عن عائشةَ أُمِّ المُؤْمِنينَ رضي الله عنها: أن النبي صلى الله عليه وسلم كان لا يَدع أربعا قَبل الظهر وركعتين قبل الغَدَاة.
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah ya yarda da ita -: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance ba ya barin (raka'o'i) huɗu kafin azahar da raka’a biyu kafin sallar (Asuba).
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana lazimta akan sallolin nafilfili a ɗakinta kuma ba ya barinsu: Raka'o'i huɗu da sallama biyu kafin sallar Azahar, da kuma raka'o'i biyu kafin sallar Asuba.
Fa’idoji
- An so kiyayewa akan raka'o'i huɗu kafin sallar Azahar, da raka'a biyu kafin sallar Asuba.
- Abinda ya fi shi ne ka sallaci (salloli) ratibai a cikin gida, da haka ne Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta bada labari.
Madogara
صحيح البخاري (2/ 59) (1182). توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، لعبد الله البسام (2/ 379).