عن عبد الله بن عبَّاس رضي الله عنهما قال: «أُمِرَ الناس أن يكون آخر عَهْدِهِمْ بالبيت، إلا أنه خُفِّفَ عن المرأة الحائض».
Daga Abdullahi Dan Abbas -Allah ya yarda da su- yace: "An umarci mutane dasu yi dawafi ga dakin Allah a karshe,sai dai anyi sauki ga mace mai haila".
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Dakin Ka'aba yana da daraja da daukaka,kuma shi wata alama ce ta bautar Allah da kankan da kai da tsoron Allah,kuma yana da kwarjini a zukatan mutane,rayuka sun damfaru da shi,suna son shi.Don haka Annabi ya umarci mahajjaci daya sanya dawafi ga dakin Allah abu na karshe,ya zama ban kwana,sai dai anyi sauki ga mace mai haila don gudun kar ta bata masallacin.wannan kuma ya shafi Hajji ne kawai banda Umra.Duba littafin Taisiril Allam,Tanbihul Afham,Ta'asisil Ahkam.
Madogara
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، عبد الله بن عبد الرحمن البسام، تحقيق: محمد صبحي حلاق، مكتبة الصحابة، الأمارات، مكتبة التابعين، القاهرة، الطبعة: العاشرة 1426هـ.
تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، محمد بن صالح العثيمين، مكتبة الصحابة، الإمارات، الطبعة: الأولى 1426هـ.
الإفهام في شرح عمدة الأحكام لابن باز، تحقيق: سعيد القحطاني، مؤسسة عبد العزيز بن باز الخيرية، الرياض، الطبعة: الأولى 1435هـ.
خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام، فيصل بن عبد العزيز المبارك، الطبعة: الثانية 1412هـ، 1992م.
صحيح البخاري، محمد بن إسماعيل البخاري الجعفي، تحقيق: محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى 1422هـ.
صحيح مسلم، مسلم بن الحجاج القشيري النيسابوري، تحقيق محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، الطبعة: 1423هـ.
تأسيس الأحكام، أحمد بن يحيى النجمي، دار المنهاج، القاهرة، الطبعة: الأولى.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي موسى الأشعري رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «إِذَا مَرِضَ الْعَبْدُ أَوْ سَافَرَ كُتِبَ لَهُ مِثْلُ مَا كَانَ يَعْمَلُ مُقِيمًا صَحِيحًا».
Daga Abu Musa Al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan bawa yayi rashin lafiya ko yayi tafiya za'a rubuta masa tamkar abinda ya kasance yana aikatawa alhali yana zaman gida kuma lafiyayye".
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bada labari game da falalar Allah da rahamarSa, kuma cewa musulmi idan ya kasance al'adarsa cewa yana aikata wani aiki na gari a halin lafiyarsa da kuma zaman gidansa, sannan wani uzuri ya faru da shi sai ya yi rashin lafiya bai samu damar yin sa ba, ko ya shagalta da tafiya bai samu ya yi shi ba, ko wani uzurin; to cewa shi za'a rubuta masa lada cikakke, kamar da ya aikata shi a halin lafiya da zaman gida.
Fa’idoji
- Yalwal falalar Allah ga bayinSa.
- Kwadaitarwa akan kokari a biyayya da cin ribar lokuta a halin lafiya da faraga.
Madogara
صحيح البخاري (4/ 57) (2996).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (1/ 36).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 211).
