Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Ban bar wata fitina a baya na ba mafi cutar da Maza kamar mata ba

عن أسامة بن زيد رضي الله عنهما عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «مَا تَرَكْتُ بَعْدِي فِتْنَةً أَضَرَّ عَلَى الرِّجَالِ مِنَ النِّسَاءِ».
Daga Usama Ɗan Zaid Allah Ya yarda da su, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Ban bar wata fitina a baya na ba mafi cutar da Maza kamar mata ba.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da labarin bai bar jarabawa a bayansa ba mafi cutar da Maza kamar mata ba, idan mace ta kasance cikin iyalansa ne, to, zai dinga kula da ita domin kada ta kaucewa Shari’a, idan kuma wata ce da ban, to, sabo da cuɗanya da kaɗaituwa da ita, da kuma irin barnar da zata biyo bayan haka.

Fa’idoji
  1. Ya wajaba a kan Musulmi ya kiyayi fitinar mata, ya toshe duk wata hanya da za ta kai ga hakan.
  2. Ya kamata ga Muminai riƙo da Allah da kwaɗayi a wurin sa domin kiyayewa daga fitintinu.
Madogara

صحيح البخاري (7/ 8) (5096). صحيح مسلم (4/ 2097) (2740). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (373). فتح الباري لابن حجر (9/ 138).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
ZARGIN SON ZUCIYA DA SHA'AWE-SHA'AWE

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com