".
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Sahabbai - Allah Ya yarda da su - sun kasance suna ganin yaƙi a tafarkin Allah da yakar maƙiya yana daga mafifitan ayyuka, sai Nana A'isah - Allah Ya yarda da ita - ta tambayi annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa zasu iya yin yaƙi? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya nuna musu mafificin yaƙi a cikin haƙƙinsu shi ne kubutaccen aikin Hajji wanda ya dace da AlKur'ani da Sunnah, wanda ya kubuta daga zunubi da kuma riya.

Fa’idoji
  1. Yaƙi yana daga mafifitan ayyuka ga maza.
  2. Hajji ga mata ya fi jihadi, kuma shi yana daga mafifitan ayyuka a gare su.
  3. Ayyuka suna fifitar juna gwargwadan mai aikin.
  4. An ambaci Hajji Jihadi; domin cewa shi jihadi ne na rai, kuma a cikinsa akwai bada dukiya, da ƙarfin jiki, shi ibada ce ta jiki da dukiya kamar yaƙi a tafarkin Allah.
Madogara

صحيح البخاري (2/ 133) (1520). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 402). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمصطفى الخِن وغيره (2/ 902). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (5/ 321).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Allah ka jikan masu yin aski, sai suka ce: da masu saisaye ya manzon Allah? sai ya ce: Allah ka jikan masu aski, sai suka ce: da masu saisaye ya manzon Allah? sai ya kuma cewa: Allah ka jikan masu aski, sai suka ce: da masu saisaye ya manzon Allah? sai ya ce da masu saisaye.

عن عبد الله بن عُمر رضي الله عنهما عن رسول الله صلى الله عليه وسلم أنه قال: «اللَّهُمَّ ارحم الْمُحَلِّقِينَ. قالوا: والْمُقَصِّرِينَ يا رسول الله؟ قال: اللهم ارحم الْمُحَلِّقِينَ. قالوا: والْمُقَصِّرِينَ يا رسول الله؟ قال: اللهم ارحم الْمُحَلِّقِينَ. قالوا: والْمُقَصِّرِينَ يا رسول الله؟ قال: والْمُقَصِّرِينَ».
An karbo daga Abdullahi dan Umar Allah ya yarda da su su biyun, daga manzon Allaha mai tsira da aminchi su kara tabbata a gareshi ya ce: {Allah ka jikan masu yin aski sai suka ce: da masu saisaye ya manzon Allah? sai ya ce: Allah ka jikan masu aski, sai suka ce: da masu saisaye ya manzon Allah? sai ya kuma cewa: Allah ka jikan masu aski, sai suka ce: da masu saisaye ya manzon Allah? sai ya ce da masu saisay }
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Aski ko saisaye na daga cikin ibadun aikin Hajji da Umara, amma yin aski yafi saisaye falala saboda shi ne mai kaiwa matuka a cikin bauta, da nuna kaskanchi ga Allah madaukakin sarki, ta hanyar katse gashin kai yana cikin biyayya ga Allah madaukakin sarki, saboda hakanan lallai Annabi mai tsira da aminchin Allah su kara tabbata a gareshi yayi addu`ar naman jin kai ga masu aski har sau uku, wadanda suke tare da shi suna ambato masa masu saisaye sai ya rabu da su, sai a ta uku ko ta hudu ya shigar da masu saisaye tare da su cikin addu`ar, wannan na yin nuni bisa cewa lallai yin aski a cikin hakkin maza shi yafi falala amma wannan yin askin idan bai kasance a umara ta tamattu`i ba saboda lokacin yayi kadan ta yanda za`ace wani gashin ya fito kafin ayi askin Hajji, yin saisaye a cikin hakkin sa shi yafi; domin cewa shi zai yi aski bayan haka

