Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

ZARGIN AYYUKAN SAƁO

Hadisai 19

Shin ba na ba ku labarin mafi girman zunubai ba?

عن أبي بكرة رضي الله عنه قال: قال النبي صلى الله عليه وسلم: «‌أَلَا ‌أُنَبِّئُكُمْ بِأَكْبَرِ الْكَبَائِرِ؟» ثَلَاثًا، قَالُوا: بَلَى يَا رَسُولَ اللهِ، قَالَ: «الْإِشْرَاكُ بِاللهِ، وَعُقُوقُ الْوَالِدَيْنِ» وَجَلَسَ وَكَانَ مُتَّكِئًا، فَقَالَ: «أَلَا وَقَوْلُ الزُّورِ»، قَالَ: فَمَا زَالَ يُكَرِّرُهَا حَتَّى قُلْنَا: لَيْتَهُ سَكَتَ.
Daga Abu bakrata - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Shin ba na ba ku labarin mafi girman zunubai ba?" sau uku, suka ce: na'am ya Manzon Allah, ya ce: "Yi wa Allah shirka, da saɓawa iyaye" sai ya zauna alhali ya kasance a kishingiɗe, sai ya ce: "Ku saurara da faɗar zur" ya ce: Bai gushe ba yana maimaitata har sai da muka ce: Ina ma dai ya yi shiru.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba wa sahabbansa labari game da mafi girman zunubai, sai ya ambaci waɗannan ukun: 1. Yi wa Allah shirka: Shi ne juyar da kowanne nau'in ibada ga wanin Allah, da daidaita wanin Allah da Allah a AllantakarSa da UbangidantakarSa da sunayenSa da siffofinSa. 2. Saɓawa iyaye: Shi ne kowacce irin cutarwa ga iyayen, magana ce ko aiki, da barin kyautatawa musu. 3. Faɗin zur, shaidar zur tana daga ciki: Shi ne dukkanin maganar da take ƙarya ce da aka yi nufin tauye wanda ta faɗa kansa ta hanyar ƙwace dukiyarsa da keta mutuncinsa, ko makamancin hakan. Haƙiƙa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya maimaita gargaɗi game da faɗin zur don faɗakarwa a kan muninta da mummunan gurbinta ga zamntakewa, har sai da sahabbansa suka ce: Ina ma dai ya yi shiru don tausaya masa, da kuma ƙin abin da zai tayar masa da hankali.

Fa’idoji
  1. Mafi girman zunubai shi ne yi wa Allah shirka; domin haka ya sanya shi farkon zunubai, kuma mafi girmansu, faɗinSa - maɗaukakin sarki yana ƙarfafa wannan: {Lallai Allah ba Ya gafartawa a yi shirka da shi, Yana gafarta koma bayan hakan ga wanda Ya so}.
  2. Girman haƙƙoƙin mahaifa, don Ya gwama haƙƙinsu da haƙƙin Allah - Maɗaukakin sarki -.
  3. Zunubai sun kasu zuwa manya da ƙanana, babban laifi shi ne: Dukkanin laifin da a cikinsa akwai uƙuba ta duniya, kamar haddodi da tsinuwa, ko narko na lahira, kamar narkon shiga wuta, kuma manyan zunubai hawa-hawa ne wasunsu sun fi wasu muni a haramci, ƙananan zunubai kuma su ne waɗanda ba wadannan ba.
Madogara

صحيح البخاري (3/ 172) (2654)، (8/ 4) (5976)، (8/ 62) (6273-6274). صحيح مسلم (1/ 91) (87). عمدة الأحكام من كلام خير الأنام صلى الله عليه وسلم (ص257) (380). شرح النووي على مسلم (2/ 81). الإلمام بشرح عمدة الأحكام لإسماعيل الأنصاري (2/ 149). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام للبسام (ص703). أعلام السنة المنشورة لاعتقاد الطائفة الناجية المنصورة، لحافظ بن أحمد الحكمي (ص111).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Akwai wani mutum daga waɗanda ke gabaninka ya kasance yana da ciwo, sai ya kasa haƙuri, sai ya ɗauki wuƙa sai ya yanke hannunsa, jinin bai tsaya ba har sai da ya mutu, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: BawaNa yayi miNi gaggawa da ransa, (saboda haka) na haramta masa aljanna

