Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

WAJIBCIN SALLAH DA HUKUNCIN MAI BARINTA

Hadisai 11

An anbaci wani mutum da ya yi bacci a darensa har saida ya wayi gari a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya ce: "Wancan wani mutum ne wanda Shaiɗan ya yi fitsari a cikin kunnuwansa, ko ce ya yi: A cikin kunnensa

عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بنِ مسعُودٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: ذُكِرَ عِنْدَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ رَجُلٌ نَامَ لَيْلَهُ حَتَّى أَصْبَحَ، قَالَ: «ذَاكَ رَجُلٌ بَالَ الشَّيْطَانُ فِي أُذُنَيْهِ، أَوْ قَالَ: فِي أُذُنِهِ».
Daga Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: An anbaci wani mutum da ya yi bacci a darensa har saida ya wayi gari a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya ce: "Wancan wani mutum ne wanda Shaiɗan ya yi fitsari a cikin kunnuwansa, ko ce ya yi: A cikin kunnensa".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

An anbaci wani mutumin da ya yi bacci har gari ya waye rana ta ɓullo bai tashi ya yi sallar farilla ba a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Lallai shi wani mutum ne wanda Shaiɗan ya yi fitsari a cikin kunnansa.

Fa’idoji
  1. Karhancin barin tsayuwar dare, kuma cewa hakan da sababin Shaiɗan ne.
  2. Tsoratarwa daga Shaiɗan wanda yake zama ga mutum a kan kowace hanya; dan ya tsare tsakaninsa da tsakanin ɗa'ar Allah - Mai girma da ɗaukaka -.
  3. Ibnu Hajar ya ce: Faɗinsa: (Bai tashi zuwa sallah ba) abin nufi jinsi, kuma zai iya ɗaukar alƙawari, kuma ana nufin sallar dare ko (sallar) farillah da shi.
  4. Al-Ɗaibi ya ce: An keɓanci kunne da anbato, duk da ido yafi dacewa da bacci, dan yin nuni zuwa nauyin bacci, domin cewa kunnuwa sune magangarar farkawa, kuma an keɓanci fitsari; domin cewa shi ya fi sauƙin shiga a cikin ciki, kuma mafi saurin zarcewa a cikin jijiyoyi, sai ya gadar da kasala a cikin dukkan gaɓɓai.
Madogara

صحيح البخاري (4/ 122) (3270). صحيح مسلم (1/ 537) (774). بهجة الناظرين، لسليم الهلالي (2/ 328). نزهة المتقين، لمجموعة من الباحثين (2/ 834). فتح الباري شرح صحيح البخاري، لأحمد العسقلاني (3/ 28). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (5/ 193). المنهاج شرح صحيح مسلم بن الحجاج، النووي (6/ 64).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

ku umarci 'ya'yanku da yin sallah alhali su suna 'yan shekara bakwai, kuma ku dake su akanta alhali su suna 'yan shekara goma, kuma ku raba tsakaninsu a wurin kwanciya

عن عمرو بن شُعيب عن أبيه عن جدِّه قال: قال رسولُ الله صلى الله عليه وسلم: «مُرُوا أولادكمِ بالصلاةِ وهم أبناءُ سبعِ سِنينَ، واضرِبوهم عليها وهم أبناءُ عَشرٍ، وفرِّقوا بينهم في المَضاجِعِ».
Daga Amr Dan Shu'aib daga babansa daga kakansa ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "ku umarci 'ya'yanku da yin sallah alhali su suna 'yan shekara bakwai, kuma ku dake su akanta alhali su suna 'yan shekara goma, kuma ku raba tsakaninsu a wurin kwanciya".
Abu Dawud ne Ya Rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa ya wajaba akan uba ya umarci 'ya'yansa - maza da mata - da yin sallah alhali suna da shekara bakwai, kuma ya sanar dasu abinda suke bukata dan tsaida ita. Idan suka kai shekara goma sai ya yi kari akan umarnin, sai ya yi duka akan kasa yin Sallar, kuma ya raba a tsakaninsu a shinfida.

