Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

An tambayi Annabi game da abu mafi yawa da yake shigar da Mutane" Al-janna? ya ce: Tsoron Allah da kyawawan Halaye, kuma aka tambaye shi game da abu mafi yawa da yake jefa Mutane wuta sai ya ce Baki da Farjin su"

عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: سئل رسول الله صلى الله عليه وسلم عن أكثر ما يُدْخِلُ الناسَ الجنة؟ قال: «تقوى الله وحسن الخلق»، وسئل عن أكثر ما يُدْخِلُ الناسَ النار، فقال: «الفم والفرج».
An karbo daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- An tambayi Annabi game da abu mafi yawa da yake shigar da Mutane" Al-janna? ya ce: Tsoron Allah da kyawawan Halaye, kuma aka tambaye shi game da abu mafi yawa da yake jefa Mutane wuta sai ya ce Baki da Farjin su"
Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shiDarajaSanadi nsa Hasan ne
Sharhi

Mafi yawan Dalilan da suke shigar da Mutum Al-jannah sune tsoron Allah da kyawawan Dabi'u da tsoron Allah ta hanyar nisantar abubuwan da ya Haramta baki dayan su, da kuma kyawawan dabi'u ga Halitta kuma mafi karancinsa barin cuta da su, kuma mafi girmansu kyautatawa ga wanda ya Munanana masa. kuma mafi yawan abubuwan da suke shigar da Mutane wuta shi Babi da kuma Farji; saboda Mutum Mafi yawa ta hanyasu yake fadawa cikin sabon Allah da kuma batawa da Mutane.

Madogara

مسند الإمام أحمد بن حنبل, تأليف: أبو عبدالله أحمد بن حنبل الشيباني, تحقيق: شعيب الأرنؤوط وعادل مرشد وآخرون, الناشر: دار الرسالة, ط1 عام 1421. سنن الترمذي، نشر: شركة مكتبة ومطبعة مصطفى البابي الحلبي – مصر، الطبعة: الثانية، 1395هـ - 1975م. سنن ابن ماجه, تأليف: أبو عبدالله محمد القزويني, تحقيق: محمد فؤاد عبدالباقي, الناشر: دار إحياء الكتب العربية. السلسلة الصحيحة وشيء من فقهها وفوائدها, تأليف: أبو عبدالرحمن محمد ناصر الدين الألباني, الناشر: مكتبة المعارف, ط1 عام 1415. بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين, تأليف: سليم بن عيد الهلالي, دار ابن الجوزي. مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح, تأليف: علي بن سلطان القاري, الناشر: دار الفكر, ط1 عام 1422.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
HALAYE NAGARI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com