عَن الحَسَنِ قال: حَدَّثنا جُنْدَبُ بْنُ عَبْدِ اللَّهِ رضي الله عنه، فِي هَذَا المَسْجِدِ، وَمَا نَسِينَا مُنْذُ حَدَّثَنَا، وَمَا نَخْشَى أَنْ يَكُونَ جُنْدُبٌ كَذَبَ عَلَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صلّى الله عليه وسلم: «كَانَ فِيمَنْ كَانَ قَبْلَكُمْ رَجُلٌ بِهِ جُرْحٌ، فَجَزِعَ، فَأَخَذَ سِكِّينًا فَحَزَّ بِهَا يَدَهُ، فَمَا رَقَأَ الدَّمُ حَتَّى مَاتَ، قَالَ اللَّهُ تَعَالَى: بَادَرَنِي عَبْدِي بِنَفْسِهِ، حَرَّمْتُ عَلَيْهِ الجَنَّةَ».
Daga Hassan ya ce: Jundub ɗan Abdullahi - Allah Ya yarda da shi - ya yi mana hadisi a cikin wannan masallacin, kuma bamu manta ba tun da ya yi mana hadisin, kuma bama jin tsoron cewa Jundub ya yi wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ƙarya, ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Akwai wani mutum daga waɗanda ke gabaninka ya kasance yana da ciwo, sai ya kasa haƙuri, sai ya ɗauki wuƙa sai ya yanke hannunsa, jinin bai tsaya ba har sai da ya mutu, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: BawaNa yayi miNi gaggawa da ransa, (saboda haka) na haramta masa aljanna".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa akwai wani mutum daga waɗanda ke gabaninku ya kasance rauni ya same shi, sai ya kasa haƙuri bai yi haƙuri akan raɗaɗin ba, sai ya ɗauki wuƙa sai ya yanke hannunsa da ita kuma ya gaggautowa mutuwa, jinin bai tsaya ba har ya mutu, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: Bawa Na ya yi miNi gaggawa da ransa, haƙiƙa na haramta masa aljanna.

Fa’idoji
  1. Falalar haƙuri akan jarrabawa, da barin ƙorafi saboda raɗaɗi dan kar ya kai zuwa mafi tsanani daga gare shi.
  2. Bayar da bayanin al'ummun da suka shuɗe da abinda a cikinsa akwai alheri da kuma wa'azi.
  3. Ibnu Hajar ya ce: A cikinsa akwai tsayuwa a wurin haƙƙoƙin Allah da kuma rahamarSa ga halittarSa inda Ya haramta musu kashe rayukansu, kuma cewa rayuka mallakin Allah ne.
  4. Haramta aikata sabubban da zasu kai zuwa kashe rai, da kuma narko mai tsanani a cikin hakan.
  5. Ibnu Hajar ya ce: Hakan ya yi nuni akan ya yanke hannun ne dan nufin mutuwa ba dan nufin yin maganin da yake kyakkyawan zai yi anfani da shi ba.
Madogara

صحيح البخاري (4/ 170) (3463). صحيح مسلم (1/ 107) (113). فتح الباري، لابن حجر (3/ 227). شرح النووي على مسلم (2/ 127). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص651).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Manyan zanubai su ne: Yi wa Allah shirka, da saɓawa iyaye, da kashe rai, rantsuwa mai dulmiyarwa

عن عبد الله بن عمرو بن العاص رضي الله عنهما عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «الْكَبَائِرُ: الْإِشْرَاكُ بِاللهِ، وَعُقُوقُ الْوَالِدَيْنِ، وَقَتْلُ النَّفْسِ، وَالْيَمِينُ الْغَمُوسُ».
Daga Abdullahi Dan Amr Dan Aas - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Manyan zanubai su ne: Yi wa Allah shirka, da saɓawa iyaye, da kashe rai, rantsuwa mai dulmiyarwa".
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana manyan zunubai cewa su ne waɗanda aka yi narko (alƙawarin azaba) a kan wanda ya aikata su da narko mai tsanani a duniya ko a lahira. Na farkonsu "Yi wa Allah shirka": Shi ne karkatar da kowanne nau'i daga Nau’ukan ibada ga wanin Allah, da daidaita wanin Allah da Allah cikin abin da ya keɓanci Allah a AllantakarSa da UbangidantakarSa da sunayenSa da siffofinSa. Na biyunsu: "Saɓawa iyaye": Shi ne dukkanin abin da yake nuna cutarwa ga iyaye; magana ce ko aiki, da barin kyautata musu. Na ukunsu "Kashe rai": ba tare da wani haƙƙi ba, kamar kisa a kan zalunci da ta'addanci. Na huɗunsu "Rantsuwa mai dulmiyarwa": Ita ce rantsuwa alhali yana mai ƙarya yana sane cewa ƙarya yake, an ambaceta da hakan; domin cewa tana dulmiya mai yinta a laifi sannan a wuta.

