Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa musulmi mai laifi ana yi masa kwadayin afuwar Allah da gafararSa, sai mai bayyanar da sabo dan alfahari da rashin kunya, to ba ya cancantar afuwa; ta inda yake aikata laifi da daddare, sannan ya wayi gari alhali Allah Ya rufa masa asiri, sai ya zantar da waninsa da cewa shi ya aikata sabo kaza jiya, ya kwana Ubangijinsa Ya rufa masa asiri, shi kuma ya wayi gari yana tona asirin da Allah Ya rufa masa!!
- Munin bayyanar da sabo bayan rufa asirin Allah - Madaukakin sarki - ya yi a gare shi .
- A bayyanar da sabo akwai yayata alfasha tsakanin muminai.
- Wanda Allah Ya rufa masa asiri a duniya Zai rufa masa asiri a lahira, wannan yana daga yalwar rahamar Allah - Madaukakin sarki - ga bayinSa.
- Wanda aka jarraba da wani sabo to ya wajaba ya rufawa kansa asiri kuma ya tubarwa Allah.
- Girman zunubin masu bayyanarwa wadanda suke nufin bayyanar da sabo, kuma suna barin afuwar Allah taba wuce su.
صحيح البخاري (8/ 20) (6069). صحيح مسلم (4/ 2291) (2990). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 15). منار القاري شرح مختصر صحيح البخاري، لحمزة قاسم (5/ 251). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 329). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، مجموعة من الباحثين (1/ 255).