عن أبِي هُرَيرةَ رضي الله عنه أنَّ رسول الله صلى الله عليه وسلمَ قال: «إذا قُلْتَ لِصَاحِبِكَ: أَنْصِتْ، يومَ الجمعةِ، والْإِمامُ يَخْطُبُ، فَقَدْ لَغَوْتَ».
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Idan ka ce wa abokinka: Yi shiru, a ranar Juma'a, a lokacin liman yana huɗuba, to, haƙiƙa ka yi zance mara anfani".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa daga ladubba na wajibi ga wanda ya halarci huɗubar Juma'a: Shi ne yin ahieu ga mai huɗuba; don ya yi tuntuntuni cikin wa'azin, kuma wanda ya yi magana - ko da da ƙanƙanin abu ne - alhali liman yana huɗuba, sai ya ce wa waninsa: "Ka yi shiru" ka "saurara", to, haƙiƙa falalar sallar Juma'a ta wuce shi.
Fa’idoji
- Haramta zance alokacin jin huɗuba, ko da da hani ne daga abin ƙi, ko amsa sallama da gaishe da mai atishawa.
- An togance wanda yake yi wa liman magana, ko liman yake yi masa magana [daga wannan hanin].
- Halaccin yin magana a lokacin huɗubobi biyu a yayin buƙata.
- Idan an ambaci Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - alhali liman yana huɗuba, to, za ka yi masa salati, a ɓoye, haka nan cewa amin ga addu'a.
Madogara
صحيح البخاري (2/ 13) (934).
صحيح مسلم (2/ 583) (851).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص244).
تنبيه الأفهام، للعثيمين (2/ 307).
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 195).
فتح الباري، لابن حجر (2/ 409).
تاج العروس من جواهر القاموس، لمحمّد الحسيني الزَّبيدي (39/ 463).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَنِ اغْتَسَلَ يَوْمَ الجُمُعَةِ غُسْلَ الجَنَابَةِ ثُمَّ رَاحَ، فَكَأَنَّمَا قَرَّبَ بَدَنَةً، وَمَنْ رَاحَ فِي السَّاعَةِ الثَّانِيَةِ، فَكَأَنَّمَا قَرَّبَ بَقَرَةً، وَمَنْ رَاحَ فِي السَّاعَةِ الثَّالِثَةِ، فَكَأَنَّمَا قَرَّبَ كَبْشًا أَقْرَنَ، وَمَنْ رَاحَ فِي السَّاعَةِ الرَّابِعَةِ، فَكَأَنَّمَا قَرَّبَ دَجَاجَةً، وَمَنْ رَاحَ فِي السَّاعَةِ الخَامِسَةِ، فَكَأَنَّمَا قَرَّبَ بَيْضَةً، فَإِذَا خَرَجَ الإِمَامُ حَضَرَتِ المَلاَئِكَةُ يَسْتَمِعُونَ الذِّكْرَ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya yi wanka irin wankan janaba a ranar Juma`a, sannan ya tafi, kamar ya bayar da sadakar rakuma ne, wanda ya tafi a lokaci na biyu, kamar ya bayar da sadakar saniya ne. wanda ya tafi a lokaci na uku kamar ya bayar da sadakar rago ne mai ƙaho. wanda ya tafi a lokaci na huɗu kamar ya bayar da kaza ne, wanda kuma ya tafi a lokaci na biyar kamar ya bayar da ƙwai ne. Idan liman ya fito Mala`iku za su halarto suna sauraron zikiri (Huɗuba)".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari game da falalar gaggawar tafiya zuwa sallar Juma'a. Gaggawa tana farawa ne daga bullowar rana zuwa lokacin zuwan liman; shi ne sa'o'i biyar, ana karkasasu kaso biyar gwargwadan lokaci tsakanin bullowar rana har zuwa shigowar liman da hawansa minbari dan huɗuba:
Na farko: Wanda ya yi wanka cikakke kamar wankan janaba, sannan ya tafi masallacin Juma'a a lokaci na farko kamar ya yi sadaka da taguwa ne.
Na biyu: Wanda ya tafi a lokaci na biyu kamar ya yi sadaka da saniya ne.
Na uku; Wanda ya tafi a lokaci na uku kamar ya yi sadaka ne da rago - shi ne namijin tinkiya - mai ƙahuhhuna.
