Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

FALALOLI NA SURORI DA AYOYI

Hadisai 14

Lallai cewa Annabi ya aika Wani Mutum a wani yaki sai ya kasane yana" karantawa abokansa in yana jansu Sallah, Sai yake cika karatunsa da: Kulhuwa.

عن عائشة رضي الله عنها «أن رسول الله صلى الله عليه وسلم بعث رجلا على سَرِيَّةٍ فكان يَقْرَأ لأصحابه في صلاتهم، فَيَخْتِمُ بـ«قل هو الله أحد» فلما رجعوا ذكروا ذلك لرسول الله صلى الله عليه وسلم فقال: سَلُوهُ لأَيِّ شيء صَنَع ذلك؟ فسألُوه، فقال: لِأنَّها صِفَةُ الرحمن عز وجل ، فأنا أُحِب أَنْ أَقْرَأ بها، فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم : أَخْبِرُوه: أنَّ الله تعالى يُحِبُّه».
Daga Nana Aisha -Allah yarda da ita- "allai cewa Annabi ya aika Wani Mutum a wani yaki sai ya kasane yana" karantawa abokansa in yana jansu Sallah, Sai yake cika karatunsa da: Kulhuwa"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi -Tsira da aminci Allah su tabbata a gareshi- ya wakilata wasu daga Sahannabnsa a kan wata Rundunar yaki, don Jagorantar ta da kuma yin hukunci a tsakaninsu, kuma don kada abin ya zama babu tsari, kuma ya zabi wanda ya fi kowanne Addini da Ilimi da kuma iya tafi da yaki, shi yasa Shugabannin sune Limamai a cikin salloli, kuma su suke bada Fatawa sabida Iliminsu da Addininsu, to sai ya rika karanta musu Kulhuwa a kowace Rakao'i biyu na kowace Sallah; sabida sonsa da Allah da kuma sunayensa da sifofinsa, kuma duk wanda yaso Allah to zai yawaita ambatonsa, to yayin da suka dawo daga yakin nasu zuwa ga Annabi sai suka gaya masa abinda ya faru sai ya cce ku tambayae shi mai yasa yake yi sai suka tambayeshi mai yasa yake yin hakan haka kawai yake yi ko kuma sabida wani abu ne? sai Jagoran nasu ya ce: ina yin haka ne Sabida ta kunshi sifofin Allah don haka nake son Maimaita ta sai Annabi ya ce ku gaya masa kamar yadda ya ke maimaita wannan sura saboda soyayyarsa da ita; kuma sabida abinda ta kunsa na sifofin Allah masu girma wanda wannan Surata kunsa na Sunayensa da aka ambata, to shima Allah yana sonsa, kai wannan ta isa falala.

Madogara

تيسير العلام للبسام الناشر: مكتبة الصحابة، الإمارات - مكتبة التابعين، القاهرة الطبعة- العاشرة، 1426 هـ - 2006 م. تنبيه الأفهام للعثيمين، طبعة مكتبة الصحابة - الإمارات - مكتبة التابعين- القاهرة- الطبعة الأولى 1426. الإلمام بشرح عمدة الأحكام لإسماعيل الأنصاري -طبعة دار الفكر- دمشق -الأولى 1381. صحيح البخاري، أبو عبد الله محمد بن إسماعيلالجعفي البخاري - تحقيق محمد زهير بن ناصر الناصر -الناشر : دار طوق النجاة - الطبعة الأولى 1422هـ. صحيح مسلم، أبو الحسين مسلم بن الحجاج القشيري النيسابوري، المحقق: محمد فؤاد عبد الباقي - الناشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت. تأسيس الأحكام، أحمد بن يحيى النجمي- دار المنهاج- القاهرة- مصر -الطبعة الأولى.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ka yi albishir da haske biyu da aka ba ka su, wanda ba'a bawa wani Annabi kafinka ba; Ita ce Fatihatul Kitab, da ƙarshen suratul Baƙarah, ba za ka karanta wani harafi daga cikinsu ba sai an ba ka shi

عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما قَالَ: «بَيْنَمَا جِبْرِيلُ قَاعِدٌ عِنْدَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ سَمِعَ نَقِيضًا مِنْ فَوْقِهِ، فَرَفَعَ رَأْسَهُ، فَقَالَ: هَذَا بَابٌ مِنَ السَّمَاءِ فُتِحَ الْيَوْمَ لَمْ يُفْتَحْ قَطُّ إِلَّا الْيَوْمَ، فَنَزَلَ مِنْهُ مَلَكٌ، فَقَالَ: هَذَا مَلَكٌ نَزَلَ إِلَى الْأَرْضِ لَمْ يَنْزِلْ قَطُّ إِلَّا الْيَوْمَ، فَسَلَّمَ، وَقَالَ: أَبْشِرْ بِنُورَيْنِ أُوتِيتَهُمَا لَمْ يُؤْتَهُمَا نَبِيٌّ قَبْلَكَ: فَاتِحَةُ الْكِتَابِ، وَخَوَاتِيمُ سُورَةِ الْبَقَرَةِ، لَنْ تَقْرَأَ بِحَرْفٍ مِنْهُمَا إِلَّا أُعْطِيتَهُ».
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: «‌Yayin da (Mala’ika) Jibrilu yake zaune a wurin Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ji wata ƙara daga samansa, sai ya ɗaga kansa sama, sai ya ce: Wannan wata ƙofa ce daga sama da aka buɗeta a yau, ba'a taɓa buɗe ta ba sai yau, sai wani Mala'ika ya sauko daga cikinta, sai ya ce: Wannan wani Mala'ika ne da ya sauko ƙasa, kuma bai taɓa sakkowa ba sai yau, sai ya yi sallama, ya ce: Ka yi albishir da haske biyu da aka ba ka su, wanda ba'a bawa wani Annabi kafinka ba; Ita ce Fatihatul Kitab, da ƙarshen suratul Baƙarah, ba za ka karanta wani harafi daga cikinsu ba sai an ba ka shi».
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Mala'ika Jibril - aminci ya tabbata agare shi - ya kasance a zaune a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ji wata ƙara daga sama kamar ƙarar ƙofar da aka buɗe, sai Mala’ika Jibril ya ɗaga kansa da idansa zuwa sama, sannan ya ba Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - labarin cewa wannan wata ƙofa ce daga sama da aka buɗeta a yau, kuma ba'a taɓa buɗeta ba sai yau ɗin nan, sai wani mala'ika daga cikin mala'iku ya sauko daga gareta zuwa ƙasa, bai taɓa sauka ba kafin nan sai yau, sai mala'ikan ya yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sallama, kuma ya ce da shi: Ina maka bushara da haske biyu waɗanda aka baka ba'a taɓa bawa wani Annabi kafinka ba; sune: Suratul Fatiha, da kuma ƙarshen ayoyi biyu na Suratul Baƙara. Sannan mala'ikan ya ce: Wani ba zai karanta wani harafi daga garesu ba sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ba shi abinda ke cikinsu na alheri da addu'a da kuma abin da yake nema.

Fa’idoji
  1. Falalar Suratul Fatiha da ƙarshen Suratul Baƙara, da kuma kwaɗaitarwa akan karanta su da aiki da abinda ke cikinsu.
  2. Sama tana da ƙofofi waɗanda umarnin Ubangiji yake sauka daga garesu, kuma ba'a buɗesu sai da umarnin Allah - Maɗaukakin sarki -.
  3. Bayanin girman Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wurin UbangijinSa, inda Ya girmama shi da abinda bai taɓa girmama Annabawan dake gabaninsa ba, sai Ya ba shi waɗannan haske biyun.
  4. Daga tsarin kira zuwa ga Allah yin bushara ta alheri.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 554) (806). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 244). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (4/ 700). مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي القاري (4/ 1464). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 760). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (13/ 122).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kada ku mayar da gidajenku makabarta, Shaiɗan yana guduwa daga gidan da ake karanta Surat Al-Bakarah a cikinsa

عن أبي هريرة رضي الله عنه: أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «لَا تَجْعَلُوا بُيُوتَكُمْ مَقَابِرَ، إِنَّ الشَّيْطَانَ يَنْفِرُ مِنَ الْبَيْتِ الَّذِي تُقْرَأُ فِيهِ سُورَةُ الْبَقَرَةِ».
Daga Abu Hurairah Allah Ya yarda da shi, Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Kada ku mayar da gidajenku makabarta, Shaiɗan yana guduwa daga gidan da ake karanta Surat Al-Bakarah a cikinsa".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana yin hani daga wofintar da gidaje daga sallah, sai su zama kamar maƙabartu, da ba a sallah a cikinsu. Sannan sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ba da labarin shaiɗan yana ficewa daga gidan da ake karanta Suratul Baƙara.

