عَنْ المِقْدَامِ بْنِ مَعْدِي كَرِبَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «مَا مَلأَ آدَمِيٌّ وِعَاءً شَرًّا مِنْ بَطْنٍ، بِحَسْبِ ابْنِ آدَمَ أَكَلاَتٌ يُقِمْنَ صُلْبَهُ، فَإِنْ كَانَ لَا مَحَالَةَ، فَثُلُثٌ لِطَعَامِهِ، وَثُلُثٌ لِشَرَابِهِ، وَثُلُثٌ لِنَفَسِهِ».
Daga Miƙdam ibnu Ma'adikarib - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: «Ɗan Adam bai cika ƙwarya mafi sharri daga ciki ba, 'yan lomomi su ishi ɗan Adam waɗanda zasu tsaida bayansa, idan ya kasance babu makawa, to ɗaya bisa uku dan abincinsa, da ɗaya bisa uku dan abin shansa, da ɗaya bisa uku dan numfashinsa».
Imam Ahmad da Tirmizi da Nasa'i da Ibnu Majah ne Suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi mai girma da daraja - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana shiryar da mu zuwa wani asali daga asalan kiwon lafiya, shi ne rigakafin da mutum zai kare lafiyarsa da shi, shi ne ƙaranta cin abinci, kawai ya ci gwargwadan abin da zai toshe kafarsa kuma ya ƙarfafe shi akan ayyyukansa na dole, kuma cewa mafi sharrin ƙwaryar da aka cika ita ce ciki, dan abin da ƙoshi yake haifarwa na cutuka masu kisa waɗanda ba za su ƙirgu ba a gaggauce ko a jinkirce a baɗini ko a zahiri. Sannan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Idan babu makawa mutum sai ya ƙoshi, to ya maida cinsa gwargwadan ɗaya bisa uku, ɗaya bisa ukun kuma dan shan ruwa, da ɗaya bisa ukun dan numfashi dan kada ƙunci da cuta su same shi, da kuma kasala daga yin abin da Allah Ya wajabta a kansa a cikin al'amarin Addininsa ko duniyarsa.
Fa’idoji
- Rashin yalwatawa a cikin ci da sha, wannan wani asali ne wanda ya tattaro asalan kiwon lafiya gaba ɗayansu, dan abin da ke cikin yawaita ƙoshi na cutuka da kuma masassara.
- Manufa a cin abin ci, ita ce kiyaye lafiya da ƙarfi wadanda da su ne ake samun kuɓutar rayuwa.
- Akwai cutuka na jiki da na Addini ga cika ciki da abinci, Umar - Allah Ya yarda da shi - ya ce: «Na haneku akan cika ciki, domin hakan mai ɓata jiki ne, kuma mai sa kasala ne daga sallah».
- Ci ta hanyar hukunci rabe-rabe ne: Wajibi, shi ne abin da a cikinsa akwai kiyaye rayuwa kuma barinsa yana kaiwa zuwa cutarwa. Ja'izi, shi ne abin da ya ƙaru akan gwargwado na wajibi, kuma ba'a jin tsoron cutuwarsa. Makruhi, shi ne abin da ake jin tsoron cutarsa. Haram, shi ne abin da aka san cutuwarsa. Mustahabbi, shi ne abin da ake neman taimako da shi akan bautar Allah da kuma yi maSa ɗa'a (biyayya), haƙiƙa ya dunƙule hakan a cikin hadisi a cikin matakai uku: Na farkonsu: Cika ciki. Na biyunsu: Cin 'yan lomomin da zasu daidaita bayansa. Na uku: Faɗinsa: «Ɗaya bisa uku dan abin cinsa da ɗaya bisa uku dan abin shansa, da ɗaya bisa uku dan numfashinsa» wannan dukkaninsa idan jinsin abin da aka ci ya zama halal ne.
- Hadisin ƙa'ida ce daga cikin ƙa'idojin kiwon lafiya, lokacin da ilimin likitanci ya dunƙule akan tushe uku ne: Kiyaye ƙarfi da taƙaita cin abin ci da kuma iska, haƙiƙa hadisi ya ƙunshi biyun farko daga cikinsu, kamar yadda yake a cikin faɗinSa - Maɗaukakin sarki -: {Ku ci, kuma ku sha kada ku yi ɓarna lallai Allah ba ya son masu ɓarna}[al-A'araf: 31].
- Cikar wannan shari'ar inda ta ƙunshi maslahohin mutum a cikin Addininsa da kuma duniyarsa.
- Daga ilimummukan shari'a akwai tushe na kiwon lafiya da kuma nau'ikansa, kamar yadda ya zo a cikin zuma da Habbaus sauda'a.
