Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

HAƘƘOƘIN MUTUM A MUSULUNCI

Hadisai 3

Kun ganni na bakwai a cikin Bakwai Bakwai. Ba mu da wani bawa sai wanda ya mari karaminmu, don haka Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya umurce mu da 'yantar da ita

عن أبي علي سويد بن مُقَرِّن رضي الله عنه قال: لقد رَأَيْتُنِي سابع سبعة من بني مُقَرِّن ما لنا خادم إلا واحدة لطمها أصغرنا فأمرنا رسول الله صلى الله عليه وسلم أن نعتقها وفي رواية: «سابع إخوة لي».
Daga Abu Ali Suwaid bin Muqrin - Allah ya yarda da shi - ya ce: Kun ganni na bakwai a cikin Bakwai Bakwai. Ba mu da wani bawa sai wanda ya mari karaminmu, don haka Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya umurce mu da 'yantar da ita kuma a cikin wata ruwaya: "Na bakwai daga' yan'uwana"
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Suwaid bin Muqrin yana cewa, “Na kasance daya daga cikin‘ yan’uwa bakwai daga Banu Muqrin, dukkansu abokan tafiya ne na bakin haure, kuma babu wanda ya shiga tare da su a cikin haka: Taro ne na ‘yan’uwa bakwai a cikin hijira, kuma babu wani daga cikinmu ya dogara ne akan aikinmu na bakwai banda ɗaya mallakar. Don haka Ya umurce mu - Allah Ya yi masa tsira da aminci - ya ‘yanta ta daga bautar. Don sanya ta saki kaffarar dukawarta.

Madogara

نزهة المتقين، تأليف: مصطفى الخن وآخرون، الناشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة الأولى: 1397 هـ الطبعة الرابعة عشر 1407 هـ. كنوز رياض الصالحين، تأليف: حمد بن ناصر بن العمار، الناشر: دار كنوز أشبيليا، الطبعة الأولى: 1430 هـ. بهجة الناظرين، تأليف: سليم بن عيد الهلالي، الناشر: دار ابن الجوزي، سنة النشر: 1418 هـ- 1997م. صحيح مسلم، تأليف: مسلم بن الحجاج النيسابوري، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي الناشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت. رياض الصالحين، تأليف: محيي الدين يحيى بن شرف النووي ، تحقيق: د. ماهر بن ياسين الفحل ، الطبعة: الأولى، 1428 هـ. شرح رياض الصالحين، العثيمين، الناشر: دار الوطن للنشر، الرياض - الطبعة: 1426 هـ. دليل الفالحين، لابن علان الصديقي، دار الكتاب العربي - بيروت.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ku dinga aikata aikin da zaku iya, na rantse da Allah, Allah ba Ya ƙosawa har sai kun ƙosa

عَنِ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤْمِنين رَضيَ اللهُ عنها زَوْجَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: أَنَّ الْحَوْلَاءَ بِنْتَ تُوَيْتِ بْنِ حَبِيبِ بْنِ أَسَدِ بْنِ عَبْدِ الْعُزَّى مَرَّتْ بِهَا وَعِنْدَهَا رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقُلْتُ: هَذِهِ الْحَوْلَاءُ بِنْتُ تُوَيْتٍ، وَزَعَمُوا أَنَّهَا لَا تَنَامُ اللَّيْلَ، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَا تَنَامُ اللَّيْلَ! خُذُوا مِنَ الْعَمَلِ مَا تُطِيقُونَ، فَوَاللهِ لَا يَسْأَمُ اللهُ حَتَّى تَسْأَمُوا».
Daga Nana A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - matar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Lallai cewa Haula'a Bint Tuwait Ibnu Habib Ibnu Asad Ibnu Abdul'uzza ta wuceta alhali Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana wurinta, sai na ce: Wannan Haula'u ce Bnit Tuwait, kuma sun yi da'awar cewa bata baccin dare, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «‌Bata baccin dare! Ku dinga aikata aikin da zaku iya, na rantse da Allah, Allah ba Ya ƙosawa har sai kun ƙosa».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Haula'u Bnt Tuwait - Allah Ya yarda da ita - ta kasance a wurin uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita -, lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shigo gurinta (Nana A'isha), sai (Haula'u) ta fita ta barta Sai Nana A'isha ta ce masa: Wannan matar bata baccin dare, kai tana raya shi da sallah. Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce yana mai tsananin yi mata inkari: Bata baccin dare! ku shagalta da aiki na gari wanda zaku iya dawwama a kansa, na rantse da Allah, Allah ba Ya ƙosawa akan baiwa bayinSa salihai masu biyayya lada da sakamako akan biyayyarsu da kuma kyawawan ayyukansu da kuma ayyukansu na gari har sai sun ƙosa sun bar aikin.