Fa’idoji
  1. Ana so a yawaita ibada da Sallolin Nafila a gidaje.
  2. Ba ya halatta yin Sallah a maƙabarta, domin hakan hanya ce daga hanyoyin shirka da wuce iyaka ga masu su, in banda sallar Janaza.
  3. Hanin yin Sallah a inda akwai kabari, ya tabbata a wurin Sahabbai, saboda haka Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana a sanya gidaje kamar maƙabartu, waɗanda su ba a Sallah a cikinsu.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 539) (780). بهجة الناظرين، لسليم الهلالي (2/ 240). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (4/ 682). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمصطفى الخِن وغيره (2/ 757). مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي القاري (4/ 1460).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Wanda ya haddace ayoyi goma daga farkon Suratul Kahf, za'a tsare shi daga Dujal". A cikin wata riwayar: "Daga ƙarshen Suratul Kahf

عن أبي الدرداء رضي الله عنه أن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «مَنْ حَفِظَ عَشْرَ آيَاتٍ مِنْ أَوَّلِ سُورَةِ الكَهْفِ، عُصِمَ مِنَ الدَّجَّالِ». وفي رواية: «مِنْ آخِرِ سُورَةِ الكَهْف».
Daga Abu Darda'i - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya haddace ayoyi goma daga farkon Suratul Kahf, za'a tsare shi daga Dujal". A cikin wata riwayar: "Daga ƙarshen Suratul Kahf".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya haddace ayoyi goma a zahirin zuciya (hadda) daga farkon Suratul Kahf za'a tsare shi za'a kare shi daga fitinar Masihul Dajjal wanda zai fito a ƙarshen zamani kuma zai yi da'awar Uluhiyya (Allantaka), kuma fitinarsa ita ce mafi girman fitinar da za ta kasance a kan ƙasa tun lokacin da aka halicci (annabi) Adam har zuwa tashin alƙiyama; saboda abinda Allah - Mai girma da ɗaukaka - Zai tabbatar masa daga sashin al'amura masu saɓa hankali waɗanda zai fitini wanda ya bi shi, hakan domin cewa farkon Suratul Kahf a cikinta akwai abubuwan mamaki da ayoyi abinda yake yafi girma daga abinda Dujal zai fitini mutane a cikinsa, wanda ya yi tuntuntuni to ba za'a fitina shi da Dujjal ba. A cikin wata riwayar: Ayoyi goma daga ƙarshen surar daga faɗinSa - Maɗaukakin sarki -: {Shin waɗanda suka kafirta suna zatan zasu riƙi...}.

Fa’idoji
  1. Bayanin falalar Suratul Kahf, kuma cewa (ayoyin) farkonta ko (ayoyin) ƙarshenta suna kiyayewa daga fitinar Dajjal.
  2. Labartawa daga al'amarin Dajjal, da bayanin abinda zai tsare shi .
  3. Kwaɗaitarwa akan haddace Suratul Kahf cikakkiya, idan ya gajiya to ya haddace ayoyi goman farko da na ƙarshe.
  4. AlƘurɗubi ya faɗa a cikin sababin hakan: An ce: Dan abinda ke cikin ƙissar Ashabul Kahf (Ma’abota Kogo) na abubuwan mamaki da ayoyi, wanda ya tsaya a kan su ba zai yi mamakin al'amarin Dajjal ba kuma hakan ba zai shagaltar da shi ba to ba zai fitinu da shi ba, kuma an ce: Saboda faɗinSa ne - Maɗaukakin sarki -: {Domin ya yi gargaɗi da azaba mai tsanani daga gare shi } dan yin riƙo da keɓantar azaba da tsanani daga gare shi , shi ya dace da abinda zai kasance daga Dajjal na da'awar Uluhiyya (allantaka) da rinjayarsa da girman fitinarsa, saboda haka ne tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya girmama al'amarinsa kuma ya gargaɗar daga fitinarsa, sai ma'anar hadisin ta zama: Cewa wanda ya karanta wadannan ayoyin kuma ya yi nazarin ma'anoninsu kuma ya tsaya akaan ma'anoninsu to ya kuɓuta daga gare shi .
Madogara

صحيح مسلم (1/ 555) (809). بهجة الناظرين، لسليم الهلالي (2/ 243). شرح النووي على مسلم (6/ 92). فيض القدير شرح الجامع الصغير، لعبدالرؤوف المناوي (6/ 119). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (13/ 115). مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لملا القاري (4/ 1465). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمصطفى الخن (2/ 760).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Wanda ya karanta ayoyi biyu na ƙarshen Suratul Bakara da daddare sun ishe shi