- Ƙunsar hukunce-hukuncen shari'a akan hikima, kuma cewa su an ginasu ne akan tunkuɗe ɓarna da jawo anfani.
Madogara
سنن الترمذي (4/ 188) (2380).
سنن ابن ماجه (4/ 448) (3349).
مسند أحمد (28/ 422) (17186).
فتح الباري لابن حجر (9/ 528).
جامع العلوم والحكم في شرح خمسين حديثا من جوامع الكلم، لابن رجب (2/ 467).
التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثًا النووية، لإسماعيل الأنصاري (ص100).
فتح القوي المتين في شرح الأربعين وتتمة الخمسين، لعبد المحسن العباد (ص148).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أسامة بن زيد رضي الله عنهما عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «مَا تَرَكْتُ بَعْدِي فِتْنَةً أَضَرَّ عَلَى الرِّجَالِ مِنَ النِّسَاءِ».
Daga Usama Ɗan Zaid Allah Ya yarda da su, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Ban bar wata fitina a baya na ba mafi cutar da Maza kamar mata ba.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da labarin bai bar jarabawa a bayansa ba mafi cutar da Maza kamar mata ba, idan mace ta kasance cikin iyalansa ne, to, zai dinga kula da ita domin kada ta kaucewa Shari’a, idan kuma wata ce da ban, to, sabo da cuɗanya da kaɗaituwa da ita, da kuma irin barnar da zata biyo bayan haka.
Fa’idoji
- Ya wajaba a kan Musulmi ya kiyayi fitinar mata, ya toshe duk wata hanya da za ta kai ga hakan.
- Ya kamata ga Muminai riƙo da Allah da kwaɗayi a wurin sa domin kiyayewa daga fitintinu.
Madogara
صحيح البخاري (7/ 8) (5096).
صحيح مسلم (4/ 2097) (2740).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (373).
فتح الباري لابن حجر (9/ 138).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي هريرة رضي الله عنه أن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «كُتب على ابن آدم نَصِيبُه من الزِنا مُدْرِكُ ذلك لا مَحَالة: العينان زِناهما النَظر، والأُذنان زِناهما الاستماع، واللسان زِناه الكلام، واليَدُ زِناها البَطْش، والرِّجل زِناها الخُطَا، والقلب يَهْوَى ويتمنى، ويُصَدِّق ذلك الفَرْج أو يُكذِّبُه».
Daga Abu Huraira -Allah ya yarda da su- cewa manzon Allah SAW ya ce: "An rubutawa Xan Adam rabonsa a Zina kuma dole sai ya same shi babu Makawa: Idanu suna Zina zianarsu Kallo, Kunnuwa suna Zina Zinar su Sauraro, Harshe yana Zina Zinarsa Magana, Hannu Zinarsa Tavawa, Qafa kuma Zinarta tafiya, Zuciya Kuma tana so da Buri, kuma Farji yana gasgata hakan ko ya qaryata shi"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara
نزهة المتقين، تأليف: مصطفى الخن، الناشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة الأولى: 1397 هـ الطبعة الرابعة عشر 1407 هـ.
كنوز رياض الصالحين، تأليف: حمد بن ناصر العمار ، الناشر: دار كنوز أشبيليا، الطبعة الأولى: 1430 هـ.
بهجة الناظرين، تأليف: سليم بن عيد الهلالي، الناشر: دار ابن الجوزي ، سنة النشر: 1418 هـ- 1997م.
صحيح مسلم، تأليف: مسلم بن الحجاج النيسابوري، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي الناشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت.
رياض الصالحين، تأليف: محيي الدين يحيى بن شرف النووي ، تحقيق: د. ماهر بن ياسين الفحل ، الطبعة: الأولى، 1428 هـ.
صحيح البخاري، تأليف: محمد بن إسماعيل البخاري، تحقيق: محمد زهير الناصر، الناشر: دار طوق النجاة الطبعة: الأولى، 1422هـ.
شرح رياض الصالحين، تأليف: محمد بن صالح العثيمين، الناشر: دار الوطن للنشر، 1426 هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن عقبة بن عامر، يقول: إن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «إنِّي أخاف على أُمَّتي اثنَتَيْن: القرآنَ واللَّبَن، أما اللَّبَن فيَبْتَغُون الرِّيفَ ويتَّبِعون الشَّهَوَاتِ ويَتْركون الصلوات، وأما القرآن فيتعلَّمه المنافقون فيُجادِلون به المؤمنين».
