Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Ku sauƙaƙa kada ku tsananta, ku yi bushara kada ku yi kora

عن أنس بن مالك رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «يَسِّرُوا وَلَا تُعَسِّرُوا، وَبَشِّرُوا وَلَا تُنَفِّرُوا».
Daga Anas Ɗan Malik Allah Ya yarda da shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Ku sauƙaƙa kada ku tsananta, ku yi bushara kada ku yi kora.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da umarnin sauƙaƙawa da rangwame wa mutane, da kada a tsananta musu a dukkanin lamura na addini da na rayuwa, wannan kuwa a daidai yadda Allah Ya halatta Ya kuma shar’anta. Kuma yana kwaɗaitarwa a kan bushara da alheri, da rashin korar (kyarar) mutane.

Fa’idoji
  1. Wajibin dake kan mumini shi ne ya sanya wa mutane son Allah, ya kwadaitar da su alheri.
  2. Ya kamata ga mai kiran mutane zuwa ga Allah ya yi nazari cikin hikima a kan yadda zai isar da saƙon Musulunci zuwa ga mutane.
  3. Bushara tana haifar da farin ciki da karɓuwa da nutsuwa da abin da mai Da'awa ya ke gabatarwa ga mutane.
  4. Tsanantawa tana haifar da ƙyama da kuma juya baya da sanya shakku a maganar mai Da’awah.
  5. Yalwatuwar rahamar Allah ga bayinSa, da cewa Ya yardar musu da addini mai sauƙi da Shari’ah mai rangwame.
  6. Sauƙi da aka yi umarni da shi, shi ne wanda Shari’a ta zo da shi.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 25) (69). صحيح مسلم (3/ 1358) (1732). شرح صحيح البخاري، لابن بطال (1/ 153). إرشاد الساري لشرح صحيح البخاري، لأبو العباس القسطلاني (1/ 169). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 687).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
HALAYE NAGARI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com