عن أبي مسعود رضي الله عنه قال: قال النبي صلى الله عليه وسلم: «مَنْ قَرَأَ بِالْآيَتَيْنِ مِنْ آخِرِ سُورَةِ الْبَقَرَةِ فِي لَيْلَةٍ كَفَتَاهُ».
Daga Abu Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Wanda ya karanta ayoyi biyu na ƙarshen Suratul Bakara da daddare sun ishe shi.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ba da bayanin duk wanda ya karanta ayoyi biyun ƙarshe na Suratul Baƙara cikin dare, to, Allah zai tsare shi daga sharri da abin ƙi, wasu kuma suka ce: Sun ishe shi nafilar dare, wasu kuma suka ce: Sun ishe shi addu’oin dare. An ce kuma: su ne mafi ƙarancin abin da zai isa na karatun Alkur’ani a nafilar dare, an ma faɗi wanin haka, kuma muna fatan duk abin da aka faɗa ɗin daidai ne, domin zai ƙunshe su duka

Fa’idoji
  1. Bayanin falalar [ayoyin] ƙarshen Baƙara, su ne daga faɗin Allah: (( Manzon ya yi imani….. har zuwa ƙarshen Surah.
  2. Ƙarshen Suratul Baƙara yana tunkuɗewa wanda ya karanta mugun abu da sharri da shaiɗanu, idan ya karanta su da daddare.
  3. Dare yana farawa ne daga faɗuwar rana, yana kuma ƙarewa ne da hudowar alfijir.
Madogara

صحيح البخاري (6/ 188) (5008-5009). صحيح مسلم (1/ 554) (807). فتح الباري بشرح صحيح البخاري، لابن حجر (9/ 56). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 240). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص593). مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لملا علي القاري (4/ 1465). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمصطفى الخِن وغيره (2/ 757).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Baka ga Wasu Ayoyi da aka saukar da su ba a wannan Daren ba'a tava ganinsu ba? Falaqi da Nasi

عن عقبة بن عامر رضي الله عنه : أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «ألَمْ تَرَ آيَاتٍ أُنْزِلَتْ هذِهِ اللَّيْلَةَ لَمْ يُرَ مِثْلُهُنَّ قَطُّ؟ (قل أعوذ برب الفلق) و(قل أعوذ برب الناس)».
Daga Uqbah bn Amer - yardar Allah ta tabbata a gare shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: “Shin ba ku ga alamun da aka saukar a wannan daren ba, irinsu ba su taba ba an gani? (Ka ce ina neman tsari ga Ubangijin mutane) da (Ka ce ina neman tsari ga Ubangijin mutane) ».
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

1-بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين؛ تأليف سليم الهلالي، دار ابن الجوزي.-الدمام 1415 2-رياض الصالحين من كلام سيد المرسلين؛ للإمام أبي زكريا النووي، تحقيق د. ماهر الفحل، دار ابن كثير-دمشق، الطبعة الأولى، 1428هـ. 3-شرح رياض الصالحين؛ للشيخ محمد بن صالح العثيمين، مدار الوطن، الرياض، 1426هـ. 4-صحيح مسلم؛ للإمام مسلم بن الحجاج، حققه ورقمه محمد فؤاد عبدالباقي، دار عالم الكتب-الرياض، الطبعة الأولى، 1417هـ. 5-مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح؛ تأليف ملا علي القاري، تحقيق صدقي العطار، دار الفكر-بيروت، الطبعة الأولى، 1412هـ. 6-نزهة المتقين شرح رياض الصالحين؛ تأليف د. مصطفى الخِن وغيره، مؤسسة الرسالة-بيروت، الطبعة الرابعة عشر، 1407هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