Fa’idoji
  1. Rantsuwa mai dulmiyarwa ba ta da kaffara; don tsananin haɗarinta da girmanta, kawai dai akwai [damar] tuba a cikinta.
  2. Taƙaituwa a kan ambaton waɗannan manyan laifukan guda huɗu a hadisin [ya kasance] don girman laifinsu ne, ba don su ne kadai ba.
  3. Zunubai sun kasu zuwa manya da ƙanana, babban laifi shi ne: Dukkanin zunubin da a cikinsa akwai uƙuba ta duniya, kamar haddi da tsinuwa, ko narko na lahira, kamar narko da shiga wuta, kuma manyan zunubai hawa-hawa ne wasu sun fi wasu muni a haramci. Kananan zunubai su ne waɗanda ba waɗannan ba.
Madogara

صحيح البخاري (8/ 137) (6675). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 408). رياض الصالحين للنووي (ص125) (337). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (5/ 610). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص964).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kaɗai kwatankwacin abokin zama na gari da mummunan abokin zama, kamar maɗaukin almiskine da mai busa zugazugi,

عَنْ أَبِي مُوسَى رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِنَّمَا مَثَلُ الْجَلِيسِ الصَّالِحِ وَالْجَلِيسِ السَّوْءِ كَحَامِلِ الْمِسْكِ وَنَافِخِ الْكِيرِ، فَحَامِلُ الْمِسْكِ: إِمَّا أَنْ يُحْذِيَكَ، وَإِمَّا أَنْ تَبْتَاعَ مِنْهُ، وَإِمَّا أَنْ تَجِدَ مِنْهُ رِيحًا طَيِّبَةً، وَنَافِخُ الْكِيرِ: إِمَّا أَنْ يُحْرِقَ ثِيَابَكَ، وَإِمَّا أَنْ تَجِدَ رِيحًا خَبِيثَةً».
Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kaɗai kwatankwacin abokin zama na gari da mummunan abokin zama, kamar maɗaukin almiskine da mai busa zugazugi, maɗaukin alimiski: Kodai ya baka, ko kuma ka saya daga gare shi, ko kuma ka samu ƙanshi mai daɗi daga gare shi, mai busa zugazugi kuwa: Kodai ya ƙona kayanka, ko kuma ka samu mummunan ƙanshi daga gare shi".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya buga misali ga nau'i biyu na mutane: Nau'i na farko: Abokin zama da aboki na gari wanda yake shiryarwa ga Allah a abinda a cikinsa akwai yardar Allah, kuma yana taimakawa akan biyayya ga Allah, To kwatankwacinsa kamar mai saida almiski ne, kodai ya baka, ko kuma ka saya daga gare shi, ko kuma ka samu ka shaƙi ƙanshi mai daɗi daga gare Shi. Nau'i na biyu: Abokin zama kuma mummunan aboki; wanda yake toshe tafarkin Allah, kuma yana taimako akan aikin saɓo, kuma kana ganin mummunan aiki daga gare shi, kuma yana tsawaita maka zargi dan abokantaka da zama da irinsa, to kwatankwacinsa kamar maƙeri ne wanda yake hura wutarsa; kodai ya ƙona maka tufafi daga tartsatsinsa mai tashi, ko ka samu mummunan wari saboda kusantakarsa.

