Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance mafi tsananin lazimtar wani abu na nafiloli ba kamar raka'o'i biyu na Alfijr
Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance mafi tsananin lazimta da kuma kiyaye wa ba akan wani abu na nafiloli sama da raka'o'i biyu ratibai na kafin sallar Asuba ba.
- Nafilolin sallah sune waɗanda ba farillai ba na ayyukan ɗa'a, kuma abin nufi a nan: Sunnoni ratibai masu bin farillai.
- Sunnoni ratibai: Raka'o'i biyu kafin Asuba, da raka'o'i huɗu kafin Azahar da biyu bayanta, da raka'o'i biyu bayan Magariba, da raka'o'i biyu bayan Issha'i.
- Ana sallatar ratibar Asuba a halin zaman gida da kuma tafiya, saɓanin ratibar Azahar da Magariba da Issha'i, ba a yin su sai a halin zaman gida.
- An so, so mai ƙarfi a raka'o'i biyun Asuba, saboda haka ba ya kamata a yi sakaci da su.
صحيح البخاري (2/ 57) (1169). صحيح مسلم (1/ 501) (724). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص113). تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (1/ 144).