‌Ku karanta Alƙur’ani domin zai zo ranar alƙiyama yana mai ceton ma'abotansa

عن أبي أمامة الباهلي رضي الله عنه قال: سمعتُ رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «اقرؤوا القرآنَ فإنَّه يأتي يوم القيامة شَفِيعًا لأصحابه، اقرؤوا الزَّهرَاوَين البقرةَ وسورةَ آل عِمران، فإنهما تأتِيان يوم القيامة كأنهما غَمَامَتان، أو كأنهما غَيَايَتانِ، أو كأنهما فِرْقانِ من طَيْر صَوافٍّ، تُحاجَّان عن أصحابهما، اقرؤوا سورة البقرة، فإن أخذها بَرَكة، وتركها حَسْرة، ولا تستطيعها البَطَلَة».
Daga Abu Umamah al-Bahili - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa: «‌Ku karanta Alƙur’ani domin zai zo ranar alƙiyama yana mai ceton ma'abotansa, Ku karanta surori biyu Baƙara da al-Imran, domin cewa su za su zo a ranar alƙiyama kamar giza-gizai ko kamar wata tawagar tsuntsaye sun yi sahu, suna kare ma'abocinsu, ku karanta Surat al-Baƙara don haddace ta albarka ne, kuma barinta asara ne, kuma matsafa ba zasu iya ta ba».
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar akan dawwama kan karatun Alƙur'ani; domin shi (Alkur’ani) zai yi ceto a ranar alƙiyama ga masu karanta shi masu aiki da shi, sannan ya ƙarfafa karanta surori biyu: Baƙara da al-Imran, kuma ya ambace su da Zahrawani masu haske; saboda haskensu da kuma shiryarawarsu, kuma lallai ladan karanta su da tadabburin ma'anoninsu da kuma aiki da abinda ke cikinsu, zasu zo ranar alƙiyama kamar gizagizai biyu ko wasunsu, ko ka ce su garken tsntsaye ne waɗanda suka shinfiɗa fukafukansu sashinsu na saduwa da sashi, suna yi wa ma'abocinsu inuwa kuma suna kare shi. Sannan (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ƙarfafa dawwama a kan karanta Suratul Baƙara da tadabburin ma'anoninta da kuma aiki da abinda ke cikinsu, kuma hakan a cikinsa akwai albarka da amfani mai girma a duniya da lahira, kuma barin hakan a cikinsa akwai asara da nadama a ranar alƙiyama, kuma daga cikin falalar wannan surar matsafa ba zasu iya cutar da wanda ya karantata ba.

Fa’idoji
  1. Umarni da karanta alƙur'ani da kuma yawaita hakan, kuma shi (Alkur’ani) zai ceci ma'abotansa a ranar alƙiyama, masu karanta shi, masu riƙo da shiriyarsa, masu tsayawa kan abinda ya yi umarni da shi, masu barin abinda ya hana.
  2. Falalar karanta Suatul Baƙara da al-Imran da kuma girman ladansu.
  3. Falalar karanta Suratul Baƙara, kuma cewa ita tana kare ma'abocinta daga tsafi.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 553) (804). مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي القاري (4/ 1460). التنوير شرح الجامع الصغير، لمحمد الصنعاني (2/ 606). شرح الأربعين النووية، لابن عثيمين (ص232). معارج القبول بشرح سلم الوصول إلى علم الأصول، لحافظ الحكمي (2/ 846). التَّحبير لإيضَاح مَعَاني التَّيسير، لمحمد الصنعاني (2/ 9). تطريز رياض الصالحين، لفيصل المبارك (ص579).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Yakai baban Al-Munzir, shin ka san wacce aya ce daga littafin Allah mafi girma tare dakai?" ya ce: Na ce; {Allah wanda babu wani abin bautawa da gaskiya sai Shi Rayayye Tabbatacce da kanSa} [Al-Baqara: 255]. Ya ce: Sai ya daki kirjina, ya ce: "Wallahi ilimi ya faranta maka kai baban Al-Munzir

