Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

DA'AWA ZUWA GA ALLAH

Hadisai 24

ku rika zantar da Mutane da abinda suka sani, ko kuna son su karyata Allah da manzonsa ne

عن علي بن أبي طالب رضي الله عنه قال: "حدثوا الناس بما يعرفون، أتريدون أن يُكذَّب اللهُ ورسولهُ؟".
Daga Aliyu Dan Abi talib -Allah ya yarda da shi ya ce: "Ku rika zantar da Mutane da abinda suka sani ko kuna son su karyata Allah da Manzonsa ne ?
Buhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Shugaban Muminai Aliyu Dan Abi Dalib - Allah ya yarda da shi - Izuwa cea bai dace ba a gayaa Mutane Marasa Ilimi sai da abinda suka saba ji kuma anda zai amfanar da su a cikin abinda yake na asalin Addininsu da Hukunce Hukuncensa na Tauhidi da bayanin Halal da Haram da kuma barin dukkan abun da ai shagaltar da su daga abubuwan da basa bukatarsu ko kuma abunda zai kai su zua kin karbar gaskiya da watsi da ita sabida rikitar da su da abinda yayi, kuma yayi musu wahalar fahimtar sa

Madogara

كتاب التوحيد للإمام محمد بن عبد الوهاب، ت: د. دغش العجمي، مكتبة أهل الأثر, الطبعة الخامسة, 1435ه. الجديد في شرح كتاب التوحيد، لمحمد بن عبد العزيز السليمان القرعاوي, ت: محمد بن أحمد سيد, مكتبة السوادي، الطبعة: الخامسة، 1424ه. الملخص في شرح كتاب التوحيد، للشيخ صالح الفوزان, دار العاصمة, الطبعة الأولى، 1422ه. صحيح البخاري, ترقيم محمد فؤاد عبد الباقي, دار طوق النجاة, الطبعة: الأولى، 1422هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ya kai baffana, ka ce : Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kalma ce wacce zan kafa maka hujja da ita awurin Allah

عن سَعِيدِ بْنِ الْمُسَيَّبِ، عَنْ أَبِيهِ قَالَ: لَمَّا حَضَرَتْ أَبَا طَالِبٍ الْوَفَاةُ، جَاءَهُ رَسُولُ اللهِ صلى الله عليه وسلم فَوَجَدَ عِنْدَهُ أَبَا جَهْلٍ وَعَبْدَ اللهِ بْنَ أَبِي أُمَيَّةَ بْنِ الْمُغِيرَةِ، فَقَالَ: «أَيْ عَمِّ، قُلْ: لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، كَلِمَةً أُحَاجُّ لَكَ بِهَا عِنْدَ اللهِ»، فَقَالَ أَبُو جَهْلٍ وَعَبْدُ اللهِ بْنُ أَبِي أُمَيَّةَ: أَتَرْغَبُ عَنْ مِلَّةِ عَبْدِ الْمُطَّلِبِ، فَلَمْ يَزَلْ رَسُولُ اللهِ صلى الله عليه وسلم يَعْرِضُهَا عَلَيْهِ، وَيُعِيدَانِهِ بِتِلْكَ الْمَقَالَةِ، حَتَّى قَالَ أَبُو طَالِبٍ آخِرَ مَا كَلَّمَهُمْ: عَلَى مِلَّةِ عَبْدِ الْمُطَّلِبِ، وَأَبَى أَنْ يَقُولَ: لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صلى الله عليه وسلم: «وَاللهِ لَأَسْتَغْفِرَنَّ لَكَ مَا لَمْ أُنْهَ عَنْكَ»، فَأَنْزَلَ اللهُ: {مَا كَانَ لِلنَّبِيِّ وَالَّذِينَ آمَنُوا أَنْ يَسْتَغْفِرُوا لِلْمُشْرِكِينَ} [التوبة: 113]، وَأَنْزَلَ اللهُ فِي أَبِي طَالِبٍ، فَقَالَ لِرَسُولِ اللهِ صلى الله عليه وسلم: {إِنَّكَ لا تَهْدِي مَنْ أَحْبَبْتَ وَلَكِنَّ اللهَ يَهْدِي مَنْ يَشَاءُ} [القصص: 56].
Daga Sa'id Dan Musayyib daga babansa ya ce: Lokacin da mutuwa ta zo wa Abu Dalib, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo masa sai ya samu Abu jahal da Abdullahi Dan Abu Umayyah Dan Mugira a wurrinsa, sai ya ce: "Ya kai baffana, ka ce : Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kalma ce wacce zan kafa maka hujja da ita awurin Allah", sai Abu jahal da Abdullahi dan Abu Umayyah suka ce : Kana kin tafarkin Abdul Muddalib, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai gushe ba yana bijiro masa da ita, suma suna maimaita masa waccan maganar, har Abu Dalib ya ce karshen abinda ya fada musu: Akan tafarkin Abdul Muddalib ya ki fadar: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wallahi zan nemamaka gafara muddin ba'a hanani ba". Sai Allah yaYa saukar da: {Bai kasance ga Annabi ba da wadanda suka yi imani da su nema wa mushrikai gafara ba} [Al-Taubah: 113], kuma Alllah Ya saukar asha'anin Abu Dalib, sai Ya cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: {Lallai kai ba zaka shiryar da wanda kake so ba sai dai Allah Yana shiryar da wanda Ya so} [Al-Kasas: 56].
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiga wurin baffansa Abu Dalib alhali shi yana kan gargara, sai ya ce masa: Ya baffana, ka ce : "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, wata kalmace da zan yi maka shaida da ita a wurin Allah, sai Abu Jahal da Abdullahi Dan Abu Umayya suka ce: Ya Abu Dalib, zaka bar tafarkin babanka Abdul Muddalib?! Shi ne bautar gumaka, basu gushe ba suna yi masa magana har ya fadi karshen wani abinda ya zantar da su da shi: Akan tafarkin Abdul Muddalib, tafarkin shirka da bautar gumaka, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Zan roka maka gafara muddin Ubangijina bai hanani hakan ba, sai fadin Allah - Madaukakin sarki - ya sauka: {Bã ya kasancẽwa ga Annabi da waɗanda suka yi ĩmãni, su yi istigifãri ga mushirikai, kuma kõ dã sun kasance ma'abũta zumunta ne daga bãyan sun bayyana a gare su, cẽwa lalle ne, sũ, 'yan Jahĩm ne} [Al-Taubah: 113], kuma fadin Allah - Madaukakin sarki - ya sauka a sha'anin Abu Dalib: {Lalle ne kai bã ka shiryar da wanda ka so, amma kuma Allah Yanã shiryar da wanda Yake so, kuma Shi ne Mafi sani daga mãsu shiryuwa} [Al-kasas: 56], lallai cewa kai ba ka shiryar da wanda ka so shiriyarsa, kawai kai isarwa ce taka, Allah Yana shiryar da wanda yake so.