Daga Uquba Bn Amir ya na cewa lallai Manzon SAW ya ce da ni: "Abubuwa biyu nafi tsoro ga Al-umma ta Al-qur'ani da kuma Nono, Amma tsorona da nono saboda zasu riqa bin kauyuka kuma suna bin son ransu kuma suna barin Sallah, kuma Al-Qur'ani shi ne Munafukai su koyeshi sai su riqa jayayya da muminai da shi"
Ahmad ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
A cikin wannan hadisin, Annabi mai tsira da amincin Allah, ya nuna tsoronsa ga al’ummarsa abubuwa biyu da suka shafi Alkur’ani da kuma madara.Sai dai ga kofi, wasu mutane suna neman sanya shi a cikin makiyaya da amfanin gona, kuma suna bin sha’awoyinsu da jin daɗinsu, kuma suna karkata daga garuruwan da ake yin sallar Juma’a da ta jam’i, sannan suna barin salla bayan Wannan buƙata ce don kofi, kuma game da Kur'ani, munafukai suna koyon sa, ba don fa'idantar da shi da aiki da shi ba, amma don jayayya da muminai da ƙarya. Don mayar da gaskiyar da suke da ita. Ba madara ba ce a cikin kansa, ko Alkurani, wannan shi ne tushen tsoro da cutarwa.Maimakon haka, suna bayyana su da misalai game da abin da ya shafe su, kuma Allah ne Mafi sani.
Madogara
-مسند الإمام أحمد بن حنبل، تحقيق: شعيب الأرنؤوط - عادل مرشد، وآخرون، نشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة: الأولى، 1421هـ - 2001م.
-سلسلة الأحاديث الصحيحة وشيء من فقهها وفوائدها، تأليف محمد ناصر الدين الألباني، الناشر: مكتبة المعارف للنشر والتوزيع، الرياض، الطبعة: الأولى، لمكتبة المعارف.
-مختار الصحاح، لزين الدين أبو عبد الله محمد بن أبي بكر بن عبد القادر الحنفي الرازي، تحقيق: يوسف الشيخ محمد، نشر: المكتبة العصرية - الدار النموذجية، بيروت – صيدا، لطبعة: الخامسة، 1420هـ / 1999م.
-النهاية في غريب الحديث والأثر، لابن الأثير، نشر: المكتبة العلمية - بيروت، 1399هـ - 1979م، تحقيق: طاهر أحمد الزاوى - محمود محمد الطناحي.
-الفتح الرباني لترتيب مسند الإمام أحمد بن حنبل الشيباني ومعه بلوغ الأماني من أسرار الفتح الرباني, أحمد بن عبد الرحمن بن محمد البنا الساعاتي, دار إحياء التراث العربي, الطبعة: الثانية.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ رضي الله عنهما أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «لَا تَعَلَّمُوا الْعِلْمَ لِتُبَاهُوا بِهِ الْعُلَمَاءَ، وَلَا لِتُمَارُوا بِهِ السُّفَهَاءَ، وَلَا تَخَيَّرُوا بِهِ الْمَجَالِسَ، فَمَنْ فَعَلَ ذَلِكَ، فَالنَّارُ النَّارُ».
Daga Jabir Dan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ku nemi ilimi dan ku yi wa malamai alfahari da shi, ko ku yi musu da wawaye da shi, kuma kada ku nufi bijiro da shi a zababbun majalisai, wanda ya aikata haka to wuta wuta".
Ibnu Majah ne ya ruwaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargadar da wanda ya nemi ilimi dan yi wa malamai alfahari, da bayyanar da cewa ni malami ne irinku, ko dan su yi magana da jayayya da wawaye masu karancin hankali, ko a nemi ilimi dan a bijiro a majalisai, a gabatar da shi akan waninsa a cikinsu. Wanda ya aikata haka; to cewa shi ya cancanci wuta da riyarsa da rashin tsarkake niyyarsa a cikin neman ilimi saboda Allah.
Fa’idoji
- Narko mai tsanani da wuta ga wanda ya nemi ilimi dan ya yi alfahari da shi ko ya yi jayayya da shi ko ya bijirowa majalisai da shi, da makamancin haka.
- Muhimmancin tsarkake niyya ga wanda ya nemi ilimi ya kuma sanar da shi.
- Niyya ita ce tushen ayyuka, kuma akanta ne sakamakon ayyuka yake kasancewa.
