Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

HUKUNCE-HUKUNCEN HUƊUBAR JUMA'A

Hadisai 2

wani mutum ya zo a lokacin Annabi- mai tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi- yana yiwa mutane huduba a ranar juma`a. sai ya ce: kayi salla ne ya kai wane? sai ya ce: a`a, sai annabi ya ce: tashi kayi raka`a biyu

عن جابِر بن عبد الله رضي الله عنهما قال: «جاء رجل والنبي صلى الله عليه وسلم يَخْطُبُ الناس يوم الجمعة، فقال: صليت يا فلان؟ قال: لا، قال: قم فاركع ركعتين، -وفي رواية: فصل ركعتين-».
Daga jabir dan Abdullahi- Allah ya kara yarda a garesu su biyun- ya ce: { Wani mutum ya zo a lokacin annabi- mai tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi- yana yiwa mutane huduba a ranar juma`a. sai ya ce: kayi salla ne ya kai wane? sai ya ce: a`a, sai annabi ya ce: tashi kayi raka`a biyu- a wata ruwayar kuma: yi sallah raka`a biyu- }
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Sulaiku algadafaniy ya shiga masallacin Annabi a lokacin annabi maitsira da amincin Allah yana yiwa mtane huduba, sai ya zauna don ya ji huduba, alhalin bai yi sallar gaisuwar masallaci ba, kodai saboda ya jahilci hukuncin ta ko kuma yana zaton sauraraon hudubar yafi muhimmanci, amma hakan bai hana annabi mai tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi ya tunatar da shi ba shagaltuwar sa da huduba bai hana shi ya tsaya ya sanar da shi ba, har magana ma yayi masa da cewa: shin kayi sallah ya kai wane a gefen masallaci kafin na ganka? sai ya ce: a`a sai ya ce : tashi kayi raka`a biyu a cikin riwayar muslim ya umarce shi da ya takaita raka`o`in ma`ana ya saukaka su, ya fadi hakan ne a cikin babban taro domin ya koyar da mutumin cikin lokacin bukata, kuma domin koyarwar ta zamo gamammiya abar yadawa tsakanin mahalarta masallacin. Duk wanda ya shiga masallaci alhalin mai huduba yana huduba to abin shar`antawa a gareshi shi ne yin salla. dalilin da yake nuni akan haka shi ne wannan hadisin, da kuma hadisin: ''Idan dayan ku yazo a ranar juma`a alhalin limami yana huduba, to lallai yayi raka`a guda biyu''. saboda haka imamun-nawawiy ya fada a cikin sharhin muslim a wurin fadar sa mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi: ''Idan dayanku yazo alhalin limami yana huduba to lallai yayi raka`o`i biyu ya kuma takaita a cikin su'' sai ya ce: wannan nassi ne da baya neman karin bayani, ba kuma na zaton wannan lafazin zai isa zuwa ga wani masani da ya tabbatar da ingancinsa sa`annan kuma ya saba masa.

Madogara

تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، عبد الله بن عبد الرحمن البسام، تحقيق: محمد صبحي حلاق، مكتبة الصحابة، الإمارات، مكتبة التابعين، القاهرة، الطبعة العاشرة، 1426هـ - 2006م. الإفهام في شرح عمدة الأحكام، لابن باز، تحقيق: سعيد القحطاني، مؤسسة عبد العزيز بن باز الخيرية، الرياض، الطبعة الأولى، 1435هـ. الإلمام بشرح عمدة الأحكام، إسماعيل بن محمد الأنصاري، دار الفكر، دمشق، الطبعة الأولى، 1381هـ. خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام، فيصل بن عبد العزيز المبارك، الطبعة الثانية، 1412هـ - 1992م. صحيح البخاري، محمد بن إسماعيل البخاري الجعفي، تحقيق: محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة الأولى، 1422هـ. صحيح مسلم، مسلم بن الحجاج القشيري النيسابوري، تحقيق محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، الطبعة، 1423هـ. تأسيس الأحكام، أحمد بن يحيى النجمي، دار المنهاج، القاهرة، الطبعة الأولى، 1427هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

{Shin yanzu kwa mayar da shayar da mai aikin Hajj da kuma raya Masallaci mai alfarma kamar wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira}[al-Taubah: 19] karanta ayar har zuwa ƙarshenta

