Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Wanda ya karanta ayoyi biyu na ƙarshen Suratul Bakara da daddare sun ishe shi

عن أبي مسعود رضي الله عنه قال: قال النبي صلى الله عليه وسلم: «مَنْ قَرَأَ بِالْآيَتَيْنِ مِنْ آخِرِ سُورَةِ الْبَقَرَةِ فِي لَيْلَةٍ كَفَتَاهُ».
Daga Abu Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Wanda ya karanta ayoyi biyu na ƙarshen Suratul Bakara da daddare sun ishe shi.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ba da bayanin duk wanda ya karanta ayoyi biyun ƙarshe na Suratul Baƙara cikin dare, to, Allah zai tsare shi daga sharri da abin ƙi, wasu kuma suka ce: Sun ishe shi nafilar dare, wasu kuma suka ce: Sun ishe shi addu’oin dare. An ce kuma: su ne mafi ƙarancin abin da zai isa na karatun Alkur’ani a nafilar dare, an ma faɗi wanin haka, kuma muna fatan duk abin da aka faɗa ɗin daidai ne, domin zai ƙunshe su duka

Fa’idoji
  1. Bayanin falalar [ayoyin] ƙarshen Baƙara, su ne daga faɗin Allah: (( Manzon ya yi imani….. har zuwa ƙarshen Surah.
  2. Ƙarshen Suratul Baƙara yana tunkuɗewa wanda ya karanta mugun abu da sharri da shaiɗanu, idan ya karanta su da daddare.
  3. Dare yana farawa ne daga faɗuwar rana, yana kuma ƙarewa ne da hudowar alfijir.
Madogara

صحيح البخاري (6/ 188) (5008-5009). صحيح مسلم (1/ 554) (807). فتح الباري بشرح صحيح البخاري، لابن حجر (9/ 56). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 240). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص593). مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لملا علي القاري (4/ 1465). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمصطفى الخِن وغيره (2/ 757).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALOLI NA SURORI DA AYOYI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com