Fa’idoji
  1. Halaccin buga misalai dan kusanto da ma'ana ga mai sauraro.
  2. Zaburarwa da kwaɗaitarwa akan zama da ma'abota biyayya da nagarta, da nisantar ma'abota ɓarna da ma'abota munanan ɗabi'u.
Madogara

صحيح البخاري (7/ 96) (5534). صحيح مسلم (4/ 2026) (2628). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 431). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، مجموعة من الباحثين (1/ 339). شرح النووي على مسلم (16/ 178).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

((Ku nisanci abubuwa bakwai masu halakarwa

عن أبي هريرة رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «اجْتَنِبُوا السَّبْعَ الْمُوبِقَاتِ»، قَالُوا: يَا رَسُولَ اللهِ وَمَا هُنَّ؟ قَالَ: «الشِّرْكُ بِاللهِ، وَالسِّحْرُ، وَقَتْلُ النَّفْسِ الَّتِي حَرَّمَ اللهُ إِلَّا بِالْحَقِّ، وَأَكْلُ الرِّبَا، وَأَكْلُ مَالِ الْيَتِيمِ، وَالتَّوَلِّي يَوْمَ الزَّحْفِ، وَقَذْفُ الْمُحْصَنَاتِ الْمُؤْمِنَاتِ الْغَافِلَاتِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: ((Ku nisanci abubuwa bakwai masu halakarwa)) suka ce: Ya Manzon Allah, wadanne ne su? Ya ce: “Shirka da Allah, da sihiri, da kashe rai wacce Allah Ya haramta sai da gaskiya, da cin riba, da cin dukiyar maraya, da juya baya ranar yaki, da yiwa mumina katangaggiya rafkananniya kazafi".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana umartar al'ummarsa da nisantar laifuka da sabo guda bakwai masu halakarwa, yayin da aka tambaye shi game da su wadanne ne su? sai ya bayyana su da cewa su ne: Na farko: Shirka da Allah, ta hanyar rikon kishiya da tamka gare Shi - tsarki ya tabbatar maSa - daga dukkanin wani zance da ya kasance, da kuma juyar da kowace irin ibada daga ibadu ga wanin Allah - Madaukakin sarki - kuma ya fara da shirka; domin cewa ita ce mafi girman zunubai. Na biyu: Sihiri - shi ne wani na daga kullace-kullace da wasu magunguna da hayake-hayake -, yanayin tasiri a cikin jikin wanda aka yi wa sihirin ta hanyar kisa ko rashin lafiya, ko ya raba tsakanin ma'aurata biyu, shi aiki ne na Shaidan, kuma da yawa daga gare shi ba'a kaiwa zuwa gareshi sai ta hanyar shirka da neman kusanci zuwa ga munanan ayyuka da wani abin da suke so. Na uku: Kashe ran da Allah Ya hana kashe ta ba da wani abinda ya halatta a shari'ance wanda shugaba zai zartar dashi. Na hudu: Amfani da riba ta hanyar ci ko waninsa ta fuskokin amfani. Na biyar: Barna akan dukiyar karamin yaron da babansa ya mutu alhali shi bai kai shekarun balaga ba. Na shida: Guduwa daga yaki da ake yi da kafirai. Na bakwai: Tuhumar 'ya'ya mata kamammu da zina, haka nan ma tuhumar maza.

Fa’idoji
  1. Lallai cewa manyan zunubai ba su takaitaba a guda bakwai ba, kuma kebance wadannan bakwan dan girmansu ne da kuma hadarinsu.
  2. Halaccin kashe rai idan ya kasance da hakki ne kamar kisasi da ridda da zina bayan katangantuwa, kuma shugaba na shari'a shi ne yake zartar da shi.
Madogara

صحيح البخاري (4/ 10) (2766). صحيح مسلم (1/ 92) (89). شرح صحيح البخارى لابن بطال (8/ 489). الملخص في شرح كتاب التوحيد، للشيخ صالح الفوزان (ص201).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

"Ba'a wani rai da zalunci sai idan ya kasance Xan Annabi Adam na farko yana da Alhaki a cikin sadomin shi ne wanda ya Sunnata kisa"