عَنِ النُّعْمَانِ بْنِ بَشِيرٍ رَضيَ اللهُ عنهُما قَالَ: كُنْتُ عِنْدَ مِنْبَرِ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ رَجُلٌ: مَا أُبَالِي أَلَّا أَعْمَلَ عَمَلًا بَعْدَ الإِسْلَامِ إِلَّا أَنْ أُسْقِيَ الحَاجَّ، وَقَالَ آخَرُ: مَا أُبَالِي أَلَّا أَعْمَلَ عَمَلًا بَعْدَ الإِسْلَامِ إِلَّا أَنْ أَعْمُرَ المَسْجِدَ الحَرَامَ، وَقَالَ آخَرُ: الجِهَادُ فِي سَبِيلِ اللهِ أَفْضَلُ مِمَّا قُلْتُمْ، فَزَجَرَهُمْ عُمَرُ، وَقَالَ: لَا تَرْفَعُوا أَصْوَاتَكُمْ عِنْدَ مِنْبَرِ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَهُوَ يَوْمُ الجُمُعَةِ، وَلَكِنْ إِذَا صَلَّيْتُ الجُمُعَةَ دَخَلْتُ فَاسْتَفْتَيْتُهُ فِيمَا اخْتَلَفْتُمْ فِيهِ، فَأَنْزَلَ اللهُ عَزَّ وَجَلَّ: {أَجَعَلْتُمْ سِقَايَةَ الْحَاجِّ وَعِمَارَةَ الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ كَمَنْ آمَنَ بِاللهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ} [التوبة: 19] الآيَةَ إِلَى آخِرِهَا.
Daga Nu'umanu Ibnu Bashir - Allah Ya yarda da su - ya ce: Na kasanace a wurin minbarin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai wani mutum ya ce: Bayan na musulunta babu ruwana da in yi wani aiki sai dai kawai in shayar da mai yin aikin Hajji. Wani kuma ya ce: Bayan na musulunta babu ruwana da in yi wani aiki sai dai in raya Masallaci mai alfarma. Wani kuma ya ce: Jihadi a tafarkin Allah ya fi abin da kuka faɗa, sai Umar ya yi musu tsawa, kuma ya ce: Kada ku ɗaga muryarku a wajen mimbarin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali ranar Juma'a ce, sai dai idan na sallaci Juma'a zan shiga in tambaye shi a cikin abin da kuka saɓa a cikinsa, sai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya saukar da: {Shin yanzu kwa mayar da shayar da mai aikin Hajj da kuma raya Masallaci mai alfarma kamar wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira}[al-Taubah: 19] karanta ayar har zuwa ƙarshenta.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Nu'umanu Ibnu Bashir - Allah Ya yarda da su - ya ambaci cewa shi yana zaune a wajen mimbarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ji wani mutum yana cewa: Bayan na musulunta ba zan damu dana aikata wani aiki ba sai dai in shayar da mai aikin Hajji. Wani kuma ya ce: Bayan na musulunta ba zan damu dana aikata wani aiki ba sai dai in raya Masallaci mai alfarma. Wani kuma ya ce: Jihadi a tafarkin Allah ya fi abin da kuka faɗa. Sai Umar Ibnul Khaɗɗabi - Allah Ya yarda da shi- ya yi musu tsawa saboda ɗaga muryarsu da suka yi a wajen mimbarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma safiyar ranar Juma'a ce, sai dai idan na yi sallar Juma'a zan shiga in tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a kan abin da kuka saɓa a cikinsa, sai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya saukar da: {Shin, kun mayar da shãyar da mahajjata da rãyar da Masallaci Mai alfarma kamar wanda ya yi ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira, kuma ya yi jihãɗi a cikin hanyar Allah? Bã su daidaita a wurin Allah. Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai} [al-Tauba: 19].

Fa’idoji
  1. Fifikon ayyuka a lada da sakamako.
  2. Fifikon ayyuka gwargwadan abin da shari'a ta zo da shi, bawai gwargwadan ƙoƙarin mutane ba.
  3. Falalar Jihadi a tafarkin Allah da sharaɗin yin imani da Allah ne da kuma ranar lahira.
  4. Nawawi ya ce: A cikinsa akwai karahiyar ɗaga murya a cikin masallatai a ranar Juma'a da waninta, kuma mutum kada ya ɗaga murya da ilimi ne ko da waninsa a lokacin taruwar mutane dan yin sallah saboda abin da ke cikinsa na takura musu da kuma masu yin sallar da kuma masu yin zikiri.
Madogara

صحيح مسلم (3/ 1499) (1879). المفهم لما أشكل من تلخيص كتاب مسلم (3/ 720). البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (32/ 395). النهاية في غريب الحديث والأثر (ص 897).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com