Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayya cewa wanda ya mance yin kowacce sallar farilla har lokacinta ya fita, to, ya wajaba a kansa ya yi gaggawar ramata a duk lokacin da ya tunata, babu gogewa ko suturtawa ga laifin barinta sai dai kawai musulmi ya sallaceta a yayin da ya tunata, Allah Ya faɗa a littafinSa Mai girma: {Ka tsai da sallah domin tunaNi} [Daha: 14], wato: Ka tsai da sallar daka manta idan ka tunata.
- Bayanin muhimmancin sallah da rashin ko’unkula da yinta da kuma ramata.
- Jinkirta sallah daga lokacinta da gangan ba tare da wani uzuri ba ba ya halatta.
- Wajabcin rama sallah a kan mai mantuwa idan ya tuna, da mai bacci idan ya farka.
- Wajabcin rama salloli a gaggauce ko da a lokutan hani ne.
صحيح البخاري (1/ 122) (597)، صحيح مسلم (1/ 477) (684)، فتح الباري لابن حجر (2/ 71)، البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (14/ 612).