عَنْ أَبِي سَعِيدٍ رضي الله عنه أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَا مِنْ مُسْلِمٍ يَدْعُو بِدَعْوَةٍ لَيْسَ فِيهَا إِثْمٌ، وَلَا قَطِيعَةُ رَحِمٍ، إِلَّا أَعْطَاهُ اللهُ بِهَا إِحْدَى ثَلَاثٍ: إِمَّا أَنْ تُعَجَّلَ لَهُ دَعْوَتُهُ، وَإِمَّا أَنْ يَدَّخِرَهَا لَهُ فِي الْآخِرَةِ، وَإِمَّا أَنْ يَصْرِفَ عَنْهُ مِنَ السُّوءِ مِثْلَهَا» قَالُوا: إِذنْ نُكْثِرُ، قَالَ: «اللهُ أَكْثَرُ».
Daga Abu sa'id AlKhudri - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Babu wani musulmi da zai yi wata addu'a wacce babu zunubi a cikinta, kuma babu yanke zumunci, face sai Allah Ya ba shi ɗayan abu uku: Kodai Ya gaggauto masa da (amsa) addu’ar sa, ko kuma Ya tanadar masa ita sai ranar alƙiyama, ko kuma Ya kawar masa da wani mummunan abu irinta". Sai (Sahabbai) suka ce: Kenan mu yawaita? Sai ya ce: "Allah Shi ne Mafi yawaitawa".
Ahmad ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa; Musulmi idan ya roƙi Allah ya roke shi wata bukata wacce ba zunubi ba ce kamar ya roƙeShi da sawwaƙa saɓo da zalinci, kuma bai yi addu'a da yanke zumunci ba; kamar ya yi mummunar addu'a akan 'ya'yansa da 'yan uwansa, sai Allah Ya ba shi ɗayan al'amura uku da addu'arsa: Kodai Ya gaggauto masa da addu'arsa Ya ba shi abinda ya roƙa. Ko kuma Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya jinkirtar masa da ita dan lada gare shi a ranar alƙiyama da ɗaukaka daraoji, ko rahama ko gafarta munanan ayyuka. Ko kuma Ya kawar masa a duniyarsa da mummuna kwatankwacinta da gwargwadan addu'ar. Sai sahabban suka cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ai sai mu yawaita addu'a; dan mu samu waɗannan falalolin? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Lallai abinda ke gurin Allah shi ya fi yawa kuma ya fi girma daga abinda kuke tambaya, kyautarSa bata ƙarewa, kuma bata tiƙewa.
Fa’idoji
- Addu'ar musulmi abar karɓa ce ba'a dawo da ita sai dai da sharuɗɗanta da kuma ladubbanta; saboda haka yana kamata ga bawa ya yawiata addu'a kada ya yi gaggawar amsawa.
- Amsa addu'a ba'a ƙayyade yake da samun abin da ake nema ba; za'a iya kankare masa (zunubinsa) da addu'arsa, ko Ya yi masa tanadi da ita a lahira.
- Ibnu Baaz ya ce: Naci, da kyakkyawan zato ga Allah, da rashin yanke ƙauna, yana daga mafi girman sabubban amsawa, to ya wajaba akan mutum ya nace a cikin addu'a, ya kyautatawa Allah - Mai girma da ɗaukaka - zato, ya kuma san cewa Shi Gwani ne kuma Masani ne, Zai iya gaggauta amsawa dan wata hikima, kuma Zai iya jinkirtata dan wata hikima, kuma Zai iya baiwa mai roƙon mafi alheri daga abinda ya roƙa.
Madogara
مسند أحمد (17/ 213) (11133).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 592).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص805).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (6/ 54).
مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، للقاري (4/ 1537).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 1020).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ سَلْمَانَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِنَّ رَبَّكُمْ حَيِيٌّ كَرِيمٌ، يَسْتَحْيِي مِنْ عَبْدِهِ إِذَا رَفَعَ يَدَيْهِ إِلَيْهِ أَنْ يَرُدَّهُمَا صِفْرًا».
Daga Salman - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lalle Ubangijinku Mai kunya ne kuma Mai karamci ne, Yana jin kunyar bawanSa idan ya ɗaga hannayensa zuwa gare Shi Ya dawo da su babu komai".
Abu Dawud da Tirmizi da Ibn Majah ne Suka Rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kwaɗaitarwa akan ɗaga hannaye a lokacin addu'a, kuma ya bada labarin cewa Allah - tsarki ya tabbatar maSa (Mai kunya ne) Mai yawan kunya ne, ba Ya barin kyauta, Yana yi wa bawa abinda yake faranta masa, kuma Yana barin abinda yake cutar da shi, (Mai yawan kyauta ne) Yana bayarwa ba tare da tambaya ba to yaya kuma bayan tambaya! Yana jin kunyar bawanSa mumini ya dawo da hannayensa bayan ɗagasu dan yin addu'a babu komai suna babu komai cikinsu a taɓe daga amsawa.
Fa’idoji
- A duk lokacin da mutum ya bayyanar da buƙatuwa zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki - da bauta, ya kasance ya fi ƙauna gare shi kuma ya fi kusanci ga amsawa.
- Kwaɗaitarwa a kan addu'a, da son ɗaga hannaye a cikinta, kuma cewa shi yana daga sabubban amsawa.
- Bayanin yalwar karamcin Allah da rahamarSa ga bayinSa.
Madogara
سنن أبي داود (2/ 609) (1488).
سنن الترمذي (5/ 521) (3556).
توضيح الأحكام من بلوغ المرام، لعبد الله البسام (7/ 552).
منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (10/ 423).
فتح ذي الجلال والإكرام، لابن عثيمين (6/ 483).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ عَائِشَةَ رضي الله عنها قَالَتْ: كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَسْتَحِبُّ الْجَوَامِعَ مِنَ الدُّعَاءِ، وَيَدَعُ مَا سِوَى ذَلِكَ.
Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana son Addu'ar da ta tattaro komai, kuma yana ƙyale wacce ba ita ba.
Abu Dawud ne ya Rawaito shi da Kuma AhmadDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana son addu'o'i masu tattaro alherin duniya da lahira wacce lafazinta kaɗan ne kuma ma'anarta yana da yawa, kuma a cikinta akwai yabo ga Allah - Maɗaukakin sarki -, da manufofi na gari, kuma yana barin koma bayan haka.
Fa’idoji
- An so addu'a da lafuza sassauƙa masu tattaro ma'anonin alheri, da kuma ƙin ɗorawa kai wahala da tsananatawa a cikin mas'ala, hakan saɓanin karantarwar Annabi ce - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
- An keɓanci Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kalmomi masu tattaro (ma'anoni).
- Kwaɗayi akan abinda ya tabbata cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi addu'a da shi; koda ya kasance mai tsawo ne, kuma kalmominsa sun yi yawa, dukkansa daga addu'o'i ne masu tattarowa.
Madogara
سنن أبي داود (2/ 605) (1482).
مسند أحمد (42/ 76) (25151).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 542).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 1003).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (6/ 15).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (17/ 349).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَن أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: «لاَ يَقُلْ أَحَدُكُمْ: اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي إِنْ شِئْتَ، ارْحَمْنِي إِنْ شِئْتَ، ارْزُقْنِي إِنْ شِئْتَ، وَليَعْزِمْ مَسْأَلَتَهُ، إِنَّهُ يَفْعَلُ مَا يَشَاءُ، لاَ مُكْرِهَ لَهُ».
ولمسلم: «وَلَكِنْ لِيَعْزِمِ الْمَسْأَلَةَ وَلْيُعَظِّمِ الرَّغْبَةَ، فَإِنَّ اللهَ لَا يَتَعَاظَمُهُ شَيْءٌ أَعْطَاهُ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ɗayanku ya ce: Ya Allah Ka gafarta mini in Ka so, Ka yi mini rahama in Ka so, Ka azirtani in Ka so, ya ƙudirce niyyar rokonsa, lallai Shi Yana aikata abinda Yake so, babu mai tilasta Shi". Kuma riwayar Muslim: "Sai dai ya ƙudirce niyyar tambaya kuma ya girmama kwaɗayi, domin Allah wani abu da Ya bada shi ba ya yi maSa girma".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani daga rataya addu'a da wani abu koda ya kasance da Mashi'ar Allah ne (ganin damar Allah) domin hakan wani al'amari ne abin sani abin sakankancewa cewa shi ba'a gafartawa sai idan tsarki ya tabbatar maSa Ya so, kuma babu wata ma'ana ga sharɗanta Mashi'a; domin cewa ita kaɗai ana sharɗantata ne ga wanda ya inganta daga gare shi ya yi aiki ba tare da ya so ba da tilastawa da waninsa daga abinda Allah - tsarki ya tabbatar maSa - Ya tsarkaka daga gare shi, haƙiƙa tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bayyana a cikin ƙarshen hadisin da faɗinSa lallai shi Allah babu mai tilasta shi, kamar yadda cewa Allah babu wani abu daya da ya bada shi yake girmama a gareShi, kuma Shi ba mai gajiyawa bane kuma wani abu ba ya girmama a gareShi har ace: Idan Ka so, kuma rataya shi da Mashi'a wani nau'i ne na wadatuwa daga gafararSa, to faɗin mai faɗa: Idan Ka so Ka bani kaza to Ka aikata, ba'ayin amfani da wannan sai tare da wanda ya wadata daga gare shi, ko tare da wanda ya gajiya, amma tare da mai iko kuma tare da mai buƙatuwa gare shi to cewa shi ya ƙudirce niyyar roƙonsa, kuma ya yi roƙo irin roƙon mabuƙaci mai tsananin buƙatuwa zuwa ga abinda ya roƙe shi, kuma ya fake zuwa ga Allah; domin cewa Shi Mawadaci ne cikakke, Mai iko a kan dukkan komai.
Fa’idoji
- Hani daga rataya addu'a da Mashi'a (ganin dama).
- Tsarkake Allah daga abinda ba ya dacewa da Shi, da yalwar falalarSa, da cikar wadatuwarSa, da karamcinSa da kyautarSa - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka -.
- Tabbatar da kamala ga Allah - Mai girma da ɗaukaka -.
- Girmama kwaɗayi ga abinda ke gurin Allah da kyautata zato gare Shi - tsarki ya tabbatar maSa -.
- Rataya addu'a da Mashi'a (ganin dama) yana faruwa daga wasu daga cikin mutane alhali su ba su sani ba, misali faɗin: Allah Ya yi maka sakayya da alheri in Allah Ya so, Allah Ya yi masa rahama in Allah Ya so, to wannan ba ya halatta saboda hadisin babin.
Madogara
صحيح البخاري (9/ 140) (7477).
صحيح مسلم (4/ 2063) (2679).
الجديد في شرح كتاب التوحيد، لمحمد القرعاوي (ص410).
الملخص في شرح كتاب التوحيد، لصالح الفوزان (ص368).
القول المفيد على كتاب التوحيد، لابن عثيمين (2/ 331).
Wannan hadisi a HadeethEnc.com