عن عبد الله بن مسعود رضي الله عنه مرفوعًا: «ليس مِنْ نَفْسٍ تُقْتَلُ ظُلماً إِلاَّ كَان على ابنِ آدَمَ الأَوَّل كِفْلٌ مِن دمِهَا؛ لِأَنَّه كان أوَّل مَن سَنَّ القَتْلَ».
Daga Abdullah bin Masoud - Allah ya yarda da shi - a cikin isnadi: “Babu wani rai da zai kashe ba da hakki ba sai dai idan dan Adam na farko ya sami mai jingina game da jininsa. Domin shine farkon wanda ya bada umarnin kisan.
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Wannan hadisin ya fadi dalilin da ya sa ɗayan sonsan Adam ya jimre da sakamakon jinin da aka ɓata a bayansa.Ya ce: Kayinu ya kashe ɗan'uwansa Habila don hassada saboda shi, saboda su ne farkon masu kisa kuma ɗayan Adaman Adam. Don haka Kayinu zai ɗauki alhakin zunubin jinin da aka zubar a bayansa. Saboda shi ne farkon wanda ya zartar da kisan; Domin duk wanda ya aikata shi bayan shi ana koyi dashi.

Madogara

تطريز رياض الصالحين، فيصل بن عبد العزيز المبارك، تحقيق: عبد العزيز بن عبد الله آل حمد، دار العاصمة للنشر والتوزيع، الرياض، الطبعة: الأولى 1423هـ، 2002م. دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين، محمد علي بن البكري بن علان، اعتنى بها: خليل مأمون شيحا، دار المعرفة، بيروت، الطبعة: الرابعة 1425هـ. رياض الصالحين من كلام سيد المرسلين، أبو زكريا محيي الدين النووي، تحقيق ماهر الفحل، دار ابن كثير، دمشق، بيروت، الطبعة: الأولى 1428هـ. كنوز رياض الصالحين، مجموعة من الباحثين برئاسة حمد بن ناصر العمار، كنوز إشبيليا، الرياض، الطبعة: الأولى 1430هـ. صحيح البخاري، محمد بن إسماعيل البخاري الجعفي، تحقيق: محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى 1422هـ. صحيح مسلم، مسلم بن الحجاج القشيري النيسابوري، تحقيق محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، الطبعة: 1423هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ya Manzon Allah, shin kana ganin idan wani mutum ya zo yana son karɓar kuɗina?

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: جَاءَ رَجُلٌ إِلَى رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: يَا رَسُولَ اللهِ، أَرَأَيْتَ إِنْ جَاءَ رَجُلٌ يُرِيدُ أَخْذَ مَالِي؟ قَالَ: «فَلَا تُعْطِهِ مَالَكَ» قَالَ: أَرَأَيْتَ إِنْ قَاتَلَنِي؟ قَالَ: «قَاتِلْهُ» قَالَ: أَرَأَيْتَ إِنْ قَتَلَنِي؟ قَالَ: «فَأَنْتَ شَهِيدٌ»، قَالَ: أَرَأَيْتَ إِنْ قَتَلْتُهُ؟ قَالَ: «هُوَ فِي النَّارِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani mutum ya zo wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah, shin kana ganin idan wani mutum ya zo yana son karɓar kuɗina? Ya ce: «‌Kada ka ba shi kuɗinka)) Ya ce: Shin kana ganin idan ya yaƙe ni? Ya ce: «‌Ka yaƙe shi» Ya ce: Shin kana ganin idan ya kashe ni? Ya ce: «‌Kai shahidi ne». Ya ce: Shin kana ganin idan na kashe shi ? Ya ce: «‌Shi yana cikin wuta»
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah, shin kana ganin idan wani mutum ya zo yana son ƙwatar dukiyata? Ya ce: Bai wajaba ka miƙa wuya ka ba shi dukiyarka ba, ya ce: Shin kana ganin idan ya yaƙeni? Ya ce: Yana halatta gareka ka yaƙe shi, ya ce: Shin kana ganin idan ya kasheni fa? Ya ce: To kai shahidi ne, ya ce: Shin kana ganin idan na kashe shi fa? Ya ce: Shi ya cancanci a yi masa uƙuba a cikin wuta a ranar alƙiyama.

