Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa; Musulmi idan ya roƙi Allah ya roke shi wata bukata wacce ba zunubi ba ce kamar ya roƙeShi da sawwaƙa saɓo da zalinci, kuma bai yi addu'a da yanke zumunci ba; kamar ya yi mummunar addu'a akan 'ya'yansa da 'yan uwansa, sai Allah Ya ba shi ɗayan al'amura uku da addu'arsa: Kodai Ya gaggauto masa da addu'arsa Ya ba shi abinda ya roƙa. Ko kuma Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya jinkirtar masa da ita dan lada gare shi a ranar alƙiyama da ɗaukaka daraoji, ko rahama ko gafarta munanan ayyuka. Ko kuma Ya kawar masa a duniyarsa da mummuna kwatankwacinta da gwargwadan addu'ar. Sai sahabban suka cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ai sai mu yawaita addu'a; dan mu samu waɗannan falalolin? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Lallai abinda ke gurin Allah shi ya fi yawa kuma ya fi girma daga abinda kuke tambaya, kyautarSa bata ƙarewa, kuma bata tiƙewa.
- Addu'ar musulmi abar karɓa ce ba'a dawo da ita sai dai da sharuɗɗanta da kuma ladubbanta; saboda haka yana kamata ga bawa ya yawiata addu'a kada ya yi gaggawar amsawa.
- Amsa addu'a ba'a ƙayyade yake da samun abin da ake nema ba; za'a iya kankare masa (zunubinsa) da addu'arsa, ko Ya yi masa tanadi da ita a lahira.
- Ibnu Baaz ya ce: Naci, da kyakkyawan zato ga Allah, da rashin yanke ƙauna, yana daga mafi girman sabubban amsawa, to ya wajaba akan mutum ya nace a cikin addu'a, ya kyautatawa Allah - Mai girma da ɗaukaka - zato, ya kuma san cewa Shi Gwani ne kuma Masani ne, Zai iya gaggauta amsawa dan wata hikima, kuma Zai iya jinkirtata dan wata hikima, kuma Zai iya baiwa mai roƙon mafi alheri daga abinda ya roƙa.
مسند أحمد (17/ 213) (11133). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 592). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص805). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (6/ 54). مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، للقاري (4/ 1537). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 1020).