Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

ku umarci 'ya'yanku da yin sallah alhali su suna 'yan shekara bakwai, kuma ku dake su akanta alhali su suna 'yan shekara goma, kuma ku raba tsakaninsu a wurin kwanciya

عن عمرو بن شُعيب عن أبيه عن جدِّه قال: قال رسولُ الله صلى الله عليه وسلم: «مُرُوا أولادكمِ بالصلاةِ وهم أبناءُ سبعِ سِنينَ، واضرِبوهم عليها وهم أبناءُ عَشرٍ، وفرِّقوا بينهم في المَضاجِعِ».
Daga Amr Dan Shu'aib daga babansa daga kakansa ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "ku umarci 'ya'yanku da yin sallah alhali su suna 'yan shekara bakwai, kuma ku dake su akanta alhali su suna 'yan shekara goma, kuma ku raba tsakaninsu a wurin kwanciya".
Abu Dawud ne Ya Rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa ya wajaba akan uba ya umarci 'ya'yansa - maza da mata - da yin sallah alhali suna da shekara bakwai, kuma ya sanar dasu abinda suke bukata dan tsaida ita. Idan suka kai shekara goma sai ya yi kari akan umarnin, sai ya yi duka akan kasa yin Sallar, kuma ya raba a tsakaninsu a shinfida.

Fa’idoji
  1. Sanar da 'ya'ya kanana al'amuran Addini kafin balaga, daga mafi muhimmancinsu sallah.
  2. Duka yana kasancewa ne dan ladabtarwa, ba dan azabtarwa ba, sai ya yi dukan da ya dace da halinsa.
  3. Kulawar shari'a a kiyaye mutunci, da toshe kowacce hanyar da zata iya kaiwa zuwa barna.
Madogara

سنن أبي داود (1/ 367) (495، 496). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، مجموعة من الباحثين (1/ 299). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 382).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
WAJIBCIN SALLAH DA HUKUNCIN MAI BARINTA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com