Daga Ummu Habiba - Allah Ya yarda da ita - matar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Wanda ya kiyaye akan raka'o'i huɗu kafin azahar da huɗu a bayanta Allah Zai haramta wuta gare shi ".
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa wanda ya yi sallar nafila raka'a huɗu kafin sallar Azahar, da raka'o'i huɗu a bayanta albishir, kuma ya dawwama ya kiyaye akansu (cewa) Allah Zai haramta wuta gare shi .
Fa’idoji
An so kiyayewa akan raka'o'i huɗu kafin Azahar da (raka'o'i) huɗu a bayanta.
Salloli ratibai kafin sallah - wato kafin farillah -; suna da hikimomi, daga cikinsu: Yi wa zuciyar mai sallah tanadi ga ibada kafin shiga cikin farilla, amma na bayan sallah daga cikin hikimominsu akwai gyara kuskure a farillai.
Akwai fa'idoji da yawa a (salloli) ratibai, na ƙarin kyawawan ayyuka, da kankare munanan ayyuka, da ɗaga darajoji.
Ka'idojin Ahlus Sunnah a cikin hadisan alkawari irin wannan hadisin: Ita ce a ɗauki (hadisan) akan mutuwa akan tauhidi, kuma cewa abin nufi rashin dawwama a cikin wuta; domin mai aikata zunubai cikin masu tauhidi ya cancanci uƙuba sai dai ba zai dawwama a cikin wuta ba in an yi masa uƙuba.
Madogara
سنن أبي داود (2/ 448) (1269).
سنن الترمذي (1/ 452) (428).
سنن النسائي (3/ 265) (1816).
سنن ابن ماجه (2/ 238) (1160).
مسند أحمد (44/ 358) (26772).
سبل السلام شرح بلوغ المرام، لمحمد الصنعاني (1/ 336).
توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، لعبد الله البسام (2/ 381).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com
Wanda ya kiyaye akan raka'o'i huɗu kafin azahar da huɗu a bayanta Allah Zai haramta wuta gare shi · Hadisai tare da sharhi · Sabīl