عَنْ ‌أُبَيِّ بْنِ كَعْبٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «يَا أَبَا الْمُنْذِرِ، أَتَدْرِي أَيُّ آيَةٍ مِنْ كِتَابِ اللهِ مَعَكَ أَعْظَمُ؟» قَالَ: قُلْتُ: اللهُ وَرَسُولُهُ أَعْلَمُ. قَالَ: «يَا أَبَا الْمُنْذِرِ، أَتَدْرِي أَيُّ آيَةٍ مِنْ كِتَابِ اللهِ مَعَكَ أَعْظَمُ؟» قَالَ: قُلْتُ: {اللهُ لا إِلَهَ إِلا هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ} [البقرة: 255]. قَالَ: فَضَرَبَ فِي صَدْرِي، وَقَالَ: «وَاللهِ لِيَهْنِكَ الْعِلْمُ، أَبَا الْمُنْذِرِ».
Daga Ubayyu Dan Ka'ab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ya kai baban Munzir, shin ka san wacce aya ce daga littafin Allah mafi girma tare da kai?" ya ce: Na ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani. Ya ce: "Yakai baban Al-Munzir, shin ka san wacce aya ce daga littafin Allah mafi girma tare dakai?" ya ce: Na ce; {Allah wanda babu wani abin bautawa da gaskiya sai Shi Rayayye Tabbatacce da kanSa} [Al-Baqara: 255]. Ya ce: Sai ya daki kirjina, ya ce: "Wallahi ilimi ya faranta maka kai baban Al-Munzir".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambayi Ubayyu Dan Ka'ab game da mafi girman aya a cikin littafin Allah, sai ya yi kai kawo a amsa, sannan ya ce: ita ce Ayatul Kursiyyi: {Allah babu wani abin bautawa da gaskiya sai Shi, Rayayye tabbatacce da kanSa}, sai Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya karfafashi, kuma Annabi ya daki kirjinsa dan nuni zuwa cikarsa da ilimi da hikima, kuma ya yi masa addu'a da ya tsira da wannan ilimin kuma ya sawwaka masa shi.

Fa’idoji
  1. Daraj mai girma ga Ubayyu Dan Ka'aba - Allah Ya yarda da shi -.
  2. Ayatul Kursiyyu ita ce mafi girman aya a cikin littafin Allah - Madaukakin sarki -, to haddace ta da tunanin ma'anoninta da aiki da su shi yake kamata.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 556) (810)، إكمال المعلم (3/178)، الكاشف عن حقائق السنن (5/1644)، المفهم (2/436)، البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (16/ 394).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
8 cikin 14
Hadisai 14
  1. Lallai cewa Annabi ya aika Wani Mutum a wani yaki sai ya kasane yana" karantawa abokansa in yana jansu Sallah, Sai yake cika karatunsa da: Kulhuwa.
  2. Ka yi albishir da haske biyu da aka ba ka su, wanda ba'a bawa wani Annabi kafinka ba; Ita ce Fatihatul Kitab, da ƙarshen suratul Baƙarah, ba za ka karanta wani harafi daga cikinsu ba sai an ba ka shi
  3. Kada ku mayar da gidajenku makabarta, Shaiɗan yana guduwa daga gidan da ake karanta Surat Al-Bakarah a cikinsa
  4. Wanda ya haddace ayoyi goma daga farkon Suratul Kahf, za'a tsare shi daga Dujal". A cikin wata riwayar: "Daga ƙarshen Suratul Kahf
  5. Wanda ya karanta ayoyi biyu na ƙarshen Suratul Bakara da daddare sun ishe shi
  6. Baka ga Wasu Ayoyi da aka saukar da su ba a wannan Daren ba'a tava ganinsu ba? Falaqi da Nasi
  7. ‌Ku karanta Alƙur’ani domin zai zo ranar alƙiyama yana mai ceton ma'abotansa
  8. Yakai baban Al-Munzir, shin ka san wacce aya ce daga littafin Allah mafi girma tare dakai?" ya ce: Na ce; {Allah wanda babu wani abin bautawa da gaskiya sai Shi Rayayye Tabbatacce da kanSa} [Al-Baqara: 255]. Ya ce: Sai ya daki kirjina, ya ce: "Wallahi ilimi ya faranta maka kai baban Al-Munzir
  9. Lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya zo wa shinfidarsa kowanne dare yana taro tafikansa, sannan ya yi tofi a cikin su, sai ya karanta a cikinsu: {Ka ce Shi ne Allah Shi kadi }, da {Ka ce ina neman tsari da Ubangijin safiya}, da {Ka ce ina neman tsari da Ubangijin mutane} (Kul huwa da Falaki da kuma Nasi)
  10. Allah - maɗaukakin sarki Ya ce: Na raba sallah tsakanina da tsakanin bawaNa gida biyu, bawaNa yana da abin da ya roƙa
  11. Na rantse da wanda raina yake hannunSa, lallai cewa ita ta yi daidai da ɗaya bisa uku na Alƙur'ani
  12. a'a ku ce: Mun ji mun bi, muna neman gafarKa ya Ubangijinmu makoma tana wurinKa
  13. Wata aya a cikin littafinku kuna karantata, da a ce agurinmu mu Yahudawa ta sauka da mun riƙi ranar idi
  14. An saukar min da wasu ayoyi (waɗanda) ba'a taɓa ganin kwatankwacinsu ba ko sau ɗaya, Falaƙi da Nasi

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com