Fa’idoji
  1. Haramcin nemawa mushrikai gafara, duk yadda kusancinsu ya kasance da ayyukan su da kyautatawarsu.
  2. Koyi da iyaye da manya akan shirka yana daga aikin 'yan Jahiliyya.
  3. Cikar tausayin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kwadayinsa akan kiran mutane da shiriyarsu.
  4. Raddi ga wanda ya yi da'awar musuluntar Abu Dalib.
  5. Ayyuka da cikawa ne.
  6. Bacin rataya ga Annabi - tsira da aminci su tabbata agare shi - da waninsa dan jawo amfani ko tunkude cuta.
  7. Wanda ya ce: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah" akan ilimi da yakini da kudircewa ya shiga Musulunci.
  8. Cutarwar munanan mutane da abokanan sharri ga mutum.
  9. Ma'anar "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah": Barin bautar gumaka da waliyyai da mutanen kirki, da kadaita Allah da bauta, kuma cewa mushrikai suna sanin ma'anarta.
  10. Halaccin gaishe da mara lafiya mushriki idan ana kwadayin musuluntarsa.
  11. Shiriya ta gamda -katar tana hannun Allah ne Shi kadai ba Shi da abokin tarayya, kawai shiriya ta nuni da shiryarwa da isarwa tana ga Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Madogara

صحيح البخاري (6/ 112) (4772). صحيح مسلم (1/ 54) (24). الملخص في شرح كتاب التوحيد، لصالح الفوزان (ص155). الجديد في شرح كتاب التوحيد، للقرعاوي (ص169).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ni ne Dimam dan Sa'alabata dan uwan Banu Sa'ad dan Bakar