Madogara

تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، عبد الله بن عبد الرحمن البسام، تحقيق: محمد صبحي حلاق، مكتبة الصحابة، الإمارات، مكتبة التابعين، القاهرة، الطبعة: العاشرة 1426هـ، 2006م. تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، محمد بن صالح العثيمين، مكتبة الصحابة، الإمارات، الطبعة: الأولى 1426هـ، 2005م. الإفهام في شرح عمدة الأحكام لابن باز، تحقيق: سعيد القحطاني، مؤسسة عبد العزيز بن باز الخيرية، الرياض، الطبعة: الأولى 1435هـ. خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام، فيصل بن عبد العزيز المبارك، الطبعة: الثانية 1412هـ، 1992م. صحيح البخاري، محمد بن إسماعيل البخاري الجعفي، تحقيق: محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى 1422هـ. صحيح مسلم، مسلم بن الحجاج القشيري النيسابوري، تحقيق محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، الطبعة: 1423هـ. تأسيس الأحكام، أحمد بن يحيى النجمي، دار المنهاج، القاهرة، الطبعة: الأولى 1427هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Babu wata Rana wacce Allah ya fi 'yanta bayi daga Wuta kamar Ranar Arfa

عن عائشة رضي الله عنها مرفوعاً: «ما مِن يومٍ أكثر مِن أنْ يُعْتِقَ اللهُ فيه عبدًا مِن النارِ، مِن يومِ عرفة، وإنَّه ليدنو، ثم يُباهي بهم الملائكةَ، فيقول: ما أراد هؤلاء؟».
Daghi yana kusantowa ne a Nana Aisha -Allah ya yarda da ita- zuwaga Manzon Allah, "Babu wata Rana wacce Allah ya fi 'yanta bayi daga Wuta kamar Ranar Arfa, kuma cewa shi yana kusantowa ne kuma yana Alfahari da su a gaban Mala-ku, yana cewa: Mai waxan nan su ke nufi?
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، نشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت. المنهاج شرح صحيح مسلم بن الحجاج، للنووي، نشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت، الطبعة: الثانية، 1392ه. مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي بن سلطان الملا الهروي القاري، الناشر: دار الفكر، بيروت – لبنان، الطبعة: الأولى، 1422هـ - 2002م. - صفات الله عز وجل الواردة في الكتاب والسنة : علوي بن عبد القادر السَّقَّاف دار الهجرة الطبعة : الثالثة ، 1426 هـ - 2006 م

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ku bibiyi tsakanin Hajji da Umarah, domin cewa su suna kore talauci da kuma zunubai kamar yadda zugazagi yake kore dattin ƙarfe, da zinariya, da azirfa, kuma kuɓutaccen Hajji ba shi da wani sakamako sai aljanna

عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ مَسْعُودٍ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «تَابِعُوا بَيْنَ الحَجِّ وَالعُمْرَةِ، فَإِنَّهُمَا يَنْفِيَانِ الفَقْرَ وَالذُّنُوبَ كَمَا يَنْفِي الكِيرُ خَبَثَ الحَدِيدِ، وَالذَّهَبِ، وَالفِضَّةِ، وَلَيْسَ لِلْحَجَّةِ الْمَبْرُورَةِ ثَوَابٌ إِلاَّ الجَنَّةُ».
An karbo daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku bibiyi tsakanin Hajji da Umarah, domin cewa su suna kore talauci da kuma zunubai kamar yadda zugazagi yake kore dattin ƙarfe, da zinariya, da azirfa, kuma kuɓutaccen Hajji ba shi da wani sakamako sai aljanna".
Tirmizi da Nasa'i da Ahmad ne Suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar akan kusantowa tsakanin yin ibadun Hajji da kuma yin Umarah da rashin yankewa daga yinsu tare da iko, domin cewa yin su yana zama sababi na kawar da talauci da zunubai da kuma tasirinsu a cikin zuciya, kamar yadda zugazugi na wuta yana zamowa sababi a cikin kawar da dattin ƙarfe da abinda yake cakuɗuwa da shi na ma'adanan da su ba daga gare shi suke ba.

Fa’idoji
  1. Falalar bibiya tsakaknin Hajji da Umarah da kuma kwaɗaitarwa akan hakan.
  2. Bibiyar Hajji da Umarah yana daga sabubban wadata da kuma gafarta zunubai.
  3. Al-Mubarakfuri ya ce: (Suna kore talauci) wato Suna gusar da shi, hakan yana ɗaukar talauci na zahiri ta hanyar samun wadatar hannu, da kuma talauci na baɗini ta hanyar samun wadatar zuci.
Madogara

سنن الترمذي (2/ 167) (810)، سنن النسائي (5/ 115) (2631)، مسند أحمد (6/ 185) (3669)، ذخيرة العقبى في شرح المجتبى (23/ 322). النهاية في غريب الحديث والأثر (819) (252).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com