Kada ku mayar da gidajenku makabarta, Shaiɗan yana guduwa daga gidan da ake karanta Surat Al-Bakarah a cikinsa
عن أبي هريرة رضي الله عنه: أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «لَا تَجْعَلُوا بُيُوتَكُمْ مَقَابِرَ، إِنَّ الشَّيْطَانَ يَنْفِرُ مِنَ الْبَيْتِ الَّذِي تُقْرَأُ فِيهِ سُورَةُ الْبَقَرَةِ».
Daga Abu Hurairah Allah Ya yarda da shi, Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Kada ku mayar da gidajenku makabarta, Shaiɗan yana guduwa daga gidan da ake karanta Surat Al-Bakarah a cikinsa".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana yin hani daga wofintar da gidaje daga sallah, sai su zama kamar maƙabartu, da ba a sallah a cikinsu.
Sannan sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ba da labarin shaiɗan yana ficewa daga gidan da ake karanta Suratul Baƙara.
Fa’idoji
Ana so a yawaita ibada da Sallolin Nafila a gidaje.
Ba ya halatta yin Sallah a maƙabarta, domin hakan hanya ce daga hanyoyin shirka da wuce iyaka ga masu su, in banda sallar Janaza.
Hanin yin Sallah a inda akwai kabari, ya tabbata a wurin Sahabbai, saboda haka Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana a sanya gidaje kamar maƙabartu, waɗanda su ba a Sallah a cikinsu.
Madogara
صحيح مسلم (1/ 539) (780).
بهجة الناظرين، لسليم الهلالي (2/ 240).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (4/ 682).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمصطفى الخِن وغيره (2/ 757).
مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي القاري (4/ 1460).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com