Fa’idoji
  1. Sanar da 'ya'ya kanana al'amuran Addini kafin balaga, daga mafi muhimmancinsu sallah.
  2. Duka yana kasancewa ne dan ladabtarwa, ba dan azabtarwa ba, sai ya yi dukan da ya dace da halinsa.
  3. Kulawar shari'a a kiyaye mutunci, da toshe kowacce hanyar da zata iya kaiwa zuwa barna.
Madogara

سنن أبي داود (1/ 367) (495، 496). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، مجموعة من الباحثين (1/ 299). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 382).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Duk wanda ya bar sallar la’asar, to, aikinshi ya ɓaci

عن بريدة بن الحصيب رضي الله عنه أنه قال: بَكِّرُوا بِصَلَاةِ الْعَصْرِ، فَإِنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَنْ تَرَكَ صَلَاةَ الْعَصْرِ فَقَدْ حَبِطَ عَمَلُهُ».
Daga Abu Buraidah Ɗan Husaib, Allah ya yarda da shi ya ce: Ku gaggauta sallar La’asar a kan lokaci, domin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Duk wanda ya bar sallar la’asar, to, aikinshi ya ɓaci.
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya tsawatar a kan jinkirta sallar La’asar daga lokacinta da gangan, kuma duk wanda ya yi hakan, to, aikinsa ya lalace, ya tafi kawai a watse.

Fa’idoji
  1. Kwaɗaitarwa a kan kiyaye sallar la’asar a farkon lokacinta, da kuma gaggawar yinta.
  2. Narkon azaba mai tsanani ga wanda ya bar sallar La’asar har loakcita ya fita, kuma barinta har fitar Lokacita ya fi tsanani a kan wata da ba ita ba, domin ita ce Sallah mafificiya wacce aka keɓance ta da umarni a faɗin Allah maɗaukaki: ((Ku kiyaye Salloli kuma ku kiyaye sallah mafificiya)). Bakara, 238.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 115) (553). مسند أحمد (38/ 152) (23045). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (5/ 56). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمصطفى الخِن وغيره (2/ 777). فيض القدير شرح الجامع الصغير (3/ 206). بهجة الناظرين، لسليم الهلالي (2/ 260). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص614).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

An gina Musulunci abisa abubuwa biyar

عَنْ عَبْدِ اللهِ بنِ عُمَر رضي الله عنهما قال: قال رسولُ الله صلى الله عليه وسلم: «بُنِيَ الْإِسْلَامُ عَلَى خَمْسٍ: شَهَادَةِ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، وَأَنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ، وَإِقَامِ الصَّلَاةِ، وَإِيتَاءِ الزَّكَاةِ، وَحَجِّ الْبَيْتِ، وَصَوْمِ رَمَضَانَ».
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "An gina Musulunci abisa abubuwa biyar, shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa ne, da tsaida sallah, da bada zakka, da ziyarar daki, da azimin Ramadan".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kamanta musulunci da ingantaccen gini da rukunansa biyar masu dauke da wancan ginin, ragowar dabi'un musulunci kamar cika ginin ne, Farkon wadanan rukunan: Shaidawa biyu; shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, (shaidawa) Annabi Muhammadu Manzon Allah ne, su rukuni daya ne; dayansu ba ya rabuwa da dayan, bawa zai furtasu yana mai tabbatar da kadaituwar Allah da kuma cancantarSa ga bauta Shi kadai banda waninSa, kuma yana mai aiki da abinda suka hukunta, kuma yana mai imani da Manzancin Annabi Mukammadu - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana mai binsa. Rukuni na biyu: Tsaida sallah, su ne sallolin farillai biyar a yini da dare: Asuba, da Azahar, da La'asar, da magariba, da Lisha, da sharuddansu da rukunansu da wajibansu. Rukuni na uku: Fitar da zakkar farilla, ita ibada ce ta dukiya wajiba a kowacce dukiyar da takai wani gwargwado abin iyakancewa a shari'a, ana bada ita ga wadanda suka cancanceta. Rukuni na hudu: Hajji, shi ne nufin Makka dan tsaida ibadu, dan yin bauta ga Allah - Mai girma da daukaka -. Rukuni na biyar: Azumin Ramadan, shi ne kamewa daga ci da sha da wasunsu daga masu bata azimi da niyyar bauta ga Allah, daga bullowar alfijir zuwa faduwar rana.

