Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Idan Ramadan ya zo to ki yi umara, domin umara a cikinsa yana daidai da Hajji

عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لِامْرَأَةٍ مِنَ الْأَنْصَارِ سَمَّاهَا ابْنُ عَبَّاسٍ فَنَسِيتُ اسْمَهَا: «مَا مَنَعَكِ أَنْ تَحُجِّي مَعَنَا؟» قَالَتْ: لَمْ يَكُنْ لَنَا إِلَّا نَاضِحَانِ فَحَجَّ أَبُو وَلَدِهَا وَابْنُهَا عَلَى نَاضِحٍ وَتَرَكَ لَنَا نَاضِحًا نَنْضِحُ عَلَيْهِ، قَالَ: «فَإِذَا جَاءَ رَمَضَانُ فَاعْتَمِرِي، فَإِنَّ عُمْرَةً فِيهِ تَعْدِلُ حَجَّةً».
Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce wa wata mata daga mutanen Madina, Ibnu Abbas ya ambaceta sai na manta sunanta: "Meya hanaki ki yi Hajji tare da mu?" Ta ce: Ba mu da komai sai raƙuma biyu, sai baban ɗanta da ɗanta suka yi Hajji akan raƙumi ɗaya, kuma ya bar mana ɗayan muna ban ruwa da shi, ya ce: "Idan Ramadan ya zo to ki yi umara, domin umara a cikinsa yana daidai da Hajji".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya dawo daga Hajjin ban kwana, sai ya cewa wata mata daga mutanen Madina wacce bata yi Hajji ba: Me yahanaki yin Hajji tare da mu? Sai ta kawo hanzarin cewa suna da raƙuma biyu ne, sai mijinta da ɗanta suka yi Hajji akan ɗayan su, kuma ya bar ɗayan dan su yi ban ruwa da shi daga rijiya. Sai Annabi - tsira da aminci su tabbata agare shi - ya bata labarin cewa yin Umura a watan Ramadan ladansa ya yi daidai da ladan Hajji.

Fa’idoji
  1. Falalar Umra a cikin watan Ramadan.
  2. Umra a Ramadan tana daidai da Hajji a lada, ba a sarayar da Hajjin farilla ba.
  3. Ladan ayyuka yana ƙaruwa da ƙaruwar ɗaukakan lokuta, daga hakan akwai ayyuka a cikin Ramadan.
Madogara

صحيح البخاري (3/ 19) (1863). صحيح مسلم (2/ 917) (1256). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 403). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمصطفى الخِن وغيره (2/ 896). المنهاج شرح صحيح مسلم بن الحجاج، للنووي (9/ 2).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALAR HAJJI DA UMARA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com