عن أَنَسَ بْنَ مَالِكٍ رضي الله عنه قال: بينما نحن جلوس مع النبي صلى الله عليه وسلم في المسجد دخل رجل على جمل، فأناخه في المسجد ثم عقله، ثم قال لهم: أيكم محمد؟ والنبي صلى الله عليه وسلم متكئ بين ظهرانيهم، فقلنا: هذا الرجل الأبيض المتكئ. فقال له الرجل: يا ابن عبد المطلب فقال له النبي صلى الله عليه وسلم: «قد أجبتك». فقال الرجل للنبي صلى الله عليه وسلم: إني سائلك فمشدد عليك في المسألة، فلا تجد علي في نفسك؟ فقال: «سل عما بدا لك» فقال: أسألك بربك ورب من قبلك، آلله أرسلك إلى الناس كلهم؟ فقال: «اللهم نعم». قال: أنشدك بالله، آلله أمرك أن نصلي الصلوات الخمس في اليوم والليلة؟ قال: «اللهم نعم». قال: أنشدك بالله، آلله أمرك أن نصوم هذا الشهر من السنة؟ قال: «اللهم نعم». قال: أنشدك بالله، آلله أمرك أن تأخذ هذه الصدقة من أغنيائنا فتقسمها على فقرائنا؟ فقال النبي صلى الله عليه وسلم: «اللهم نعم». فقال الرجل: آمنت بما جئت به، وأنا رسول من ورائي من قومي، وأنا ضمام بن ثعلبة أخو بني سعد بن بكر.
Daga Anas Ibnu Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Muna zaune tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin masallaci sai wani mutum ya shigo akan wani rakumi, sai ya dirkusar da shi a cikin masallaci sannan ya daure shi, sannan ya ce da su: Waye Muhammad a cikinku? alhali Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kishingide a tsakaninsu, sai muka ce : Wannan farin mutumin wanda ke kishingide. Sai mutumin ya ce da shi: Ya kai Dan Abdul Mudallib sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce da shi: "Hakika na amsa maka". Sai mutumin ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ni mai tambayarka ne mai tsananta maka a tambaya, kada ka ji haushi na a ranka? sai ya ce: "Ka tambayi abinda ya bayyana gareka" sai ya ce: Ina tambayarka dan Ubangijinka da Ubangijin wadanda suka gabaceka, shin Allah ne Ya aikoka zuwa ga mutane gaba dayansu? sai ya ce: "Eh ya Allah". Ya ce: Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da mu yi salloli biayr a yini da dare? ya ce: "Eh ya Allah ne.” ya ce Ina maka magiya da Allah shin Allah ne Ya umarceka da mu yi azumin wannan watan a shekara? ya ce: "Eh ya Allah". Ya ce; Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da ka karbi wannan sadakar daga mawadatanmu sai ka rabata ga talakawan mu? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Eh ya Allah". sai mutumin ya ce; na yi imani da abinda ka zo da shi, kuma ni manzo ne na wadanda ke bayana cikin mutane na, Ni ne Dimam dan Sa'alabata dan uwan Banu Sa'ad dan Bakar.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Anas dan Malik - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa: Lokacin da sahabbai suna zaune tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin masallaci yayin da wani mutum ya shigo akan wani rakumi, sai ya durkusar da rakumin sannan ya daure shi. Sannan ya tambayesu: Waye Muhammd a cikinku? Alhali Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kishingide tsakanin mutanen, sai muka ce : Wannan farin mutumin. Sai mutumin ya ce da shi: Yakai Dan Abdul Muddalib. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce da shi: Na ji ka yi tambaya in amsa maka. Sai mutumin ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ni mai tambayarka ne kuma mai tsananta maka a tambaya, kada ka ji wani abu game dani a ranka. Wato: Kada ka yi fushi da ni kuma kada kunci ya sameka. Sai ya ce: Ka tambayi abinda kake so. Sai ya ce: Ina ina hada ka da Ubangijinka kuma Ubangijin wadanda suka gabace ka, shin Allah ne Ya aikoka zuwa ga mutane? Sai ya ce: Eh ya Allah, dan karfafa gaskiyarsa. Sai Mutumin ya ce: Ina yi maka magiya da Allah, wato; Ina tambayarka sabo da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da ka yi salloli biyar a yini da dare? Su ne salloli wadanda aka faralanta ?., Ya ce: Eh ya Allah, Ya ce: Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da mu azimci wannan watan daga shekara? wato: Watan Ramadan, Ya ce: Eh ya Allah, Ya ce: Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka daka karbi wannan sadakar daga mawadatanmu sai ka rabata ga talakawanmu? ita ce zakka. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Eh ya Allah, Sai Dimam ya musulunta, kuma ya ba Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - labarin cewa shi zai kira mutanensa zuwa Musulunci. Sannan ya yi bayanin kansa cewa shi ne Dimam dan Sa'alabata daga Banu Sa'ad Ibnu Bakar.

Fa’idoji
  1. Tawali'un Annabi - tsira da aminci su tabbata agare shi -; dan mutum ba zai iya banbancewa ya raba tsakaninsa da sahabbansa ba.
  2. Kyakkyawar dabi'un Annabi - aminci ya tabbata agare shi -, da tausasawarsa a bada amsa ga mai tambaya, kuma cewa kyakkyawar bada amsa tana daga sabubban karbar Da’awah.
  3. Halaccin bayanin mutum da wata siffa na fari da ja, da tsawo da gajarta, da makamancin wannan daga abinda ba'a nufin aibatawa da shi, idan ba ya kin hakan.
  4. Halaccin shigar kafiri masallaci dan bukata.
  5. Bai ambaci Hjji ba a cikin hadisin domin cewa shi zai iya kasancewa ba'a wajabta Hajjin ba a lokacin zuwansa ba.
  6. Kwadayin sahabbai akan kiran mutane; daga musuluntarsa ya yi kwadayin kiran mutanensa.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 23) (63)، صحيح مسلم (1/ 41) (12)، شرح ابن بطال (1/145)، عمدة القاري شرح صحيح البخاري (2/ 22).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com