Madogara
سنن ابن ماجه (1/ 170) (254)، مرشد ذوي الحجا والحاجة (2/378)، مشارق الأنوار الوهاجة ومطالع الأسرار البهاجة في شرح سنن الإمام ابن ماجه (4/ 482).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ النَّوَّاسِ بْنِ سَمْعَانَ الْأَنْصَارِيِّ رضي الله عنه عَنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «ضَرَبَ اللهُ مَثَلًا صِرَاطًا مُسْتَقِيمًا، وَعَلَى جَنْبَتَيْ الصِّرَاطِ سُورَانِ، فِيهِمَا أَبْوَابٌ مُفَتَّحَةٌ، وَعَلَى الْأَبْوَابِ سُتُورٌ مُرْخَاةٌ، وَعَلَى بَابِ الصِّرَاطِ دَاعٍ يَقُولُ: أَيُّهَا النَّاسُ، ادْخُلُوا الصِّرَاطَ جَمِيعًا، وَلَا تَتَعَرَّجُوا، وَدَاعٍ يَدْعُو مِنْ فَوْقِ الصِّرَاطِ، فَإِذَا أَرَادَ يَفْتَحُ شَيْئًا مِنْ تِلْكَ الْأَبْوَابِ، قَالَ: وَيْحَكَ لَا تَفْتَحْهُ، فَإِنَّكَ إِنْ تَفْتَحْهُ تَلِجْهُ، وَالصِّرَاطُ الْإِسْلَامُ، وَالسُّورَانِ: حُدُودُ اللهِ، وَالْأَبْوَابُ الْمُفَتَّحَةُ: مَحَارِمُ اللهِ، وَذَلِكَ الدَّاعِي عَلَى رَأْسِ الصِّرَاطِ: كِتَابُ اللهِ، وَالدَّاعِي مِنِ فَوْقَ الصِّرَاطِ: وَاعِظُ اللهِ فِي قَلْبِ كُلِّ مُسْلِمٍ».
Daga Nawwas Dan Sam'an Al’Ansary - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Allah Ya buga wani misali hanya ce madaidaiciya, a gefunan hanyar biyu akwai ganuwowi biyu, a cikinsu akwai budaddun kofofi, akan kofofin akwai sakakkun labulaye, a kofar hanyar akwai wani mai kira yana cewa; Yaku mutane, ku shigo hanyar gaba daya, kada ku karkace, da wani mai kiran kuma yana kira a birbishin hanyar, idan ya yi nufin ya bude wani abu daga wadancan kofofin, zai ce: Kaicanka kada ka bude shi , domin cewa kai idan ka bude shi zaka shige shi.
Tafarkin shi ne Musulunci, ganuwowin biyu kuma: Su ne iyakokin Allah, budaddun kofofin kuma: Su ne abubuwan da Allah Ya haramta, wannan mai kiran kuma akan tafarkin: Shi ne littafin Allah, mai kiran kuma a birbishin tafarkin: Mai wa'azin Allah ne (Ajiyoyin Allah) a cikin zuciyar kowane musulmi".
Tirmizi da Ahmad sun rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa; Allah Ya buga wani misali ga Musulunci da hanya madaidaiciya mikakkiya babu karkata a cikinta, agefan wannan hanyar akwai ganuwowi biyu, to bangwaye da suke kewaye da ita ta fuskarsa su ne iyakokin Allah, wasu budaddun kofofi suna shiga wadannan ganuwowi biyun su ne Abubuwan da Allah Ya haramta, akan wadannan kofofin akwai labulayen da basa bayyanar da wanda yake cikinsu ga mai wucewa akan hanyar, afarkon hanyar akwai wani mai kira yake fuskantar da mutane kuma yake shiryar da su yana ce musu: Ku tafi akansa ba tare da kun karkace zuwa wani bangaren ba, wannan mai kiran duk lokacin da mai tafiya akan tafarkin ya yi niyyar ya bude wani gwargwado mai sauki daga labulayen kofofin sai ya tsawatar masa ya ce da shi: Kaicanka kada ka bude shi! domin cewa kai idan ka bude shi zaka shigeshi kuma ba zaka sami damar kare kanka ba daga shiga, wannan mai kiran shi ne mai wa'azin Allah a cikin zuciyar kowane Musulmi.
Fa’idoji
- Musulunci shi ne addinin gaskiya, kuma shi ne tafarki madaidaici wanda zai sadar da mu zuwa Aljanna.
- Wajabcin lazimtar iyakokin Allah da abinda Ya halatta da abinda Ya haramta, kuma cewa sakaci a cikinsu yana gadar da halaka.
- Falalar Alkur’ani mai girma da kwadaitarwa akan aiki da shi, a cikinsa akwai shiriya da haske da tsira.
- Rahamar Allah ga bayinSa da abinda Ya ajiye shi a cikin zukatan muminai na a binda zai hanasu ya kuma wa'azantar da su daga fadawa a cikin halaka.
- Allah da rahamarSa Ya sanya shamakin da zai hana bayinSa afkawa cikin sabo.
- Daga cikin hanyoyin koyarwa akwai buga misali dan kusantowa da bayyanawa.
