Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance mafi tsananin lazimtar wani abu na nafiloli ba kamar raka'o'i biyu na Alfijr

عن عائشةَ أمِّ المؤْمنِين رضي الله عنها قالت: لَمْ يَكُنِ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَلَى شَيْءٍ مِنَ النَّوَافِلِ أَشَدَّ مِنْهُ تَعَاهُدًا عَلَى رَكْعَتَيِ الفَجْرِ.
Daga Nana Aisha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce : Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance mafi tsananin lazimtar wani abu na nafiloli ba kamar raka'o'i biyu na Alfijr.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance mafi tsananin lazimta da kuma kiyaye wa ba akan wani abu na nafiloli sama da raka'o'i biyu ratibai na kafin sallar Asuba ba.

Fa’idoji
  1. Nafilolin sallah sune waɗanda ba farillai ba na ayyukan ɗa'a, kuma abin nufi a nan: Sunnoni ratibai masu bin farillai.
  2. Sunnoni ratibai: Raka'o'i biyu kafin Asuba, da raka'o'i huɗu kafin Azahar da biyu bayanta, da raka'o'i biyu bayan Magariba, da raka'o'i biyu bayan Issha'i.
  3. Ana sallatar ratibar Asuba a halin zaman gida da kuma tafiya, saɓanin ratibar Azahar da Magariba da Issha'i, ba a yin su sai a halin zaman gida.
  4. An so, so mai ƙarfi a raka'o'i biyun Asuba, saboda haka ba ya kamata a yi sakaci da su.
Madogara

صحيح البخاري (2/ 57) (1169). صحيح مسلم (1/ 501) (724). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص113). تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (1/ 144).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALAR SALLAR NAFILA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com