بهجة قلوب الأبرار وقرة عيون الأخيار في شرح جوامع الأخبار، لعبد الرحمن السعدي (ص83).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أُبَيِّ بْنِ كَعْبٍ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: كَانَ رَجُلٌ لَا أَعْلَمُ رَجُلًا أَبْعَدَ مِنَ الْمَسْجِدِ مِنْهُ، وَكَانَ لَا تُخْطِئُهُ صَلَاةٌ، قَالَ: فَقِيلَ لَهُ: أَوْ قُلْتُ لَهُ: لَوْ اشْتَرَيْتَ حِمَارًا تَرْكَبُهُ فِي الظَّلْمَاءِ، وَفِي الرَّمْضَاءِ، قَالَ: مَا يَسُرُّنِي أَنَّ مَنْزِلِي إِلَى جَنْبِ الْمَسْجِدِ، إِنِّي أُرِيدُ أَنْ يُكْتَبَ لِي مَمْشَايَ إِلَى الْمَسْجِدِ، وَرُجُوعِي إِذَا رَجَعْتُ إِلَى أَهْلِي، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «قَدْ جَمَعَ اللهُ لَكَ ذَلِكَ كُلَّهُ».
Daga Ubayyu ɗan Ka'ab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani mutum ya kasance nesa da masallaci sama da kowa a iya sanina, kuma ya kasance ba wata sallah da take wuce shi, ya ce: Sai aka ce masa: Ko nace masa: Ai da za ka sayi jakin da zaka dinga hawan shi cikin duhu, da zafin rana, sai ya ce; Ba na son gidana ya kasance a gefen masallaci, lallai ni ina son a rubuta mini tafiya ta zuwa masallaci, da dawowa ta idan na dawo zuwa iyalaina, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: «Haƙiƙa Allah Ya haɗa maka wadannan gaba ɗayan su».
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Ubayyu ɗan Ka'ab - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa wani mutum daga cikin mutanen Madina yana daga cikin mafi nisan gida daga masallacin Annabi, kuma ya kasance sallah bata wuce shi; kai yana halattar kowace sallah tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai aka ce masa: Inama dai a ce zaka sayi jakin da zaka dinga hawansa a cikin duhun dare da kuma cikin zafin ƙasa a cikin rana, ya ce: Bana son a ce gidana yana gefen masallaci, lallai ni ina son Allah Ya rubuta mini tafiyata zuwa masallaci, da kuma dawowata idan na dawo zuwa ga iyalaina, sai maganarsa ta kai wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: «Haƙiƙa Allah Ya haɗa maka hakan baki ɗayansu».
Fa’idoji
- Tsananin kwaɗayin sahabbai akan alheri da neman ƙaruwar shi da kuma neman lada.
- Nawawi ya ce: A cikinsa akwai tabbatar da lada a cikin takun dawowa daga sallah kamar yadda yake tabbata a tafiya.
- Musulmi su yi wa junansu wasiyya da alheri da kuma nasiha da aikin alheri, wanda ya ga cewa ɗan'uwansa wata wahala tana riskarsa to ya gabatar masa da nasiha a gusar da ita.
- Nisan gida daga masallaci ba uzuri ba ne a kan barin jam’i, muddin dai yana jin kiran sallah.
Madogara
صحيح مسلم (1/ 460) (663).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 162).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 199).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «إذا قَام أحَدُكُم من الليل، فَاسْتَعْجَمَ القرآن على لِسَانه، فلم يَدْرِ ما يقول، فَلْيَضْطَجِع».
Daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - wanda ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan dayanku ya tashi da daddare, Alkur'ani ya kasa hakuri a kan harshensa, kuma bai san abin da zai fada ba, don haka ya yi karya."
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Ma'anar hadisin: Idan bawa yana cikin sallar dare, to yana da wahala ya karanta Alkur'ani. Saboda bacci mai nauyi ne da bai san me zai ce ba, sai a barshi ya kwanta, har sai ya yi bacci. Don kar ya canza kalmomin Allah ya canza ta, kuma wataƙila zai kawo abin da bai halatta ba, daga juya ma'anarsa, gurɓata kalmominsa, kuma wataƙila yin addu'a a kan kansa. Kuma a cikin Bukhari daga Anas - Allah Ya yarda da shi - da isnadi: If Idan] ayanku zai yi barci a cikin sallah, to ya yi bacci har sai ya san abin da yake karantawa. ”
Madogara
- رياض الصالحين من كلام سيد المرسلين؛ للإمام أبي زكريا النووي، تحقيق د. ماهر الفحل، دار ابن كثير - دمشق، الطبعة الأولى، 1428ه.
- بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين؛ تأليف سليم الهلالي، دار ابن الجوزي- الطبعة الأولى 1418ه.
- نزهة المتقين شرح رياض الصالحين؛ تأليف د. مصطفى الخِن وغيره، مؤسسة الرسالة-بيروت، الطبعة الرابعة عشر، 1407هـ.
- صحيح مسلم؛ للإمام مسلم بن الحجاج، حققه ورقمه محمد فؤاد عبد الباقي، دار عالم الكتب-الرياض، الطبعة الأولى، 1417هـ.
- كنوز رياض الصالحين، لحمد بن ناصر العمار، دار كنوز إشبيليا- الطبعة الأولى 1430ه.
- إِكمَالُ المُعْلِمِ بفَوَائِدِ مُسْلِم، لعياض بن موسى اليحصبي السبتي أبو الفضل - المحقق: الدكتور يحْيَى إِسْمَاعِيل - دار الوفاء للطباعة والنشر والتوزيع، مصر- الطبعة: الأولى، 1419 هـ - 1998 م.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «كُلُّ سُلاَمَى مِنَ النَّاسِ عَلَيْهِ صَدَقَةٌ، كُلَّ يَوْمٍ تَطْلُعُ فِيهِ الشَّمْسُ يَعْدِلُ بَيْنَ الِاثْنَيْنِ صَدَقَةٌ، وَيُعِينُ الرَّجُلَ عَلَى دَابَّتِهِ فَيَحْمِلُ عَلَيْهَا أَوْ يَرْفَعُ عَلَيْهَا مَتَاعَهُ صَدَقَةٌ، وَالكَلِمَةُ الطَّيِّبَةُ صَدَقَةٌ، وَكُلُّ خُطْوَةٍ يَخْطُوهَا إِلَى الصَّلاَةِ صَدَقَةٌ، وَيُمِيطُ الأَذَى عَنِ الطَّرِيقِ صَدَقَةٌ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kowacce gaɓa daga (jikin) mutane akwai sadaka a kanta, kowanne yinin da rana ta fito a cikin sa da (mutum) zai daidaita tsakanin mutune biyu sadaka ne, kuma ya taimaki mutum game da dabbar sa; sai ya ɗora shi a kanta, ko ya ɗauke masa kayan sa a kanta, to, sadaka ne, kuma kalma mai daɗi sadaka ce, kuma kowanne taku da zai yi zuwa sallah sadaka ne, kuma ya kau da ƙazanta daga hanya sadaka ne".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa akwai sadaka ta ɗawwu'i saboda Allah - Maɗaukakin sarki - akan kowanne musulmi mukallafi a kowacce rana a kan kowacce gaba daga cikin gabban jikinsa, sadaka ta Nafila ga Allah madaukakin sarki akan tafarkin godiya gare Shi akan lafiya, kuma sanya ƙasusuwansa gaɓɓai zai samu dama da suna damƙa da shinfiɗawa. kuma cewa wannan sadakar tana kaiwa ga ayyukan alheri gabaɗayanta bata tsayuwa akan bada wata dukiya, Daga ciki: Daidaitawarka da yin sulhunka tsakanin masu husuma sadaka ne. A taimakonka ga wani gajiyayye a dabbarsa (abin hawa) sai ka ɗora shi akanta, ko ka ɗauke masa kayansa sadaka ne. Kalma mai daɗi ta zikiri ce da addu'a da sallama da wasunsu sadaka ce. Kowanne takin da ka yi tafiya da shi zuwa sallah sadaka ne, kawar da abinda ake cutuwa da shi a hanya sadaka ne.
