Ubayyu ɗan Ka'ab - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa wani mutum daga cikin mutanen Madina yana daga cikin mafi nisan gida daga masallacin Annabi, kuma ya kasance sallah bata wuce shi; kai yana halattar kowace sallah tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai aka ce masa: Inama dai a ce zaka sayi jakin da zaka dinga hawansa a cikin duhun dare da kuma cikin zafin ƙasa a cikin rana, ya ce: Bana son a ce gidana yana gefen masallaci, lallai ni ina son Allah Ya rubuta mini tafiyata zuwa masallaci, da kuma dawowata idan na dawo zuwa ga iyalaina, sai maganarsa ta kai wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: «Haƙiƙa Allah Ya haɗa maka hakan baki ɗayansu».
- Tsananin kwaɗayin sahabbai akan alheri da neman ƙaruwar shi da kuma neman lada.
- Nawawi ya ce: A cikinsa akwai tabbatar da lada a cikin takun dawowa daga sallah kamar yadda yake tabbata a tafiya.
- Musulmi su yi wa junansu wasiyya da alheri da kuma nasiha da aikin alheri, wanda ya ga cewa ɗan'uwansa wata wahala tana riskarsa to ya gabatar masa da nasiha a gusar da ita.
- Nisan gida daga masallaci ba uzuri ba ne a kan barin jam’i, muddin dai yana jin kiran sallah.
صحيح مسلم (1/ 460) (663). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 162). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 199).