Na huɗu: Wanda ya tafi a lokaci na huɗu kamar ya yi sadaka ne da kaza.
Na biyar: Wanda ya tafi a lokaci na biyar kamar ya yi sadaka ne da ƙwai.
Idan liman ya fito dan huɗuba; sai mala'ikun da suke zaune a ƙofofi dan rubuta masu shiga masallaci na farko da mai biye da shi sai su dakatar da rubutu, sai su zo suna jin zikiri da huɗuba.
Fa’idoji
- Kwaɗaitarwa akan yin wanka ranar Juma'a, kuma yana kasancewa ne kafin tafiya zuwa sallah.
- Falalar gaggawa zuwa sallar Juma'a daga farkon sa'o'in yini.
- Kwaɗaitarwa akan gaggawa ga ayyuka na gari.
- Halartowar mala'iku sallar Juma'a da sauraransu ga huɗuba.
- Mala'iku suna ƙofofin masallatai, suna rubuta masu shigowa, na farko sai mai beye da shi, a zuwa sallar Juma'a.
- Ibnu Rajab ya ce: Faɗinsa: "Wanda ya yi wanka ranar Juma'a, sannan ya tafi" yana nuni akan cewa wankan da ake so dan Juma'a farkonsa shi ne bullowar alfijir, ƙarshensa kuma tafiya zuwa Juma'a.
Madogara
صحيح البخاري (2/ 3) (881).
صحيح مسلم (2/ 582) (850).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، عبد الله البسام (ص244).
تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (2/ 308).
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، إسماعيل الأنصاري (1/ 196).
معالم السنن (شرح سنن أبي داود)، أبو سليمان الخطابي (1/ 109).
تهذيب اللغة، محمد الأزهري (14/ 102).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن عَبْدِ اللهِ بْنِ عُمَرَ رضي الله عنهما قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم يَقُولُ: «مَنْ جَاءَ مِنْكُمُ الْجُمُعَةَ فَلْيَغْتَسِلْ».
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa: "Wanda zai je Juma'a a cikinku to ya yi wanka".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana ƙarfafa cewa wanda ya yi nufin zuwa sallar Juma'a to an so gareshi ya yi wanka, kamar irin wankansa na janaba.
Fa’idoji
- Ƙarfafa wankan Juma'a, kuma cewa shi sunna ne ga mumini ranar Juma'a kuma ya kasance a lokacin tafiya zuwa sallah ya fi.
- Kwaɗaitarwa akan tsafta da kyakkyawan ƙanshi yana daga ɗabi'un musulmi da ladubbansa, kuma umarnin yana ƙarfafa a lokacin haɗuwa da mutane da zama da su, musammama dai a Juma'o'i da jam'i.
- Magana a cikin hadisin ga wanda Juma'a ta wajaba akansa ne; domin cewa shi ne zai zo Juma’ar.
- An so ga wanda zai ke Juma'a ya zama mai tsafta, sai ya yi wanka don wari daga jikinsa ya gushe kuma ya shafa turare, idan ya yi alwala kawai to hakan ya isar masa.
Madogara
صحيح البخاري (2/ 81) (1294).
صحيح مسلم (1/ 99) (103).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص239).
تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (2/ 302).
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 192).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن سَلَمَةَ بْنِ الأَكْوَعِ رضي الله عنه وكان من أصحاب الشجرة قال: «كنا نُصَلِّي مع رسول الله صلى الله عليه وسلم الْجُمُعَةَ، ثم نَنْصَرِفُ، وليس للحيطان ظِلٌّ نستظِلّ به».
وفي لفظ: «كنا نُجَمِّعُ مع رسول الله صلى الله عليه وسلم إذا زالت الشمس، ثم نرجع فَنَتَتَبَّعُ الْفَيْءَ».
A kan Salama Bin Al-Akwaa - yardar Allah ta tabbata a gare shi - kuma yana daya daga cikin masu wannan itaciyar da suka ce: "Mun kasance muna yin Sallah tare da Manzon Allah - Salatin Allah da amincin Allah su tabbata a gare shi - sallar Juma'a, sannan muka tashi, kuma bangayen ba su da inuwar da za a sha." Kuma a cikin jumlar: "Mun kasance muna haduwa tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - idan rana ta faɗi, to sai mu koma mu bi maslahar."
