Daga Abdullahi ibnu Amr ibnul Aas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Imanin ɗayanku ba zai cika ba har sai son zuciyarsa ya kasance mai bi ga abin da na zo da shi».
Mun rawaito shi a cikin littafin Al-Hujjah da isnadi ingantacceDarajaNawawi ya ce: Hadisi ne Ingantacce
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa mutum ba ya zama mumini mai cikakken imani na wajibi har sai soyayyarsa ta zama mai bi ga abin da Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo da shi na umarni da hani da wasunsu, sai ya so abin da ya yi umarni da shi, ya kuma ƙi abin da ya yi hani daga gare shi .
Fa’idoji
Hadsin ƙa'ida ce a cikin sallamawa shari'a da kuma jawuwa gareta.
Yi wa mutum gargaɗi cewa duk wanda ya yarda da hukuncin hankali ko na al'ada kuma ya gabatar da shi akan abin da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ta zo da shi, wanda ya aikata haka to haƙiƙa an kore imani daga gare shi.
Wajabcin hukunci da shari'a a cikin kowanne abu saboda faɗinsa: «Ga abin da na zo da shi».
Lallai imani yana ƙaruwa da yin ɗa'a, kuma yana raguwa da aikata saɓo.
Madogara
الحجة على تارك المحجة لأبي الفتح نصر بن إبراهيم المقدسي، برقم (25).
فتح الباري لابن حجر (13/289).
جامع العلوم والحكم (3/1146).
شرح النووي على مسلم (1/77).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com