Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Lallai wasu mutane kodai su hanu daga barin Juma'o'i, ko Allah Zai yi yumƙi akan zukatansu, sannan zasu kasance daga marafkana

عن عبد الله بن عُمر وأبي هريرة رضي الله عنهما أنهما سمعا رسول الله صلى الله عليه وسلم، يقول على أعواد منبره: «لَيَنْتَهِيَنَّ أَقْوَامٌ عَنْ وَدْعِهِمُ الْجُمُعَاتِ أَوْ لَيَخْتِمَنَّ اللهُ عَلَى قُلُوبِهِمْ، ثُمَّ لَيَكُونُنَّ مِنَ الْغَافِلِينَ».
Daga Abdullahi ɗan Umar da kuma Abu Huraira - Allah Ya yarda da su - cewa su sun ji manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbat agare shi - yana faɗa akan minbarinsa: "Lallai wasu mutane kodai su hanu daga barin Juma'o'i, ko Allah Zai yi yumƙi akan zukatansu, sannan zasu kasance daga marafkana"
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kan mimbari ya yi gargaɗi daga barin sallar Juma'a da zama na kin zuwa ba tare da wani uzuri ba, dan wulaƙantarwa da kuma kasala, ko Allah Ya yi yumƙi akan zukatansu Ya rufesu kuma Ya sanya kariyar da zai hanasu bin gaskiya, sannan zasu kasance daga rafkanannu daga sabubban alheri, mai korewa rayukansu ayyukan ɗa'a.

Fa’idoji
  1. Tsanantawa akan masu ƙin zuwa sallar Juma'a, kuma cewa hakan yana daga cikin manyan zunubai.
  2. AlNawawi ya ce: A cikinsa cewa sallar Juma'a farilla ce ta aini (wacce ta wajaba akan kowa da kowa).
  3. Halaccin riƙar minbari dan yin huɗuba.
  4. Sindi ya ce: Ma'ana cewa ɗaya daga cikin al'amura biyu mai kasancewa ne babu makawa, kodai dena barin zuwa Juma'o'i ko Allah Ya yi yumƙi (wato ya toshe) zukatansu, domin cewa sabawa da barin Jumu'o'i yana tabbatar da rufi akan zuciya kuma yana korewa rayuka ayyukan ɗa'a.
  5. Yana kamata ga mai wa'azi da mai tinatarwa ya ɓoye (sunayen) mutanen da yake so ya yi musu wa'azi; domin cewa hakan ya fi saurin sa a karɓi nasiha, da kuma kamanta umarni.
Madogara

صحيح مسلم (2/ 591) (865). النهاية في غريب الحديث والأثر (964). البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (17/ 250).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
Virtue of Friday

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com