Sahabbai - Allah Ya yarda da su - sun kasance suna ganin yaƙi a tafarkin Allah da yakar maƙiya yana daga mafifitan ayyuka, sai Nana A'isah - Allah Ya yarda da ita - ta tambayi annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa zasu iya yin yaƙi? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya nuna musu mafificin yaƙi a cikin haƙƙinsu shi ne kubutaccen aikin Hajji wanda ya dace da AlKur'ani da Sunnah, wanda ya kubuta daga zunubi da kuma riya.
- Yaƙi yana daga mafifitan ayyuka ga maza.
- Hajji ga mata ya fi jihadi, kuma shi yana daga mafifitan ayyuka a gare su.
- Ayyuka suna fifitar juna gwargwadan mai aikin.
- An ambaci Hajji Jihadi; domin cewa shi jihadi ne na rai, kuma a cikinsa akwai bada dukiya, da ƙarfin jiki, shi ibada ce ta jiki da dukiya kamar yaƙi a tafarkin Allah.
صحيح البخاري (2/ 133) (1520). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 402). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمصطفى الخِن وغيره (2/ 902). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (5/ 321).