Fa’idoji
  1. Lazimtuwar shaidawa biyu, dayansu ba ya inganta sai da dayan; saboda haka ya sanya su rukuni daya ne.
  2. Shaidawa biyu su ne tushen Addini, ba'a karbar wata magana ko wani aiki sai da su.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 11) (8)، صحيح مسلم (1/ 45) (16)، و(1/ 88) (82)، فتح الباري لابن رجب (1/ 22)، جامع العلوم والحكم (1/147)، شرح الأربعين لابن العطّار (ص 62)، شرح الأربعين النووية لعبد الكريم الخضير (ص 87)، فتح القوي المتين في شرح الأربعين للعباد (ص 29)، شرح الأربعين النووية لصالح آل الشيخ (ص 91 - 95)، التحفة الربانية لإسماعيل الأنصاري (ص 12).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ni ne Dimam dan Sa'alabata dan uwan Banu Sa'ad dan Bakar

عن أَنَسَ بْنَ مَالِكٍ رضي الله عنه قال: بينما نحن جلوس مع النبي صلى الله عليه وسلم في المسجد دخل رجل على جمل، فأناخه في المسجد ثم عقله، ثم قال لهم: أيكم محمد؟ والنبي صلى الله عليه وسلم متكئ بين ظهرانيهم، فقلنا: هذا الرجل الأبيض المتكئ. فقال له الرجل: يا ابن عبد المطلب فقال له النبي صلى الله عليه وسلم: «قد أجبتك». فقال الرجل للنبي صلى الله عليه وسلم: إني سائلك فمشدد عليك في المسألة، فلا تجد علي في نفسك؟ فقال: «سل عما بدا لك» فقال: أسألك بربك ورب من قبلك، آلله أرسلك إلى الناس كلهم؟ فقال: «اللهم نعم». قال: أنشدك بالله، آلله أمرك أن نصلي الصلوات الخمس في اليوم والليلة؟ قال: «اللهم نعم». قال: أنشدك بالله، آلله أمرك أن نصوم هذا الشهر من السنة؟ قال: «اللهم نعم». قال: أنشدك بالله، آلله أمرك أن تأخذ هذه الصدقة من أغنيائنا فتقسمها على فقرائنا؟ فقال النبي صلى الله عليه وسلم: «اللهم نعم». فقال الرجل: آمنت بما جئت به، وأنا رسول من ورائي من قومي، وأنا ضمام بن ثعلبة أخو بني سعد بن بكر.
Daga Anas Ibnu Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Muna zaune tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin masallaci sai wani mutum ya shigo akan wani rakumi, sai ya dirkusar da shi a cikin masallaci sannan ya daure shi, sannan ya ce da su: Waye Muhammad a cikinku? alhali Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kishingide a tsakaninsu, sai muka ce : Wannan farin mutumin wanda ke kishingide. Sai mutumin ya ce da shi: Ya kai Dan Abdul Mudallib sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce da shi: "Hakika na amsa maka". Sai mutumin ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ni mai tambayarka ne mai tsananta maka a tambaya, kada ka ji haushi na a ranka? sai ya ce: "Ka tambayi abinda ya bayyana gareka" sai ya ce: Ina tambayarka dan Ubangijinka da Ubangijin wadanda suka gabaceka, shin Allah ne Ya aikoka zuwa ga mutane gaba dayansu? sai ya ce: "Eh ya Allah". Ya ce: Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da mu yi salloli biayr a yini da dare? ya ce: "Eh ya Allah ne.” ya ce Ina maka magiya da Allah shin Allah ne Ya umarceka da mu yi azumin wannan watan a shekara? ya ce: "Eh ya Allah". Ya ce; Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da ka karbi wannan sadakar daga mawadatanmu sai ka rabata ga talakawan mu? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Eh ya Allah". sai mutumin ya ce; na yi imani da abinda ka zo da shi, kuma ni manzo ne na wadanda ke bayana cikin mutane na, Ni ne Dimam dan Sa'alabata dan uwan Banu Sa'ad dan Bakar.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Anas dan Malik - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa: Lokacin da sahabbai suna zaune tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin masallaci yayin da wani mutum ya shigo akan wani rakumi, sai ya durkusar da rakumin sannan ya daure shi. Sannan ya tambayesu: Waye Muhammd a cikinku? Alhali Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kishingide tsakanin mutanen, sai muka ce : Wannan farin mutumin. Sai mutumin ya ce da shi: Yakai Dan Abdul Muddalib. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce da shi: Na ji ka yi tambaya in amsa maka. Sai mutumin ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ni mai tambayarka ne kuma mai tsananta maka a tambaya, kada ka ji wani abu game dani a ranka. Wato: Kada ka yi fushi da ni kuma kada kunci ya sameka. Sai ya ce: Ka tambayi abinda kake so. Sai ya ce: Ina ina hada ka da Ubangijinka kuma Ubangijin wadanda suka gabace ka, shin Allah ne Ya aikoka zuwa ga mutane? Sai ya ce: Eh ya Allah, dan karfafa gaskiyarsa. Sai Mutumin ya ce: Ina yi maka magiya da Allah, wato; Ina tambayarka sabo da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da ka yi salloli biyar a yini da dare? Su ne salloli wadanda aka faralanta ?., Ya ce: Eh ya Allah, Ya ce: Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da mu azimci wannan watan daga shekara? wato: Watan Ramadan, Ya ce: Eh ya Allah, Ya ce: Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka daka karbi wannan sadakar daga mawadatanmu sai ka rabata ga talakawanmu? ita ce zakka. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Eh ya Allah, Sai Dimam ya musulunta, kuma ya ba Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - labarin cewa shi zai kira mutanensa zuwa Musulunci. Sannan ya yi bayanin kansa cewa shi ne Dimam dan Sa'alabata daga Banu Sa'ad Ibnu Bakar.