Madogara
سنن الترمذي (4/ 539) (2859)، مسند أحمد (29/ 181، 183) (17634)، جامع العلوم والحكم (2/161)، فيض القدير (4/253)، التنوير شرح الجامع الصغير (7/100)، الفتح الرباني لترتيب مسند الإمام أحمد بن حنبل الشيباني (1/ 83).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ عَائِشَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهَا قَالَتْ: تَلَا رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ هَذِهِ الْآيَةَ: {هُوَ الَّذِي أَنْزَلَ عَلَيْكَ الْكِتَابَ مِنْهُ آيَاتٌ مُحْكَمَاتٌ هُنَّ أُمُّ الْكِتَابِ وَأُخَرُ مُتَشَابِهَاتٌ فَأَمَّا الَّذِينَ فِي قُلُوبِهِمْ زَيْغٌ فَيَتَّبِعُونَ مَا تَشَابَهَ مِنْهُ ابْتِغَاءَ الْفِتْنَةِ وَابْتِغَاءَ تَأْوِيلِهِ، وَمَا يَعْلَمُ تَأْوِيلَهُ إِلَّا اللَّهُ، وَالرَّاسِخُونَ فِي الْعِلْمِ يَقُولُونَ آمَنَّا بِهِ كُلٌّ مِنْ عِنْدِ رَبِّنَا وَمَا يَذَّكَّرُ إِلَّا أُولُو الْأَلْبَابِ} [آل عمران: 7]. قَالَتْ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «فَإِذَا رَأَيْتِ الَّذِينَ يَتَّبِعُونَ مَا تَشَابَهَ مِنْهُ فَأُولَئِكَ الَّذِينَ سَمَّى اللهُ، فَاحْذَرُوهُمْ».
Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya karanta wannan ayar: {Shi ne wanda ya saukar maka da littafi daga gareshi akwai ayoyi bayyanannu su ne mafi yawan littafi da wasu masu kama da juna, amma wadanda a cikin zukatansu akwai karkata sai suke bin abinda yake kama da juna daga gareshi dan neman fitina da neman tawilinsa, kuma babu wanda yasan tawilinsa sai Allah, matabbata a cikin ilimi suna cewa mun yi imani da shi dukkansa daga gurin Ubangijinmu ne, Ba mai tinani sai ma'abota hankula} [Aal Imran: 7]. Ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan kaga wadanda suke bin masu kama da juna daga gareshi to wadannan su ne Allah Ya ambata, to ku gujesu".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya karanta wannan ayar:{Shi ne wanda ya saukar maka da littafi daga cikinsa akwai ayoyi bayyanannu su ne mafi yawan littafi da wasu masu kama da juna, amma wadanda a cikin zukatansu akwai karkata sai suke bin abinda ya yi kama da juna daga gare shi dan neman fitina da neman tawilinsa, kuma babu wanda ya san tawilinsa sai Allah, matabbata a cikin ilimi suna cewa mun yi imani da shi dukkansa daga gurin Ubangijinmu ne Ba mai tunani sai ma'abota hankalu}.
a cikin wannan ayar Allah - tsarki ya tabbatar maSa -Ya bada labari cewa Shi ne wanda Ya saukar da Alkur’ani ga AnnabinSa, wanda daga cikinsa akwai wasu ayoyi masu bayyananar nuni, hukunce-hukuncensu sanannu ne babu rikici a cikinsu, su ne asalin littafi kuma makomarsa, su ne makoma yayin sabani, daga cikinsa akwai wasu ayoyin daban masu daukar sama da ma'ana, ma'anarsu tana rikitarwa ga wasu daga mutane, ko ya zaci cewa tsakakninsu da wata ayar akwai karo, sannan Allah Ya bayyana mu'amalar mutane tare da wadannan ayoyin.
wadanda a cikin zukatansu akwai karkata daga gaskiya sai su bar bayyayanannu, su yi riko da masu kama da juna masu daukar ma'anoni sama da daya, suna neman tayar da rikici ta hakan da batar da mutane, kuma suna neman tawilinsu akan abinda ya dace da son ransu, amma matabbata a cikin ilimi to cewa su suna sanin wadannan masu kama da junan, suna dawo da shi ga bayyananne, kuma suna yin imani da shi kuma cewa shi daga gurin Allah yake - Madaukakin sarki -, ba zai yiwu ya rikitar ba ko ya yi karo da juna, saidai ba mai tunanin hakan sai mai wa'azantuwa ma'abota hankula lafiyayyu.
Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce wa Uwar Muminai A'isha - Allah Ya yarda da ita - cewa ita idan ta ga wadanda suke neman masu kama da juna to cewa su ne wadanda Allah Ya ambace su a cikin fadinSa; {Amma wadanda a cikin zukatansu akwai karkata} to ku gujesu kada ku karkata zuwa gare su.
Fa’idoji
- Bayyanannu daga ayoyin Alkur’ani ; Su ne wadanda nuninsu ya bayyana kuma ma'anarsu ta bayyana. Mai kama da juna kuma: Wanda ya dauki sama da ma'ana daya kuma ya bukatu zuwa duba da fahimta.
