Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Virtue of Friday

Hadisai 2

Lallai wasu mutane kodai su hanu daga barin Juma'o'i, ko Allah Zai yi yumƙi akan zukatansu, sannan zasu kasance daga marafkana

عن عبد الله بن عُمر وأبي هريرة رضي الله عنهما أنهما سمعا رسول الله صلى الله عليه وسلم، يقول على أعواد منبره: «لَيَنْتَهِيَنَّ أَقْوَامٌ عَنْ وَدْعِهِمُ الْجُمُعَاتِ أَوْ لَيَخْتِمَنَّ اللهُ عَلَى قُلُوبِهِمْ، ثُمَّ لَيَكُونُنَّ مِنَ الْغَافِلِينَ».
Daga Abdullahi ɗan Umar da kuma Abu Huraira - Allah Ya yarda da su - cewa su sun ji manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbat agare shi - yana faɗa akan minbarinsa: "Lallai wasu mutane kodai su hanu daga barin Juma'o'i, ko Allah Zai yi yumƙi akan zukatansu, sannan zasu kasance daga marafkana"
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kan mimbari ya yi gargaɗi daga barin sallar Juma'a da zama na kin zuwa ba tare da wani uzuri ba, dan wulaƙantarwa da kuma kasala, ko Allah Ya yi yumƙi akan zukatansu Ya rufesu kuma Ya sanya kariyar da zai hanasu bin gaskiya, sannan zasu kasance daga rafkanannu daga sabubban alheri, mai korewa rayukansu ayyukan ɗa'a.

Fa’idoji
  1. Tsanantawa akan masu ƙin zuwa sallar Juma'a, kuma cewa hakan yana daga cikin manyan zunubai.
  2. AlNawawi ya ce: A cikinsa cewa sallar Juma'a farilla ce ta aini (wacce ta wajaba akan kowa da kowa).
  3. Halaccin riƙar minbari dan yin huɗuba.
  4. Sindi ya ce: Ma'ana cewa ɗaya daga cikin al'amura biyu mai kasancewa ne babu makawa, kodai dena barin zuwa Juma'o'i ko Allah Ya yi yumƙi (wato ya toshe) zukatansu, domin cewa sabawa da barin Jumu'o'i yana tabbatar da rufi akan zuciya kuma yana korewa rayuka ayyukan ɗa'a.
  5. Yana kamata ga mai wa'azi da mai tinatarwa ya ɓoye (sunayen) mutanen da yake so ya yi musu wa'azi; domin cewa hakan ya fi saurin sa a karɓi nasiha, da kuma kamanta umarni.
Madogara

صحيح مسلم (2/ 591) (865). النهاية في غريب الحديث والأثر (964). البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (17/ 250).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Wanda ya bar Juma'o'i uku dan wulaƙantar da su Allah zai yi yumƙi akan zuciyarsa

عَنْ أَبِي الْجَعْدِ الضَّمْرِيِّ رَضيَ اللهُ عنهُ، وَكَانَتْ لَهُ صُحْبَةٌ، أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَنْ تَرَكَ ثَلَاثَ جُمَعٍ تَهَاوُنًا بِهَا طَبَعَ اللَّهُ عَلَى قَلْبِهِ».
Daga Abul Ja'ad al-Damri - Allah Ya yarda da shi -, kuma ya kasance sahabi ne, cewa manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya bar Juma'o'i uku dan wulaƙantar da su Allah zai yi yumƙi akan zuciyarsa".
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi daga barin sallar Juma'a, kuma wanda ya bar sallar Juma'a sau uku dan sakaci da kasawa ba tare da wani uzuri ba Allah zai rufe zuciyarsa ta hanyar hana isar alheri gare shi .

Fa’idoji
  1. Ibnul Munzir ya hakaito Ijma'i akan cewa sallar Juma'a farilla ce ta aini (wato ta hau kan kowa).
  2. Narko akan wanda ya bar Juma'a dan sakaci shi ne Allah zai yi yumƙi akan zuciyarsa.
  3. Wanda ya bar Juma'a dan wani uzuri to shi ba ya shiga cikin narkon.
  4. Al-Shaukani ya ce: Faɗinsa: (Juma'o'i uku), yana ɗaukar cewa ana nufin faruwar barin kai tsaye daidai ne Juma'o'in a jere ne ko sun rarrabu, hatta da a ce duk shekara zai bar Juma'a ɗaya da Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yi yumƙi akan zuciyarsa bayan ta uku shi ne zahirin hadisin, kuma zai iya ɗaukar cewa ana nufin Juma'o'i ukun a jere.
Madogara

سنن أبي داود (2/ 284) (1052). سنن الترمذي (1/ 630) (500). سنن النسائي (3/ 88) (1369). سنن ابن ماجه (2/ 213) (1125). مسند أحمد (24/ 255) (15498). النهاية في غريب الحديث والأثر (557). شرح سنن أبي داود للعباد (134/ 3).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com