Fa’idoji
  1. Tawali'un Annabi - tsira da aminci su tabbata agare shi -; dan mutum ba zai iya banbancewa ya raba tsakaninsa da sahabbansa ba.
  2. Kyakkyawar dabi'un Annabi - aminci ya tabbata agare shi -, da tausasawarsa a bada amsa ga mai tambaya, kuma cewa kyakkyawar bada amsa tana daga sabubban karbar Da’awah.
  3. Halaccin bayanin mutum da wata siffa na fari da ja, da tsawo da gajarta, da makamancin wannan daga abinda ba'a nufin aibatawa da shi, idan ba ya kin hakan.
  4. Halaccin shigar kafiri masallaci dan bukata.
  5. Bai ambaci Hjji ba a cikin hadisin domin cewa shi zai iya kasancewa ba'a wajabta Hajjin ba a lokacin zuwansa ba.
  6. Kwadayin sahabbai akan kiran mutane; daga musuluntarsa ya yi kwadayin kiran mutanensa.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 23) (63)، صحيح مسلم (1/ 41) (12)، شرح ابن بطال (1/145)، عمدة القاري شرح صحيح البخاري (2/ 22).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Wanda ya manta wata sallah, to, ya sallaceta idan ya tunata, babu kaffara gareta sai hakan

عن أنس بن مالك رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «مَنْ نَسِيَ صَلَاةً فَلْيُصَلِّ إِذَا ذَكَرَهَا، لَا كَفَّارَةَ لَهَا إِلَّا ذَلِكَ: {وَأَقِمِ الصَّلاةَ لِذِكْرِي} [طه: 14]».
Daga Anas Ɗan Malik Allah Ya yarda da shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Wanda ya manta wata sallah, to, ya sallaceta idan ya tunata, babu kaffara gareta sai hakan: {Ku tsai da sallah domin tunani} [Daha: 14".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayya cewa wanda ya mance yin kowacce sallar farilla har lokacinta ya fita, to, ya wajaba a kansa ya yi gaggawar ramata a duk lokacin da ya tunata, babu gogewa ko suturtawa ga laifin barinta sai dai kawai musulmi ya sallaceta a yayin da ya tunata, Allah Ya faɗa a littafinSa Mai girma: {Ka tsai da sallah domin tunaNi} [Daha: 14], wato: Ka tsai da sallar daka manta idan ka tunata.