- Gargadarwa daga cakuduwa da ma'abota karkata da 'yan bidi'a da wanda yake jefa mushkiloli dan batar da mutane da sa su kokwanto.
- A karshen ayar da fadinSa - Madaukakin sarki -: {Ba mai tunani sai ma'abota hankula} jirwaye mai kama da wanka ga karkatattu, da yabo ga matabbata a ilimi, yana nufin: Wanda bai yi tinaniba bai wa'azantuba, kuma ya bi son ransa to ba ya daga ma'abota hankula.
- Bin masu kamanceceniya da juna sababine ga karkatar zuciya.
- Wajabcin dawo da ayoyi masu kamanceceniya da juna wadanda ba'a fahimtar ma'anarsu zuwa ga ayoyi bayyanannu.
- Allah - tsarki ya tabbatar maSa - Ya sanya sashin Alkur’ani bayyananne, da wani sashinsa kuma mai kama da juna; dan jarraba mutane dan kuma ma'abota imani su ware daga ma'abota bata.
- A cikin afkuwar mai kama da juna a cikn Alkur’ani: Bayyanar da falalar malamai akan wasunsu, da sanarwar takaituwar hankula; dan su mika wuya ga Mahaliccinsu su yi ikirari da gajiyawarsu.
- Falalar tabbata a cikin ilimi da wajibcin tabbata a cikinsa.
- A hukuncin tsayawa akan {Allah} daga fadinSa: {Kuma babu wanda yasan tawilinsa sai Allah da matabbata a cikin ilimi} a kwai maganganu biyu na masu tafsiri: Wanda ya tsaya akan {Allah}, sai ya zama abin nufi da tawili shi ne sanin hakikanin abu da yadda yake da abinda babu wata hanya zuwa riskarsa kamar al'amarin rai da Alkiyama wadanda Allah ne Ya kebantu da saninsa, matabbata a cikin ilimi suna imani da shi suna fawwala hakikaninsa zuwa ga Allah, sai su mika wuya su kubuta. Wanda kuma ya zarce (a karatu) bai tsaya a {Allah} ba, sai abin nufi da tawili ya zama fassara da bayyanarwa, sai Allah Ya zama Ya san shi matabbata a cikin ilimi suma sun san shi , sai su yi imani da su kuma su dawo da su ga bayyananne.
Madogara
صحيح البخاري (6/ 33) (4547)، صحيح مسلم (4/ 2053) (2665)، فتح الباري (8/211)، شرح النووي على مسلم (16/217)، النهاية في غريب الحديث والأثر (ص 407، 465)، فتح الودود في شرح سنن أبي داود (4/415)، تحفة الأبرار شرح مصابيح السنّة (1/129)، البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (41/ 559).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ حُذَيْفَةَ رضي الله عنه قَالَ: كُنَّا عِنْدَ عُمَرَ رضي الله عنه، فَقَالَ: أَيُّكُمْ سَمِعَ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَذْكُرُ الْفِتَنَ؟ فَقَالَ قوْمٌ: نَحْنُ سَمِعْنَاهُ، فَقَالَ: لَعَلَّكُمْ تَعْنُونَ فِتْنَةَ الرَّجُلِ فِي أَهْلِهِ وَجَارِهِ؟ قَالُوا: أَجَلْ، قَالَ: تِلْكَ تُكَفِّرُهَا الصَّلَاةُ وَالصِّيَامُ وَالصَّدَقَةُ، وَلَكِنْ أَيُّكُمْ سَمِعَ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَذْكُرُ الَّتِي تَمُوجُ مَوْجَ الْبَحْرِ؟ قَالَ حُذَيْفَةُ: فَأَسْكَتَ الْقَوْمُ، فَقُلْتُ: أَنَا، قَالَ: أَنْتَ لِلَّهِ أَبُوكَ، قَالَ حُذَيْفَةُ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «تُعْرَضُ الْفِتَنُ عَلَى الْقُلُوبِ كَالْحَصِيرِ عُودًا عُودًا، فَأَيُّ قَلْبٍ أُشْرِبَهَا نُكِتَ فِيهِ نُكْتَةٌ سَوْدَاءُ، وَأَيُّ قَلْبٍ أَنْكَرَهَا نُكِتَ فِيهِ نُكْتَةٌ بَيْضَاءُ، حَتَّى تَصِيرَ عَلَى قَلْبَيْنِ، عَلَى أَبْيَضَ مِثْلِ الصَّفَا فَلَا تَضُرُّهُ فِتْنَةٌ مَا دَامَتِ السَّمَاوَاتُ وَالْأَرْضُ، وَالْآخَرُ أَسْوَدُ مُرْبَادًّا كَالْكُوزِ، مُجَخِّيًا لَا يَعْرِفُ مَعْرُوفًا، وَلَا يُنْكِرُ مُنْكَرًا، إِلَّا مَا أُشْرِبَ مِنْ هَوَاهُ»، قَالَ حُذَيْفَةُ: وَحَدَّثْتُهُ، أَنَّ بَيْنَكَ وَبَيْنَهَا بَابًا مُغْلَقًا يُوشِكُ أَنْ يُكْسَرَ، قَالَ عُمَرُ: أَكَسْرًا لَا أَبَا لَكَ؟ فَلَوْ أَنَّهُ فُتِحَ لَعَلَّهُ كَانَ يُعَادُ، قُلْتُ: لَا بَلْ يُكْسَرُ، وَحَدَّثْتُهُ أَنَّ ذَلِكَ الْبَابَ رَجُلٌ يُقْتَلُ أَوْ يَمُوتُ حَدِيثًا لَيْسَ بِالْأَغَالِيطِ. قَالَ أَبُو خَالِدٍ: فَقُلْتُ لِسَعْدٍ: يَا أَبَا مَالِكٍ، مَا أَسْوَدُ مُرْبَادٌّ؟ قَالَ: شِدَّةُ الْبَيَاضِ فِي سَوَادٍ، قَالَ: قُلْتُ: فَمَا الْكُوزُ مُجَخِّيًا؟ قَالَ: مَنْكُوسًا.
Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun kasance a wurin Umar - Allah Ya yarda da shi - sai ya ce: Waye a cikinku ya ji manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayanin fitintinu? Sai wasu mutane suka ce: Mu mun ji shi, sai ya ce: Wataƙila ku kuna nufin fitinar mutum a cikin iyalansa da maƙwanbcinsa ? suka ce: Eh, ya ce: Wannan sallah da azimi da sadaka zasu kankaresu, sai dai waye a cikinku ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayani akan wacce take tasowa kamar tasowar kumfar kogi? Huzaifa ya ce: Sai mutane suka yi shiru, sai na ce: Ni, ya ce: ka kyauta kuwa kai ne, Huzaifa ya ce: Na ji manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Za'a bijiro da fitintinu akan zukata kamar tabarma kara-kara, duk zuciyar da aka cakuɗata da su sai ta yi masa baƙin ɗigo, duk zuciyar data musantasu kuwa za’a yi mata farin ɗigo, har su zama akan zukata biyu (nau'i biyu), akan farar zuciya kwatankwacin fal dutse, to wannan fitinar ba zata cutar da ita ba muddin sammai da ƙasa suna nan, ɗayar kuma baƙace ƙirin kamar kifaffiyar ƙwarya, ba ta san wani aikin alheri, kuma bata inkarin wani abin ƙi, sai abinda aka cakuɗa mata na son ranta". Huzaifa ya ce: Kuma na zantar da shi, cewa lallai tsakaninka da su akwai wata kullalliyar ƙofa ta kusa a karya ta, Umar ya ce: Shin karyawa za'a yi kaicanka? Inama dai bude ta za'a yi watakila a dawo da ita, na ce: Kuma na zantar da shi wani labarin da bana galadi ba cewa wannan kofar wani mutum ne da za'a kashe ko ya mutu.
Abu Khalida ya ce: Sai na ce wa Sa'ad: Ya Abu Malik, me ake nufi da Aswad Murbadun? Ya ce: Tsananin fari a cikin baki. Ya ce: Sai na ce: To me ake nufi da al-Kuzul mujakkhiya? ya ce: Wacce aka kife.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Sarkin muminai Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya kasance a majalisarsa a tare da shi akwai wasu Jama’a daga cikin sahabbai - Allah Ya yarda da su - sai ya ce da su: Waye a cikinku ya ji manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake bayanin fitintinu? Wasu daga cikinsu suka ce: Mu mun ji shi yana bayanin fitintinu, sai Umar - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wataƙila kuna nufin ibtila'i da jarrabar mutum a cikin abinda ya keɓance shi; a matarsa da ɗansa saboda yawan soyayyarsa garesu, da kuma ƙwauransa a kansu, da shagaltarsa da su daga alkairai da yawa, ko dan sakacinsa da abinda yake lazimtarsa na tsayuwa da haƙƙoƙinsu da ladabtar da su da kuma koyar da su, haka nan fitinar mutum a maƙwabcinsa da makamancin haka, wataƙila kuna nufin hakan? Suka ce: Eh, ya ce: wadannan wasu fitintinu ne da suke hukunta hisabi, daga cikinsu akwai zunuban da ake kwaɗayin kankaresu da kyawawan ayyuka kamar sallah da azimi da sadaka. Saidai waye a cikinku ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayanin fitintinu masu gamewa saboda tsananin girmansu da yawan yaɗuwarsu suna girgiza mutane kamar girgizar kumfar kogi? Sai mutanen suka yi shiru, sai Huzaifa ɗan Yaman - Allah Ya yarda da su - ya ce: Ni na ji shi, sai Umar - Allah Ya yarda da shi - ya yi farin ciki, kuma ya ce masa: Ya mamakin ilimin babanka da ya haifi irinka; Faɗi, Huzaifa ya ce: (Manzon Allah) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Fitintinu