Ku bibiyi tsakanin Hajji da Umarah, domin cewa su suna kore talauci da kuma zunubai kamar yadda zugazagi yake kore dattin ƙarfe, da zinariya, da azirfa, kuma kuɓutaccen Hajji ba shi da wani sakamako sai aljanna
An karbo daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku bibiyi tsakanin Hajji da Umarah, domin cewa su suna kore talauci da kuma zunubai kamar yadda zugazagi yake kore dattin ƙarfe, da zinariya, da azirfa, kuma kuɓutaccen Hajji ba shi da wani sakamako sai aljanna".
Tirmizi da Nasa'i da Ahmad ne Suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar akan kusantowa tsakanin yin ibadun Hajji da kuma yin Umarah da rashin yankewa daga yinsu tare da iko, domin cewa yin su yana zama sababi na kawar da talauci da zunubai da kuma tasirinsu a cikin zuciya, kamar yadda zugazugi na wuta yana zamowa sababi a cikin kawar da dattin ƙarfe da abinda yake cakuɗuwa da shi na ma'adanan da su ba daga gare shi suke ba.
Fa’idoji
Falalar bibiya tsakaknin Hajji da Umarah da kuma kwaɗaitarwa akan hakan.
Bibiyar Hajji da Umarah yana daga sabubban wadata da kuma gafarta zunubai.
Al-Mubarakfuri ya ce: (Suna kore talauci) wato Suna gusar da shi, hakan yana ɗaukar talauci na zahiri ta hanyar samun wadatar hannu, da kuma talauci na baɗini ta hanyar samun wadatar zuci.
Madogara
سنن الترمذي (2/ 167) (810)،
سنن النسائي (5/ 115) (2631)،
مسند أحمد (6/ 185) (3669)،
ذخيرة العقبى في شرح المجتبى (23/ 322).
النهاية في غريب الحديث والأثر (819) (252).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com