Fa’idoji
- Tsarin ƙasusuwan ɗan Adam da lafiyarsu yana daga mafi girman ni'imomin Allah - Maɗaukakin sarki - ga mutum, to kowanne ƙashi daga cikinsu yana buƙatuwa zuwa ga sadaka daga gare shi a karankansa dan godiyar wancan ni'imar ta cika.
- Kwaɗaitarwa akan jaddada godiya a kowacce rana dan dawwaamar da waɗancan ni'imomin.
- Kwaɗaitarwa a kan dawwama da nafilifili da sadakoki Kowacce rana.
- Falalar yin sulhu tsakanin mutane.
- Zaburarwa akan taimakon mutum ga ɗan'uwansa; domin taimakonsa gare shi sadaka ne.
- Zaburarwa akan halartar sallar jam'i da tafiya zuwa gareta, da raya masallatai da hakan.
- Wajabcin girmama hanyoyin musulmai ta hanyar nisantar da abinda zai kware su ko ya cutar da su.
Madogara
صحيح البخاري (4/ 56) (2989).
صحيح مسلم (1/ 498) (720).
-التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثًا النووية، مطبعة دار نشر الثقافة، الإسكندرية، الطبعة: الأولى، 1380 هـ.
-شرح الأربعين النووية، للشيخ ابن عثيمين، دار الثريا للنشر.
-فتح القوي المتين في شرح الأربعين وتتمة الخمسين، دار ابن القيم، الدمام المملكة العربية السعودية، الطبعة: الأولى، 1424هـ/2003م.
-الفوائد المستنبطة من الأربعين النووية، للشيخ عبد الرحمن البراك، دار التوحيد للنشر، الرياض.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن عائشة رضي الله عنها مرفوعاً: «إذا نَعَسَ أحدكم وهو يصلي فَلْيَرْقُدْ حتى يذهب عنه النوم، فإن أحدكم إذا صلى وهو نَاعِسٌ لا يدري لعله يذهب يستغفر فَيَسُبُّ نَفْسَهُ».
An rawaito daga Nana Aisha -Allah ya yarda da ita- daga Annabi: "Idan dayanku yayi gyagyadi a cikin Sallah to ya kwanta har sai baccin ya tafi, saboda dayanku idan yayi Sallah yana gyangyadi bai san watakila yaje yana neman Istigfari sai ya zagi kansa (Maimakon haka)"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Abunda Hadisin yake nunawa kin wahalar da kai a Ibada sai mai Sallah yaji da Alamar rinjayar Bacci kuma shi yana Sallah sai ya yanke sallarsa ko ya cika ta sannan ya kwanta ya hutar da kansa, har don kada wani abu ya same shi na rashin dadi Addu'a halin gajiyarsa
Madogara
صحيح البخاري, تأليف: محمد بن إسماعيل البخاري, تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر, دار طوق النجاة ترقيم محمد فؤاد عبدالباقي, ط 1422.
صحيح مسلم ،تأليف: مسلم بن الحجاج النيسابوري, تحقيق: محمد فؤاد عبدالباقي, دار إحياء التراث العربي.
مقاييس اللغة, تأليف: أحمد بن فارس الرازي, المحقق: عبدالسلام محمد هارون, الناشر: دار الفكر, عام 1399
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين, تأليف: سليم بن عيد الهلالي, دار ابن الجوزي،الطبعة الأولى1418.
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين, تأليف: مصطفى الخن ومصطفى البغا ومحي الدين مستو وعلي الشربجي ومحمد لطفي, مؤسسة الرسالة, ط 14 عام 1407 - 1987.
دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين؛ لمحمد بن علان الشافعي، تحقيق خليل مأمون شيحا-دار المعرفة-بيروت-الطبعة الرابعة1425ه.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِنَّ الدِّينَ يُسْرٌ، وَلَنْ يُشَادَّ الدِّينَ أَحَدٌ إِلَّا غَلَبَهُ، فَسَدِّدُوا وَقَارِبُوا، وَأَبْشِرُوا، وَاسْتَعِينُوا بِالْغَدْوَةِ وَالرَّوْحَةِ وَشَيْءٍ مِنَ الدُّلْجَةِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai Addini mai sauƙi ne, babu wanda zai tsananta cikinsa face sai ya rinjaye shi, saboda haka ku daidaita ku kusanto, ku yi bushara, ku nemi taimakon Allah da jijjifi da kuma yammaci da wani abu na duhun dare".
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa Addinin Musulunci an gina shi akan sauƙaƙawa da sauƙi a dukkan sha’aninsa, sauƙi yana ƙarfafa a lokacin samun gajiyawa da buƙata, kuma domin cewa tsanantawa a ayyuka na Addini da barin sauƙi ƙarshensa shi ne gajiyawa da yankewa daga barin aiki gabaɗayansa ko wani daga ciki. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar akan tsakatsakiya ba tare da zirfafawa ba; kada bawa ya taƙaita a cikin abinda aka umarce shi da shi, kuma kada ya ɗorawa kansa abinda ba zai iya ba, idan ya gajiya daga cikakken aiki to ya yi aiki akan abinda yake kusa da hakan.
Tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi bushara da sakamako mai yawa akan dawwamammen aiki koda kadan ne ga wanda ya gajiya daga aiki cikakke; domin kasawa idan bata kasance daga aikinsa ba to bata lazimtar tauye ladansa.
Yayin da cewa duniya a haƙiƙa gidan tafiya ce da tashi zuwa lahira sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi umarni da neman taimako akan dawwama akan ibada ta hanyar yinta a cikin lokuta uku masu sa nishaɗantarwa:
Na farko: Jijjifi: Da tafiya a farkon yini; tsakanin sallar Asuba da hudowar rana.
Na biyu: Yammaci: Da tafiya bayan karkacewar rana.
Na uku: Duhun dare: Da tafiyar dare gabaɗayansa ko sashinsa, domin cewa aikin dare yafi wahala akan aikin rana sai aka yi umarni da sashinsa da faɗinsa: Da wani abu daga duhun dare.
Fa’idoji
- Sauƙi da afuwar shari'ar Musulunci da tsakatsakiyarta tsakanin wuce gona da iri da kuma sakaci.
- Ya wajaba akan bawa ya aikata umarni gwargwadan ikonsa, ba tare da sakaci ko tsanantawa ba.
- Ya wajaba akan bawa ya zaɓi lokutan nishaɗi a cikin ibada, waɗannan lokuta ukun a keɓancesu sune mafi hutawar jiki dan yin ibada a cikinsu.
- Ibnu Hajar Al’Asƙalani ya ce: Kamar cewa shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa matafiyi magana ne zuwa manufa, waɗannan lokuta ukun sune mafi daɗin lokutan matafiyi, sai ya faɗakar da shi akan lokutan kazar-kazar; domin matafiyi idan ya yi tafiyar dare da rana gaba ɗaya zai gajiya ya yanke, idan ya kintaci tafiya a cikin waɗannan lokuta masu nishaɗantarwa sai ya samu damar dawwama ba tare da wahala ba.
- Ibnu Hajar ya ce: Nuni a cikin wannan hadisin zuwa riƙo da sauƙi na shari'a, domin riƙo da azima a lokacin sauƙi zirfafawa ne, kamar wanda ya bar Taimama a lokacin gajiyawa daga anfani da ruwa sai anfani da shi ya kai shi zuwa faruwar wata cuta.
