Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

GAMEWAR ADDININ MUSULUNCI

Hadisai 3

Ka bauta wa Allah shi kaxai, kada ka hada kome da Shi, kuma ka bar abin da ubanninka suka fada, kuma Ya umurce mu da yin addu’a da gaskiya

عن أبي سفيان صخر بن حرب رضي الله عنه قال: قال هِرَقل: فماذا يَأمُرُكُم -يعني: النبي صلى الله عليه وسلم- قال أبو سفيان: قلت: يقول: «اعبدُوا الله وَحدَه لاَ تُشرِكُوا بِهِ شَيئًا، وَاترُكُوا ما يَقُول آبَاؤُكُم، ويَأمُرُنَا بِالصَّلاَة، والصِّدق، والعَفَاف، والصِّلَة».
Daga Abu Sufyan Sakhr bin Harb - yardar Allah ta tabbata a gare shi - ya ce: Hercules ya ce: Me yake umartarku - ma'ana: Annabi, Salati da amincin Allah su tabbata a gare shi - Abu Sufyan ya ce: Na ce: "Ka bauta wa Allah shi kaɗai, kada ka haɗa shi da wani abu, kuma bari mahaifinka ya faɗi abin da ya ce. Ta hanyar addu’a, gaskiya, tsabtar rai, da addu’a ».
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي، ط1، دار ابن الجوزي، الدمام، 1415هـ. تطريز رياض الصالحين، للشيخ فيصل المبارك، ط1، تحقيق: عبد العزيز بن عبد الله آل حمد، دار العاصمة، الرياض، 1423هـ. دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين، لمحمد علي بن محمد بن علان، ط4، اعتنى بها: خليل مأمون شيحا، دار المعرفة، بيروت، 1425هـ. رياض الصالحين للنووي، ط1، تحقيق: ماهر ياسين الفحل، دار ابن كثير، دمشق، بيروت، 1428هـ. رياض الصالحين، ط4، تحقيق: عصام هادي، وزارة الأوقاف والشؤون الإسلامية القطرية، دار الريان، بيروت، 1428هـ. شرح رياض الصالحين، للشيخ ابن عثيمين، دار الوطن للنشر، الرياض، 1426هـ. صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422هـ. صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت. نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين، ط14، مؤسسة الرسالة، 1407هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Na rantse da wanda raina yake a hannunSa, Ibnu Maryam (Annabi Isa) ya kusa ya sauka a cikinku yana mai hukunci mai adalci, sai ya karya gicciyayye (cross), ya kashe alade, ya sarayar da jizya, dukiya ta yawaita har babu wanda zai karbeta

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «وَالَّذِي نَفْسِي بِيَدِهِ، لَيُوشِكَنَّ أَنْ يَنْزِلَ فِيكُمْ ابْنُ مَرْيَمَ حَكَمًا مُقْسِطًا، فَيَكْسِرَ الصَّلِيبَ، وَيَقْتُلَ الخِنْزِيرَ، وَيَضَعَ الجِزْيَةَ، وَيَفِيضَ المَالُ حَتَّى لاَ يَقْبَلَهُ أَحَدٌ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Na rantse da wanda raina yake a hannunSa, Ibnu Maryam (Annabi Isa) ya kusa ya sauka a cikinku yana mai hukunci mai adalci, sai ya karya gicciyayye (cross), ya kashe alade, ya sarayar da jizya, dukiya ta yawaita har babu wanda zai karbeta".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana rantsuwa akan kusancin saukar (Annabi) Isa dan Nana Maryam - aminci ya tabbata agare shi - dan ya yi hukunci a tsakanin mutane da adalci da shari'ar Annabi muhammadu, kuma shi zai karya gicciyayye (kros) wanda kiristoci suke girmama shi, kuma Annabi Isa - aminci ya tabbata agare shi - zai kashe alade, kuma cewa shi aminci ya tabbata agare shi zai sarayar da jiziya zai dora mutane gaba dayansu a shiga Addinin Musulunci. Kuma dukiya za ta yawaita wani ba zai karbeta ba; dan yawanta, da wadatuwar kowa da abinda ke hannunsa, da saukar albarka da malalowar alkairai.