Fa’idoji
  1. Nawawu ya ce: Kare Mutuncin matar mutum (daga faɗe) wajibi ne ba tare da wani saɓani ba, kuma a sha'anin kare kai da kisa to akwai saɓani a cikin mazahabarmu (Shafi’iyyah) da mazahabar wasunmu, kare dukiya ya halatta amma ba wajibi ba ne.
  2. Hadisin dalili ne akan cewa lallai ilmi (ya zama) kafin aiki, inda wannan sahabin ya tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga abinda yake wajaba a kansa kafin ya aikata shi .
  3. Yana kamata abi a hankali a kare kai daga ɗan ta’adda, farko ta hanyar wa'azi ko neman agaji kafin fara kashe shi, idan ya fara yakar shi to lallai ƙoƙarinsa ya zama kare kai ne ba wai kisan ba.
  4. Jinin musulmi da dukiyarsa da kuma mutuncinsa to haramun ne.
  5. Nawawi ya ce: Ka sani cewa shahidi ya kasu gida uku; Na farkonsu wanda aka kashe a yaƙar kafirai, saboda wani sababi daga cikin sabubban yaƙi, to wannan yana da hukuncin shahidai a ladan lahira da kuma hukunce-hukuncen duniya, shi ne cewa ba za’a yi masa wanka ba kuma ba za’a yi masa sallah ba. Na biyu Shahidi a lada amma banda hukunce-hukuncen duniya, shi ne wanda ya mutu da ciwon ciki, da wanda aka kashe, da wanda gini ya faɗa masa, da wanda aka kashe dan kare dukiyarsa, da wasunsu daga waɗanda hadisai ingantattu suka zo da ambatansa shahidi, to wannan za’a yi masa, wanka za’a yi masa sallah, kuma shi a lahira yana da ladan shihidai, kuma baya lazimta ya zama yana da kwatankwacin ladan na farko. Na uku wanda ya saci ganima da makamancinta wanda hadisai suka zo da kore ambatansa shahidi idan an kashe shi a yaƙin kafirai, to wannan yana cikin shahidai a duniya, ba za’a yi masa wanka ba, kuma ba za’a yi masa sallah ba, kuma ba shi da ladansu cikakke a lahira.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 124) (140). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 449). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 936). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (5/ 389).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Duk al'ummata an yafe musu sai masu bayyanarwa

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «كُلُّ أُمَّتِي مُعَافًى إِلَّا المُجَاهِرِينَ، وَإِنَّ مِنَ المُجَاهَرَةِ أَنْ يَعْمَلَ الرَّجُلُ بِاللَّيْلِ عَمَلًا، ثُمَّ يُصْبِحَ وَقَدْ سَتَرَهُ اللَّهُ عَلَيْهِ، فَيَقُولَ: يَا فُلاَنُ، عَمِلْتُ البَارِحَةَ كَذَا وَكَذَا، وَقَدْ بَاتَ يَسْتُرُهُ رَبُّهُ، وَيُصْبِحُ يَكْشِفُ سِتْرَ اللَّهِ عَنْهُ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Duk al'ummata an yafe musu sai masu bayyanarwa, kuma yana daga bayyanarwa mutum ya aikata wani aiki (mummuna) da daddare, sannan ya wayi gari Allah Ya rufa masa asiri, sai ya ce: Ya (ya falalarsa kansa) wane, jiya da daddare na aikata kaza da kaza, alhali ya kwana Uabangijinsa Ya rufa masa asiri, shi kuma ya wayi gari yana tona asirin da Allah Ya rufa masa".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa musulmi mai laifi ana yi masa kwadayin afuwar Allah da gafararSa, sai mai bayyanar da sabo dan alfahari da rashin kunya, to ba ya cancantar afuwa; ta inda yake aikata laifi da daddare, sannan ya wayi gari alhali Allah Ya rufa masa asiri, sai ya zantar da waninsa da cewa shi ya aikata sabo kaza jiya, ya kwana Ubangijinsa Ya rufa masa asiri, shi kuma ya wayi gari yana tona asirin da Allah Ya rufa masa!!