Fa’idoji
  1. Bayanin muhimmancin sallah da rashin ko’unkula da yinta da kuma ramata.
  2. Jinkirta sallah daga lokacinta da gangan ba tare da wani uzuri ba ba ya halatta.
  3. Wajabcin rama sallah a kan mai mantuwa idan ya tuna, da mai bacci idan ya farka.
  4. Wajabcin rama salloli a gaggauce ko da a lokutan hani ne.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 122) (597)، صحيح مسلم (1/ 477) (684)، فتح الباري لابن حجر (2/ 71)، البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (14/ 612).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Lallai tsakanin mutum da shirka da kafirci (shi ne) barin sallah

عن جابرٍ رضي الله عنه قال: سمعت النبي صلى الله عليه وسلم يقول: «إِنَّ بَيْنَ الرَّجُلِ وَبَيْنَ الشِّرْكِ وَالْكُفْرِ تَرْكَ الصَّلَاةِ».
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Lallai tsakanin mutum da shirka da kafirci (shi ne) barin sallah".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi gargaɗi game da barin sallar farilla, ya ba da labarin cewa tsakanin mutum da afkawa a shirka da kafirci (shi ne) barin sallah, sallah ita ce rukuni na biyu daga rukunan musulunci, al'amarinta mai girma ne a musulunci, wanda ya barta yana mai musun wajabcinta, to, ya kafirta da ijima'in musulmai, idan ya barta gabaɗaya don wulaƙantarwa da kasala, to, shi kafiri ne, an cirato ijma'in sahabbai a kan hakan, idan ya kasance yana bari wani lokaci wani lokaci kuma yana yin sallah, to, ya kai kansa ga wannan narkon mai tsanani.

Fa’idoji
  1. Muhimmancin sallah da kiyayewa a kanta, ita ce mai banbanta wa tsakanin kafirci da imani.
  2. Gargaɗi mai tsanani a kan barin sallah da tozartata.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 88) (82)، المفهم لما أشكل من تلخيص كتاب مسلم (1/ 271)، البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (2/ 622).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Lallai alƙawarin da ke tsakanin mu da su (shi ne) sallah, wanda ya barta, to, haƙiƙa ya kafirta

عن بريدة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «إِنَّ الْعَهْدَ الَّذِي بَيْنَنَا وَبَيْنَهُمُ الصَّلَاةُ، فَمَنْ تَرَكَهَا فَقَدْ كَفَرَ».
Daga Buraidah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce -: "Lallai alƙawarin da ke tsakanin mu da su (shi ne) sallah, wanda ya barta, to, haƙiƙa ya kafirta".
Tirmizi da Nasa'i da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa alƙawari tsakanin musulmai da wasunsu daga kafirai da munafikai (shi ne) sallah, wanda ya barta to haƙiƙa ya kafirta.

Fa’idoji
  1. Girman al'amarin sallah, kuma cewa ita ce mai banbantawa tsakanin mumini da kafiri.
  2. Tabbatar da hukunce-hukuncen musulunci da zahiri daga halin mutum ba baɗininsa ba.
Madogara

سنن النسائي (1/ 231) (463)، سنن الترمذي (4/ 365) (2621)، سنن ابن ماجه (2/ 181) (1079)، مسند أحمد (38/ 20) (22937)، فيض القدير (4/ 395)، ذخيرة العقبى في شرح المجتبى (6/ 192) (6/ 193).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
8 cikin 11
Hadisai 11
  1. An anbaci wani mutum da ya yi bacci a darensa har saida ya wayi gari a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya ce: "Wancan wani mutum ne wanda Shaiɗan ya yi fitsari a cikin kunnuwansa, ko ce ya yi: A cikin kunnensa
  2. ku umarci 'ya'yanku da yin sallah alhali su suna 'yan shekara bakwai, kuma ku dake su akanta alhali su suna 'yan shekara goma, kuma ku raba tsakaninsu a wurin kwanciya
  3. Duk wanda ya bar sallar la’asar, to, aikinshi ya ɓaci
  4. An gina Musulunci abisa abubuwa biyar
  5. Ni ne Dimam dan Sa'alabata dan uwan Banu Sa'ad dan Bakar
  6. Wanda ya manta wata sallah, to, ya sallaceta idan ya tunata, babu kaffara gareta sai hakan
  7. Lallai tsakanin mutum da shirka da kafirci (shi ne) barin sallah
  8. Lallai alƙawarin da ke tsakanin mu da su (shi ne) sallah, wanda ya barta, to, haƙiƙa ya kafirta
  9. Wanda ya sallaci irin sallarmu kuma ya fuskanci alƙiblarmu, kuma ya ci yankanmu to wannan shine muslmin da yake da alƙawarin Allah da alƙawarin ManzonSa, dan haka kada ku warware alƙawarin Allah
  10. Ku kula da sallah da abinda hannayenku suka mallaka
  11. An gina Musulunci abisa abubuwa biyar

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com