Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Na rantse da wanda raina yake hannunSa, lallai cewa ita ta yi daidai da ɗaya bisa uku na Alƙur'ani

عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الخُدْرِيِّ رَضيَ اللهُ عنهُ: أَنَّ رَجُلًا سَمِعَ رَجُلًا يَقْرَأُ: {قُلْ هُوَ اللَّهُ أَحَدٌ} يُرَدِّدُهَا، فَلَمَّا أَصْبَحَ جَاءَ إِلَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَذَكَرَ ذَلِكَ لَهُ، وَكَأَنَّ الرَّجُلَ يَتَقَالُّهَا، فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «وَالَّذِي نَفْسِي بِيَدِهِ إِنَّهَا لَتَعْدِلُ ثُلُثَ القُرْآنِ».
Daga Abu Sa'id al-Kudri - Allah Ya yarda da shi -: Cewa wani mutum ya ji wani mutum yana karanta: {Ka ce Shi ne Allah Shi kaɗai}, yana maimaita ta, lokacin da ya wayi gari sai ya zo wurin manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya fada masa hakan, kai ka ce mutumin yana ganin ƙanƙantarta, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Na rantse da wanda raina yake hannunSa, lallai cewa ita ta yi daidai da ɗaya bisa uku na Alƙur'ani".
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Abu Sa'id al-Khudr - Allah Ya yarda da shi - ya fadi cewa wani mutum ya ji wani mutumin daban yana karanta Suratu (Ikhlas): {Ka ce Shi ne Allah Shi kaɗai} yana maimaitata a kowanne dare ba ya ƙari akanta, lokacin da ya wayi gari sai ya zo gurin manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ambata masa haka, kamar shi mai maganar yana ganin cewa ta yi kaɗan, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi rantsuwa akan ma'anar ƙarfafawa: Na rantse da wanda raina yake a hannunSa lallai cewa ita (Surar) ta yi daidai da ɗaya bisa uku na Alƙur'ani.

Fa’idoji
  1. Falalar Suratul Ikhlas, kuma ita tana daidai da ɗaya bisa uku na Alƙur'ani.
  2. Halaccin karatu a sallar tsayuwar dare koda da ayoyi kaɗan ne da kuma maimaita su, da rashin ƙaranta hakan.
  3. AlMaziri ya ce: An ce: Ma'anarsa: Cewa Alƙur'ani yana da ɓangarori uku; Kissoshi da hukunce-hukunce da kuma siffofin Allah - Maɗaukakin sarki -, {Ka ce Shi ne Allah Makaɗaici} mai tacewa ce - yana nufin ga siffofin Allah -, dan haka ita ce ɗaya bisa uku, kuma wani yanki daga cikin yankuna uku. Kum an ce: Ma'narsa: Cewa ladan karantata ana ninka shi da gwargwadan ladan karatun ɗaya bisa uku na Alƙur'ani ba tare da ninkawa ba.
Madogara

صحيح البخاري (6/ 189) (5013). إرشاد الساري لشرح صحيح البخاري (7/ 463).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALOLI NA SURORI DA AYOYI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com