- Ibnul Munir ya ce; A cikin wannan Hadisin akwai alama daga alamomin Annabci, haƙiƙa mun ga mutane a gabaninmu sun ga cewa dukkan mai zirfafawa a Addini zai yanke, bawai ana nufin hana neman mafi cika a ibada ba cewa shi yana daga al'amura ababen yabo, kai hana wuce gona da iri mai kaiwa ne zuwa ƙosawa, kai zirfafawa a aikin nafila mai kaiwa ne zuwa ga barin abin da ya fi, ko fitar da farilla daga lokacinta kamar wanda ya kwana yana sallar dare gaba ɗayansa sai ya yi bacci daga sallar Asuba a cikin jam’i, ko zuwa lokacin hudowar rana sai lokacin farillar ya fita.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 16) (39).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 219).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص115).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي هريرة رضي الله عنه مرفوعاً: «بينما رجلٌ يمشي بطريقٍ اشتَدَّ عليه العَطَشُ، فوَجَدَ بِئْرًا فنزل فيها فَشَرِبَ، ثم خَرَجَ فإذا كَلْبٌ يَلْهَثُ يأكل الثَّرَى مِنَ العَطَشِ، فقال الرجلُ: لقد بَلَغَ هذا الكَلْبَ مِنَ العَطَشِ مِثْلَ الذِي كان قَدْ بَلَغَ مِنِّي، فنَزَلَ البِئْرَ، فَمَلَأَ خُفَّهُ ماءً ثم أَمْسَكَهُ بِفِيهِ حَتَّى رَقِيَ، فَسَقَى الكَلْبَ، فشَكَرَ اللهُ له، فَغَفَرَ لهُ» قالوا: يا رسول الله، إنَّ لَنَا في البَهَائِمِ أَجْرًا؟ فقال: «في كُلِّ كَبِدٍ رَطْبَةٍ أَجْرٌ».
وفي رواية: «فشَكَرَ اللهُ له، فغَفَرَ له، فَأَدْخَلَهُ الجَنَّةَ».
وفي رواية: «بَيْنَمَا كَلْبٌ يُطِيفُ بِرَكْيَةٍ قد كَادَ يَقْتُلُهُ العَطَشُ إذ رَأَتْهُ بَغِيٌّ مِنْ بَغَايَا بَنِي إِسْرَائِيلَ، فَنَزَعَتْ مُوقَهَا فَاسْتَقَتْ له بهِ فَسَقَتْهُ فَغُفِرَ لها بِهِ».
Daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - tare da isnadi: “Yayin da wani mutum yake tafiya a kan wata hanya da ta ji kishin ruwa sosai, sai ya sami wata rijiya, sai ya sha, sannan ya fito. Sai rijiyar ta sauko, ta cika takalminsa da ruwa, sannan ya rike ta a ciki har sai an shayar da shi, kuma ya shayar da karnuka, don haka Allah ya gode masa, don haka ya gafarta masa. Ya ce: "Akwai albashi a cikin kowane hanta." Kuma a cikin wata ruwaya: "Allah ya gode masa, sai ya gafarta masa, sai ya sanya shi a Aljanna." Kuma a cikin ruwaya: “Yayin da kare yake yawo a cikin maraƙi, sai ƙishirwa ta kusan kashe shi, lokacin da ta ganshi da muradi saboda Isra’ilawa, sai ta birkice ta.
Buhari ne ya rawaito shi - Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara
رياض الصالحين، للنووي، نشر: دار ابن كثير للطباعة والنشر والتوزيع، دمشق – بيروت، تحقيق: ماهر ياسين الفحل، الطبعة: الأولى، 1428هـ - 2007م.
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، نشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة: الرابعة عشر، 1407ه 1987م.
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين، نشر: دار الوطن للنشر، الرياض، الطبعة: 1426ه.
كنوز رياض الصالحين، نشر: دار كنوز إشبيليا، الطبعة: الأولى، 1430ه 2009م.
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، للهلالي، نشر: دار ابن الجوزي. ط1 -1415
المعجم الوسيط، نشر: دار إحياء التراث العربي، بيروت – لبنان، الطبعة: الثانية.
صحيح البخاري، نشر: دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم ترقيم محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى، 1422ه.
صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، نشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com