Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

SUNAN RAWATIB

Hadisai 3

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance mafi tsananin lazimtar wani abu na nafiloli ba kamar raka'o'i biyu na Alfijr

عن عائشةَ أمِّ المؤْمنِين رضي الله عنها قالت: لَمْ يَكُنِ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَلَى شَيْءٍ مِنَ النَّوَافِلِ أَشَدَّ مِنْهُ تَعَاهُدًا عَلَى رَكْعَتَيِ الفَجْرِ.
Daga Nana Aisha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce : Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance mafi tsananin lazimtar wani abu na nafiloli ba kamar raka'o'i biyu na Alfijr.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance mafi tsananin lazimta da kuma kiyaye wa ba akan wani abu na nafiloli sama da raka'o'i biyu ratibai na kafin sallar Asuba ba.

Fa’idoji
  1. Nafilolin sallah sune waɗanda ba farillai ba na ayyukan ɗa'a, kuma abin nufi a nan: Sunnoni ratibai masu bin farillai.
  2. Sunnoni ratibai: Raka'o'i biyu kafin Asuba, da raka'o'i huɗu kafin Azahar da biyu bayanta, da raka'o'i biyu bayan Magariba, da raka'o'i biyu bayan Issha'i.
  3. Ana sallatar ratibar Asuba a halin zaman gida da kuma tafiya, saɓanin ratibar Azahar da Magariba da Issha'i, ba a yin su sai a halin zaman gida.
  4. An so, so mai ƙarfi a raka'o'i biyun Asuba, saboda haka ba ya kamata a yi sakaci da su.
Madogara

صحيح البخاري (2/ 57) (1169). صحيح مسلم (1/ 501) (724). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص113). تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (1/ 144).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance ba ya barin (raka'o'i) huɗu kafin azahar da raka’a biyu kafin sallar (Asuba)

عن عائشةَ أُمِّ المُؤْمِنينَ رضي الله عنها: أن النبي صلى الله عليه وسلم كان لا يَدع أربعا قَبل الظهر وركعتين قبل الغَدَاة.
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah ya yarda da ita -: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance ba ya barin (raka'o'i) huɗu kafin azahar da raka’a biyu kafin sallar (Asuba).
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana lazimta akan sallolin nafilfili a ɗakinta kuma ba ya barinsu: Raka'o'i huɗu da sallama biyu kafin sallar Azahar, da kuma raka'o'i biyu kafin sallar Asuba.

Fa’idoji
  1. An so kiyayewa akan raka'o'i huɗu kafin sallar Azahar, da raka'a biyu kafin sallar Asuba.
  2. Abinda ya fi shi ne ka sallaci (salloli) ratibai a cikin gida, da haka ne Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta bada labari.
Madogara

صحيح البخاري (2/ 59) (1182). توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، لعبد الله البسام (2/ 379).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Wanda ya kiyaye akan raka'o'i huɗu kafin azahar da huɗu a bayanta Allah Zai haramta wuta gare shi

عَنْ أُمِّ حَبِيبَةَ رضي الله عنها زَوْجِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالت: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «مَنْ حَافَظَ عَلَى أَرْبَعِ رَكَعَاتٍ قَبْلَ الظُّهْرِ وَأَرْبَعٍ بَعْدَهَا حَرَّمَهُ اللَّهُ عَلَى النَّارِ».
Daga Ummu Habiba - Allah Ya yarda da ita - matar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Wanda ya kiyaye akan raka'o'i huɗu kafin azahar da huɗu a bayanta Allah Zai haramta wuta gare shi ".
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa wanda ya yi sallar nafila raka'a huɗu kafin sallar Azahar, da raka'o'i huɗu a bayanta albishir, kuma ya dawwama ya kiyaye akansu (cewa) Allah Zai haramta wuta gare shi .

Fa’idoji
  1. An so kiyayewa akan raka'o'i huɗu kafin Azahar da (raka'o'i) huɗu a bayanta.
  2. Salloli ratibai kafin sallah - wato kafin farillah -; suna da hikimomi, daga cikinsu: Yi wa zuciyar mai sallah tanadi ga ibada kafin shiga cikin farilla, amma na bayan sallah daga cikin hikimominsu akwai gyara kuskure a farillai.
  3. Akwai fa'idoji da yawa a (salloli) ratibai, na ƙarin kyawawan ayyuka, da kankare munanan ayyuka, da ɗaga darajoji.
  4. Ka'idojin Ahlus Sunnah a cikin hadisan alkawari irin wannan hadisin: Ita ce a ɗauki (hadisan) akan mutuwa akan tauhidi, kuma cewa abin nufi rashin dawwama a cikin wuta; domin mai aikata zunubai cikin masu tauhidi ya cancanci uƙuba sai dai ba zai dawwama a cikin wuta ba in an yi masa uƙuba.
Madogara

سنن أبي داود (2/ 448) (1269). سنن الترمذي (1/ 452) (428). سنن النسائي (3/ 265) (1816). سنن ابن ماجه (2/ 238) (1160). مسند أحمد (44/ 358) (26772). سبل السلام شرح بلوغ المرام، لمحمد الصنعاني (1/ 336). توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، لعبد الله البسام (2/ 381).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com