Fa’idoji
  1. Yawaita ibada sama da yadda jiki zai iya, yana kaiwa zuwa ga ƙosawa da kuma yankewa sai zuciya ta daina yin aikin.
  2. Daidaituwa da tsakatsaki a cikin yin ibada hakan yana sawa a ci gaba da ibadar da kuma tabbata a kanta.
  3. Kanƙanin aiki da aka dawwama ana yi ya fi alheri akan aiki mai yawa mai sa a yanke aikin.
  4. Nawawi ya ce: Ta hanyar dawwama da aiki kaɗan ɗa'a tana zarcewa da zikiri da muraƙaba da ikhlasi da kuma fuskanta ga Allah, saɓanin aiki mai yawa mai wahalarwa har aiki ɗan kaɗan ya ƙaru ta inda zai fi mai yawa wanda aka daina da lada mai yawa.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 17) (43). صحيح مسلم (1/ 542) (785). فتح الباري شرح صحيح البخاري، لابن رجب (1/ 164). معجم اللغة العربية المعاصرة، أحمد مختار(2/ 1020). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 212).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ya ku mutane lallai Allah Ya kawar muku da wautar Jahilci da jiji da kai da iyayen da take sa su

عَنِ ‌ابْنِ عُمَرَ رضي الله عنهما: أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ خَطَبَ النَّاسَ يَوْمَ فَتْحِ مَكَّةَ، فَقَالَ: «يَا أَيُّهَا النَّاسُ، إِنَّ اللهَ قَدْ أَذْهَبَ عَنْكُمْ عُبِّيَّةَ الْجَاهِلِيَّةِ وَتَعَاظُمَهَا بِآبَائِهَا، فَالنَّاسُ رَجُلَانِ: بَرٌّ تَقِيٌّ كَرِيمٌ عَلَى اللهِ، وَفَاجِرٌ شَقِيٌّ هَيِّنٌ عَلَى اللهِ، وَالنَّاسُ بَنُو آدَمَ، وَخَلَقَ اللهُ آدَمَ مِنْ تُرَابٍ، قَالَ اللهُ: {يَا أَيُّهَا النَّاسُ إِنَّا خَلَقْنَاكُمْ مِنْ ذَكَرٍ وَأُنْثَى وَجَعَلْنَاكُمْ شُعُوبًا وَقَبَائِلَ لِتَعَارَفُوا إِنَّ أَكْرَمَكُمْ عِنْدَ اللهِ أَتْقَاكُمْ إِنَّ اللهَ عَلِيمٌ خَبِيرٌ} [الحجرات: 13]».
Daga Ɗan Umar Allah Ya yarda da su: Lallai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi wa mutane huɗuba a ranar buɗe Makka, sai ya ce: "Ya ku mutane lallai Allah Ya kawar muku da wautar Jahilci da jiji da kai da iyayen da take sa su, sabo da haka mutane sun kasu biyu: Mai biyayya ga Allah kuma mai tsoronSa mai girma a wajen Allah, da kuma fajiri taɓaɓɓe wulaƙantacce a wajen Allah, mutane 'ya'yan (Annabi) Adam ne, kuma Allah Ya halicci Annabi Adam daga turɓaya, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Ya ku mutane lallai Mun halicce ku daga namiji da mace, kuma muka sanya ku jama'a da ƙabilu don ku san juna, lallai mafi girmanku a wurin Allah shi ne mafificinku a tsoron Allah, lallai Allah Masani ne kuma mai ba da labari [Al-Hujrat: 13].
Tirmizi da Ibn Hibban ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi wa mutane huɗuba a ranar buɗe Makka sai ya ce: Ya ku mutane lallai cewa Allah haƙiƙa ya ɗauke kuma ya gusar muku da girman kan Jahiliyya, da jiji da kanta, da alfahari da iyaye, kawai dai mutane sun rabu gida biyu: Ko dai mumini mutumin kirki mai tsoron Allah mai biyayya ga Allah - Mai girma da ɗaukaka -, to, wannan mai girma ne a wajen Allah, ko da bai zama mai wani matsayi ko nasaba a wurin mutane ba. Ko kafiri fajiri taɓaɓɓe, to, wannan wulaƙantacce ne ƙasƙantacce a wurin Allah, kuma bai yi daidai da komai ba, ko da ya zama mai matsayi kuma yana da alfarma da mulki. Mutane dukkaninsu 'ya'yan Adam ne, kuma Allah Ya halicci Adam daga turɓaya, ba ya dacewa ga wanda asalinsa daga turɓaya ne ya yi girman kai ya yi jiji da kai, gasgata hakan shi ne faɗin Allah - Mai girma da ɗaukaka -: {Ya ku mutane lallai Mu Mun halicceku daga namiji da mace, kuma mun sanyaku jama'a da ƙabilu don ku san juna, lallai mafi girmanku a wajen Allah shi ne mafi tsoronku ga Allah, lallai Allah Masani ne Mai ba da labari} [Al-Hujurat: 13].

Fa’idoji
  1. Hani daga alfahari da dangantaka da kuma matsayi.
Madogara

سنن الترمذي (5/ 309) (3270)، صحيح ابن حبان (9/ 137) (3828)، عون المعبود وحاشية ابن القيم (14/ 16)، النهاية في غريب الحديث والأثر (ص587).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com