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Salamah bin Al-Akwa - Allah ya yarda da shi - ya ambaci cewa sun kasance suna yin shaida tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sallar Juma’a, don haka suka kasance suna yin addu’o’i da wuri, don haka sai suka gama huduba da salloli biyu, sannan suka tafi gidajensu, kuma bangayen ba su da inuwar da za su nemi mafaka da ita. Ruwaya ta biyu: Sun kasance suna yin sallar juma'a tare da annabi –SAW- idan rana ta fadi, to za su dawo. Malamai sun yi ijma’i a kan cewa lokacin karshe na sallar Juma’a shi ne na karshe a sallar azahar, kuma shi ne lokaci na farko kuma mafi kyau da za a yi addu’a bayan sallar azahar. Domin shine abinda yafi kowa tabbata ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Kuma saboda lokaci ne da aka yi ittifaqi a kan malamai in dai ba larura. Idan mutum yana da zafi sosai, kuma ba su da abin da za su nemi mafaka da shi, ko kuma suna son fita don yin jihadi kafin merida, babu laifi idan ta yi addu’a jim kaɗan kafin merida.
Madogara
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، عبد الله بن عبد الرحمن البسام، تحقيق: محمد صبحي حلاق، مكتبة الصحابة، الإمارات، مكتبة التابعين، القاهرة، الطبعة: العاشرة 1426هـ، 2006م.
تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، محمد بن صالح العثيمين، مكتبة الصحابة، الإمارات، الطبعة: الأولى 1426هـ، 2005م.
عمدة الأحكام من كلام خير الأنام -صلى الله عليه وسلم- لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، دار الثقافة العربية، دمشق، بيروت، مؤسسة قرطبة، الطبعة: الثانية 1408هـ، 1988م.
صحيح البخاري، محمد بن إسماعيل البخاري الجعفي، تحقيق: محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى 1422هـ.
صحيح مسلم، مسلم بن الحجاج القشيري النيسابوري، تحقيق محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، الطبعة: 1423هـ.
فتح الباري شرح صحيح البخاري، زين الدين عبد الرحمن بن رجب البغدادي، تحقيق: محمود بن شعبان بن عبد المقصود ومجدي بن عبد الخالق الشافعي وغيرهم، الناشر: مكتبة الغرباء الأثرية، المدينة النبوية، الحقوق: مكتب تحقيق دار الحرمين، القاهرة الطبعة: الأولى 1417هـ، 1996م.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن عبد الله بن عُمر بن الخطاب رضي الله عنهما قال: «كان النبي صلى الله عليه وسلم يخطب خطبتين يقعد بينهما» وفي رواية لجابر - رضي الله عنه-: «كان رسول الله صلى الله عليه وسلم يَخْطُبُ خُطْبَتَيْنِ وهو قائم، يفصل بينهما بجلوس».
An karbo daga Abdullahi dan umar dan khaddabi- Allah ya kara yarda a gare su su biyun- ya ce: { Annabi tsira da aminci su kara tabbata a gareshi ya kasance yana yin hudubobi guda biyu yana zama a tsakanin su } a wata ruwayar ta jabir- Allah ya kara masa yarda-: { manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi- ya kasance yana yin hudubobi guda biyu alhali yana tsaye, yana raba tsakanin su da zama }.
Al-Baihaki ne Ya Rawaito shi - Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne duka Riwayoyin nasa guda biyun
Sharhi
Ranar juma`a matattara ce babba gamammiya ga mutanen gari baki dayan su saboda haka ne annabi tsira da aminci sukara tabbata a gareshi ya kasance daga cikin hikimar sa yana yiwa mutane huduba ranar juma`a hudubobi guda biyu, yana fuskantar da su izuwa dukkan alherai a cikin hudubobin guda biyu, yana tsawatar da su ga barin sharri ya kasance yana zuwa da hudubobi guda biyu alhali yana tsaye akan munbari, don ya kasance ya kai isa matuka cikin koyar da su da yimusu wa`azi, da abinda ke ciki na tsayuwa wajen bayyanar da karfin musulunci da bashi cikakkiyar kulawa. idan ya gama da hudubar farko, sai ya zauna zama sassauka don ya dan huta, sai ya raba tsakanin ta farko da ta biyu, sa`annan ya mike yayi huduba ta biyu saboda kada mai huduba ya gaji mai sauraro kuma ya kosa.