zasu bayyana zasu ɗanfaru ta hanyar bijirowa da gefen zuciyar mutum, kamar yadda shinfiɗar tabarma take ɗanfaruwa da gefen mai bacci a kanta, kuma tsananin ɗanfaruwar fitintinun da ita yana tasiri a cikin zuciya, kuma waɗannan fitintinun zasu dinga dawowa, fitina zata maimatu bayan wata, duk zuciyar data shiga cikinta, kuma ta so ta, ta cakuɗa da ita kamar cakuɗar abin sha da kuma shigarta; zata yi baƙin ɗigo a cikin zuciyarsa, kuma duk zuciyar da taƙi karɓar fitintinun za’a yi farin ɗigo a cikinta har zuciyoyi biyun su zama akan nau'i biyu:
Akan farar zuciya dan tsananinta akan ƙulla imani, da kuma kuɓutarta daga ɓaci, kuma fitintinu basu danfara da ita ba, kuma ba su yi tasiri a cikinta ba kamar falalin dutse mulmulalle wanda wani abu bai makale a jikin shi ba, dan haka wata fitina ba zata cutar da ita ba , har sai ya gamu da Allah. Ɗaya zuciyar kuma ita ce zuciyar da launinta ya canza zuwa baƙi saboda fitintinu kamar karkatacciya ko juyayyar butar da ruwa ba ya zama a cikinta, to haka wannan zuciyar take wani alheri ko wata hikima ba ta damfare da ita, bata sanin wani abin alheri, kuma bata inkarin wani abin ƙi, sai abinda ta so kuma ranta ya so shi kawai. Huzaifa ya ce wa Umar: Lallai waɗannan fitintinun wani abu ba zai fita daga garesu a cikin rayuwarka ba, kuma tsakaninka da su akwai wata kullalliyar ƙofa ta kusa a karyata, Umar ya ce: Shin karyawa za’a yi karara? inama dai a ce a buɗeta wataƙila ta kasance a dawo da ita sai a kulleta, Huzaifa ya ce: A'a, kai, karyata za’a yi, kuma lallai wannan ƙofar wani mutum ne da za’a kashe ko ya mutu. Kuma abinda na ambace shi labari ne na gaskiya, kuma ba ya cikin littattafan ma'abota littafi biyu (Yahudawa da Nasara), kuma ba ijtihadi ne na wani ma'abocin wani ra'ayi ba, kai daga Hadisin Annabi ne - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Fa’idoji
- Haɗarin gamammun fitintinu; dan abinda yake faruwa a cikinsu na zubar da jini (rasa rayuka) da asarar dukiya da gushewar aminci.
- Keɓantattun fitintinu idan sun kasance masu danfare da addini ne to ma'abocinsu abin zargi ne; domin su kodai bidi'o'i ne ko kuma saɓo, idan kuma sun kasance masu rataya ne da al'amuran duniya, to su jarrabawa ce ga ma'abocinsu, kuma haƙuri shi ya wajaba a kansa.
- Zuciya tana tasirantuwa da fitintinun da suke bijiro mata, wanda ya dace, shi ne wanda Allah Ya shiryar da shi ya tabbata akan shiriya.
- Nawawi ya ce: Mai (Littafin) al-Tahrir ya ce: Ma'anar Hadisin: Cewa mutum idan ya bi son ransa ya aikata saɓo sai duhu ya shiga cikin zuciyarsa saboda dukkan saɓon da yake yi, idan ya zama kamar haka sai ya fitunu kuma hasken musulunci ya gushe daga gare shi, zuciya kwatankwacin kofi ne idan aka kifar da shi sai abinda ke cikinsa ya zube, kuma wani abu ba zai shiga cikinsa ba.
- Maganar Umar ga Huzaifa: (La aba laka) ma'anarsa: Ka yi ƙoƙari a cikin wannan al'amarin, ka zage dantse ka yi shiri, irin shirin wanda ba shi da wani mataimaki.
- Falalar Umar - Allah Ya yarda da shi -, kuma shi ne kullalliyar ƙofar tsakanin mutane da fitina.
Madogara
صحيح مسلم (1/ 128-129) (144).
النهاية في غريب الحديث والأثر (606) (649) (471) (521) (340) (139).
شرح النووي على مسلم (2/ 171).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com