Fa’idoji
  1. Tabbatar da saukar Annabi Isa - aminci ya tabbata agare shi - a karshen zamani, kuma cewa shi yana daga alamomin Alkiyama .
  2. Shari'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - watanta ba za ta shafeta ba.
  3. Saukar albarkoki a dukiya a karshen zamani, tare da cewa mutane zasu guje mata.
  4. Albishir da wanzuwar Addinin Musulunci ta yadda Annabi Isa - aminci ya tabbata agare shi - zai yi hukunci da shi a karshen zamani.
Madogara

صحيح البخاري (3/ 82) (2222)، صحيح مسلم (1/ 135) (155)، شرح النووي على مسلم (1/471)، التوضيح (14/555)، عمدة القاري شرح صحيح البخاري (12/ 35).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ya ku mutane lallai Allah Ya kawar muku da wautar Jahilci da jiji da kai da iyayen da take sa su

عَنِ ‌ابْنِ عُمَرَ رضي الله عنهما: أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ خَطَبَ النَّاسَ يَوْمَ فَتْحِ مَكَّةَ، فَقَالَ: «يَا أَيُّهَا النَّاسُ، إِنَّ اللهَ قَدْ أَذْهَبَ عَنْكُمْ عُبِّيَّةَ الْجَاهِلِيَّةِ وَتَعَاظُمَهَا بِآبَائِهَا، فَالنَّاسُ رَجُلَانِ: بَرٌّ تَقِيٌّ كَرِيمٌ عَلَى اللهِ، وَفَاجِرٌ شَقِيٌّ هَيِّنٌ عَلَى اللهِ، وَالنَّاسُ بَنُو آدَمَ، وَخَلَقَ اللهُ آدَمَ مِنْ تُرَابٍ، قَالَ اللهُ: {يَا أَيُّهَا النَّاسُ إِنَّا خَلَقْنَاكُمْ مِنْ ذَكَرٍ وَأُنْثَى وَجَعَلْنَاكُمْ شُعُوبًا وَقَبَائِلَ لِتَعَارَفُوا إِنَّ أَكْرَمَكُمْ عِنْدَ اللهِ أَتْقَاكُمْ إِنَّ اللهَ عَلِيمٌ خَبِيرٌ} [الحجرات: 13]».
Daga Ɗan Umar Allah Ya yarda da su: Lallai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi wa mutane huɗuba a ranar buɗe Makka, sai ya ce: "Ya ku mutane lallai Allah Ya kawar muku da wautar Jahilci da jiji da kai da iyayen da take sa su, sabo da haka mutane sun kasu biyu: Mai biyayya ga Allah kuma mai tsoronSa mai girma a wajen Allah, da kuma fajiri taɓaɓɓe wulaƙantacce a wajen Allah, mutane 'ya'yan (Annabi) Adam ne, kuma Allah Ya halicci Annabi Adam daga turɓaya, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Ya ku mutane lallai Mun halicce ku daga namiji da mace, kuma muka sanya ku jama'a da ƙabilu don ku san juna, lallai mafi girmanku a wurin Allah shi ne mafificinku a tsoron Allah, lallai Allah Masani ne kuma mai ba da labari [Al-Hujrat: 13].
Tirmizi da Ibn Hibban ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi wa mutane huɗuba a ranar buɗe Makka sai ya ce: Ya ku mutane lallai cewa Allah haƙiƙa ya ɗauke kuma ya gusar muku da girman kan Jahiliyya, da jiji da kanta, da alfahari da iyaye, kawai dai mutane sun rabu gida biyu: Ko dai mumini mutumin kirki mai tsoron Allah mai biyayya ga Allah - Mai girma da ɗaukaka -, to, wannan mai girma ne a wajen Allah, ko da bai zama mai wani matsayi ko nasaba a wurin mutane ba. Ko kafiri fajiri taɓaɓɓe, to, wannan wulaƙantacce ne ƙasƙantacce a wurin Allah, kuma bai yi daidai da komai ba, ko da ya zama mai matsayi kuma yana da alfarma da mulki. Mutane dukkaninsu 'ya'yan Adam ne, kuma Allah Ya halicci Adam daga turɓaya, ba ya dacewa ga wanda asalinsa daga turɓaya ne ya yi girman kai ya yi jiji da kai, gasgata hakan shi ne faɗin Allah - Mai girma da ɗaukaka -: {Ya ku mutane lallai Mu Mun halicceku daga namiji da mace, kuma mun sanyaku jama'a da ƙabilu don ku san juna, lallai mafi girmanku a wajen Allah shi ne mafi tsoronku ga Allah, lallai Allah Masani ne Mai ba da labari} [Al-Hujurat: 13].

Fa’idoji
  1. Hani daga alfahari da dangantaka da kuma matsayi.
Madogara

سنن الترمذي (5/ 309) (3270)، صحيح ابن حبان (9/ 137) (3828)، عون المعبود وحاشية ابن القيم (14/ 16)، النهاية في غريب الحديث والأثر (ص587).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com