Madogara
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، عبد الله بن عبد الرحمن البسام، تحقيق: محمد صبحي حلاق، مكتبة الصحابة، الإمارات، مكتبة التابعين، القاهرة، الطبعة: العاشرة 1426هـ، 2006م.
تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، محمد بن صالح العثيمين، مكتبة الصحابة، الإمارات، الطبعة: الأولى 1426هـ، 2005م.
الإفهام في شرح عمدة الأحكام لابن باز، تحقيق: سعيد القحطاني، مؤسسة عبد العزيز بن باز الخيرية، الرياض، الطبعة: الأولى 1435هـ.
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، إسماعيل بن محمد الأنصاري، دار الفكر، دمشق، الطبعة: الأولى 1381هـ.
خلاصة الكلام –فيصل المبارك الحريملي -الطبعة: الثانية، 1412 هـ - 1992 م.
تأسيس الأحكام، أحمد بن يحيى النجمي، دار المنهاج، القاهرة، الطبعة: الأولى 1427هـ.
صحيح البخاري، محمد بن إسماعيل البخاري الجعفي، تحقيق: محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى 1422هـ.
صحيح مسلم، مسلم بن الحجاج القشيري النيسابوري، تحقيق محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، الطبعة: 1423هـ.
المجتبى من السنن ( السنن الصغرى )، أحمد بن شعيب النسائي، تحقيق: عبد الفتاح أبو غدة، مكتب المطبوعات الإسلامية، حلب، الطبعة: الثانية 1406هـ، 1986م.
سنن الدارمي، تحقيق: حسين سليم أسد الداراني، دار المغني للنشر والتوزيع، المملكة العربية السعودية، الطبعة: الأولى 1412هـ، 2000م.
تهذيب اللغة، محمد بن أحمد الأزهري أبو منصور، تحقيق: محمد عوض مرعب، الناشر: دار إحياء التراث العربي، بيروت، الطبعة: الأولى، 2001م.
إرواء الغليل في تخريج أحاديث منار السبيل - محمد ناصر الدين الألباني إشراف: زهير الشاويش-المكتب الإسلامي – بيروت-الطبعة: الثانية 1405 هـ - 1985م.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي عبد الله جابر بن سمرة رضي الله عنهما قال: كنت أصلي مع النبي صلى الله عليه وسلم الصلوات، فكانت صلاته قَصْدًا وخطبته قَصْدًا.
An rawaito daga Abdullahi Jabir Bn Samarah -Allah ya yarda da su- ya ce:"Na kasance ina Sallah tare da Annabi -Amincin Allah a gare shi- Salloli Sallarsa ta kasance tsakatsaki ce haka Hudubarsa tsakatsaki ce"
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara
المسند الصحيح (صحيح مسلم), تأليف: مسلم بن حجاج النيسابوري, تحقيق: محمد فؤاد عبدالباقي, دار إحياء التراث العربي.
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين, تأليف: سليم بن عيد الهلالي, دار ابن الجوزي.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن معاذ بن أنس الجهني رضي الله عنه : أن النبي صلى الله عليه وسلم نَهى عن الحِبْوَةِ يوم الجمعة والإمام يخطب.
An rawaito daga Ali Bn Abu Dalib -Allah ya yarda da shi- "Cewa Annabi ya hana Auren Mutu'a a Ranar yakin Khaibara, da kuma cin Naman Jakin gida"
Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shiDarajaHasan ne
Madogara
نزهة المتقين، تأليف: جمعٌ من المشايخ، الناشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة الأولى: 1397 هـ الطبعة الرابعة عشر 1407 هـ
كنوز رياض الصالحين، تأليف: حمد بن ناصر بن العمار ، الناشر: دار كنوز أشبيليا، الطبعة الأولى: 1430 هـ
سنن أبي داود، تأليف: سليمان بن الأشعث السِّجِسْتاني، تحقيق: محمد محيي الدين عبد الحميد، الناشر: المكتبة العصرية، صيدا.
