Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Idan ka ce wa abokinka: Yi shiru, a ranar Juma'a, a lokacin liman yana huɗuba, to, haƙiƙa ka yi zance mara anfani

عن أبِي هُرَيرةَ رضي الله عنه أنَّ رسول الله صلى الله عليه وسلمَ قال: «إذا قُلْتَ لِصَاحِبِكَ: أَنْصِتْ، يومَ الجمعةِ، والْإِمامُ يَخْطُبُ، فَقَدْ لَغَوْتَ».
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Idan ka ce wa abokinka: Yi shiru, a ranar Juma'a, a lokacin liman yana huɗuba, to, haƙiƙa ka yi zance mara anfani".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa daga ladubba na wajibi ga wanda ya halarci huɗubar Juma'a: Shi ne yin ahieu ga mai huɗuba; don ya yi tuntuntuni cikin wa'azin, kuma wanda ya yi magana - ko da da ƙanƙanin abu ne - alhali liman yana huɗuba, sai ya ce wa waninsa: "Ka yi shiru" ka "saurara", to, haƙiƙa falalar sallar Juma'a ta wuce shi.

Fa’idoji
  1. Haramta zance alokacin jin huɗuba, ko da da hani ne daga abin ƙi, ko amsa sallama da gaishe da mai atishawa.
  2. An togance wanda yake yi wa liman magana, ko liman yake yi masa magana [daga wannan hanin].
  3. Halaccin yin magana a lokacin huɗubobi biyu a yayin buƙata.
  4. Idan an ambaci Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - alhali liman yana huɗuba, to, za ka yi masa salati, a ɓoye, haka nan cewa amin ga addu'a.
Madogara

صحيح البخاري (2/ 13) (934). صحيح مسلم (2/ 583) (851). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص244). تنبيه الأفهام، للعثيمين (2/ 307). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 195). فتح الباري، لابن حجر (2/ 409). تاج العروس من جواهر القاموس، لمحمّد الحسيني الزَّبيدي (39/ 463).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
SALLAR JUMA'A

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com