Fa’idoji
  1. Munin bayyanar da sabo bayan rufa asirin Allah - Madaukakin sarki - ya yi a gare shi .
  2. A bayyanar da sabo akwai yayata alfasha tsakanin muminai.
  3. Wanda Allah Ya rufa masa asiri a duniya Zai rufa masa asiri a lahira, wannan yana daga yalwar rahamar Allah - Madaukakin sarki - ga bayinSa.
  4. Wanda aka jarraba da wani sabo to ya wajaba ya rufawa kansa asiri kuma ya tubarwa Allah.
  5. Girman zunubin masu bayyanarwa wadanda suke nufin bayyanar da sabo, kuma suna barin afuwar Allah taba wuce su.
Madogara

صحيح البخاري (8/ 20) (6069). صحيح مسلم (4/ 2291) (2990). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 15). منار القاري شرح مختصر صحيح البخاري، لحمزة قاسم (5/ 251). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 329). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، مجموعة من الباحثين (1/ 255).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
8 cikin 19
Hadisai 19
  1. Shin ba na ba ku labarin mafi girman zunubai ba?
  2. Akwai wani mutum daga waɗanda ke gabaninka ya kasance yana da ciwo, sai ya kasa haƙuri, sai ya ɗauki wuƙa sai ya yanke hannunsa, jinin bai tsaya ba har sai da ya mutu, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: BawaNa yayi miNi gaggawa da ransa, (saboda haka) na haramta masa aljanna
  3. Manyan zanubai su ne: Yi wa Allah shirka, da saɓawa iyaye, da kashe rai, rantsuwa mai dulmiyarwa
  4. Kaɗai kwatankwacin abokin zama na gari da mummunan abokin zama, kamar maɗaukin almiskine da mai busa zugazugi,
  5. ((Ku nisanci abubuwa bakwai masu halakarwa
  6. "Ba'a wani rai da zalunci sai idan ya kasance Xan Annabi Adam na farko yana da Alhaki a cikin sadomin shi ne wanda ya Sunnata kisa"
  7. Ya Manzon Allah, shin kana ganin idan wani mutum ya zo yana son karɓar kuɗina?
  8. Duk al'ummata an yafe musu sai masu bayyanarwa
  9. Lokacin da aka hau da ni (aka yi Mi'iraji da ni) na wuce wasu mutane da suke da farata na tagulla, suna yakusar fuskokinsu da ƙirazansu da su
  10. Idan musulmai biyu suka haɗu da takubbansu, to, wanda ya kashe da wanda aka kashe suna cikin wuta
  11. An tambayi Annabi game da abu mafi yawa da yake shigar da Mutane" Al-janna? ya ce: Tsoron Allah da kyawawan Halaye, kuma aka tambaye shi game da abu mafi yawa da yake jefa Mutane wuta sai ya ce Baki da Farjin su"
  12. Bana baku labari ba Maye cizo? shi ne Gulmar da ake yada kadarta cikin Mutane
  13. ‌Mutum uku Allah ba zai yi musu magana ba a ranar alƙiyama kuma ba zai tsarkakesu ba kuma suna da zaba mai raɗaɗi
  14. "Idan Allah ya so yiwa wasu Mutane Azaba, sai Azabar ta sami wadanda suke cikin su, Sannan sai a tashe su a kan Ayyukansu"
  15. Qararrawa ita ce garayar Shaixan ce
  16. Abubuwa guda huɗu wanda ya kasance a cikinsa to ya zama munafiki tsantsa, wanda ya kasance a tare da shi akwai wata ɗabi'a daga cikinsu to ya kasance akwai ɗabi'a ta munafunci a tare da shi har sai ya barta: Idan zai yi magana sai ya yi ƙarya, idan an ƙulla yarjejeniya da shi sai ya yi yaudara, idan ya yi alƙawari sai ya saɓa, idan an yi faɗa da shi sai ya yi fajirci
  17. Wanda ya gangaro daga wani dutse sai ya kashe kansa to shi yana cikin wuta zai dinga gangarowa a cikinta yana abin dawwamarwa a cikinta har abada
  18. Na haneku da ƙananan zunibai
  19. Abubuwa guda huɗu wanda ya kasance a cikinsa to ya zama munafiki tsantsa, wanda ya kasance a tare da shi akwai wata ɗabi'a daga cikinsu to ya kasance akwai ɗabi'a ta munafunci a tare da shi har sai ya barta: Idan zai yi magana sai ya yi ƙarya, idan an ƙulla yarjejeniya da shi sai ya yi yaudara, idan ya yi alƙawari sai ya saɓa, idan an yi faɗa da shi sai ya yi fajirci

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com