مسند الإمام أحمد، تأليف: أحمد بن محمد بن حنبل، تحقيق: شعيب الأرناؤوط وغيره، الناشر: الناشر: مؤسسة الرسالة ، الطبعة: الأولى، 1421 هـ
رياض الصالحين، تأليف : محيي الدين يحيى بن شرف النووي ، تحقيق: د. ماهر بن ياسين الفحل ، الطبعة: الأولى، 1428 هـ
شرح رياض الصالحين، تأليف: محمد بن صالح العثيمين، الناشر: دار الوطن للنشر، الطبعة: 1426 هـ
سنن الترمذي، تأليف: محمد بن عيسى الترمذي، تحقيق أحمد شاكر وغيره ، الناشر: شركة مكتبة ومطبعة مصطفى البابي الحلبي، الطبعة: الثانية، 1395 هـ
المنهاج شرح صحيح مسلم، تأليف: محيي الدين يحيى بن شرف النووي، الناشر: دار إحياء التراث العربي، الطبعة: الثانية 1392 هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن سمرة رضي الله عنه مرفوعاً: «من توضَّأَ يوم الجُمعة فَبِهَا ونِعْمَتْ، ومن اغْتَسَل فهو أفْضَل».
Daga Samra - Allah ya yarda da shi - tare da marfuu: "Wanda ya yi alwala a ranar Juma'a kuma ya sanya albarka a cikinta, kuma wanda ya yi alwala shi ne mafi alheri."
Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi - Al-Darumi Ya Rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi
"Duk wanda yayi alwala a ranar juma'a" to yana nufin alwala ne don sallar juma'a. Don haka da shi, ma'ana ya dauki Sunna da lasisi, da ni'ima, wato, abin da ya aikata ta hanyar daukar ta a cikin Sunna, don haka wannan abin yabo ne a gare shi. "Kuma wanda ya yi alwala, to wannan ya fi kyau" yana nufin: duk wanda ya yi alwala don sallar juma'a tare da alwala, to, ya fi alwala wacce ba ta alwala ba. Da wannan ne mafiya yawan malamai, gami da limamai huxu, da waxanda su ma sheda ce a kansu sun xauki hadisin Muslim: (Duk wanda ya yi alwala kuma ya yi alwala mai kyau, to ya zo juma'a ya saurara, za a gafarta masa tsakanin Juma'a da Juma'a da qarin kwana uku)
Madogara
سنن أبي داود، سليمان بن الأشعث السِّجِسْتاني، تحقيق: محمد محيي الدين عبد الحميد: المكتبة العصرية، صيدا - بيروت.
سنن الترمذي، لمحمد بن عيسى الترمذي، تحقيق وتعليق:أحمد محمد شاكر ومحمد فؤاد عبد الباقي وإبراهيم عطوة عوض، شركة مكتبة ومطبعة مصطفى البابي الحلبي، مصر، الطبعة الثانية، 1395 هـ - 1975م.
سنن ابن ماجه: لابن ماجه أبو عبد الله محمد بن يزيد القزويني، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء الكتب العربية - فيصل عيسى البابي الحلبي.
مسند الإمام أحمد بن حنبل، المحقق: شعيب الأرنؤوط - عادل مرشد، وآخرون إشراف: د عبد الله بن عبد المحسن التركي، مؤسسة الرسالة، الطبعة: الأولى، 1421 هـ - 2001 م.
السنن الكبرى للنسائي، حققه وخرج أحاديثه: حسن عبد المنعم شلبي، أشرف عليه: شعيب الأرناءوط، مؤسسة الرسالة، بيروت، الطبعة: الأولى، 1421 هـ - 2001 م.
سنن الدارمي، لعبد الله بن عبد الرحمن الدارمي، التميمي تحقيق: حسين سليم أسد الداراني، دار المغني للنشر والتوزيع، المملكة العربية السعودية، الطبعة: الأولى، 1412 هـ - 2000 م.
توضيح الأحكام شرح بلوغ المرام، تأليف عبد الله البسام، مكتبة الأسدي، مكة المكرمة، الطبعة:الخامِسَة، 1423 هـ - 2003 م.
تسهيل الإلمام بفقه الأحاديث من بلوغ المرام، تأليف: الشيخ صالح الفوزان، عناية عبد السلام السليمان، مؤسسة الرسالة الطبعة الأولى.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com